Coronavirus: Bayanai kai tsaye kan alkaluman cutar a Afrika
Ga bayanai kai tsaye na yawan masu dauke da coronavirus a kasashen Afrika da wadanda suka warke da kuma wadanda suka mutu
Ku latsa nan don karantawa:
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan ne karon farko da aka samu coronavirus a jihar Katsina.
Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Awwal Ahmad Janyau
Ga bayanai kai tsaye na yawan masu dauke da coronavirus a kasashen Afrika da wadanda suka warke da kuma wadanda suka mutu
Ku latsa nan don karantawa:
Editan BBC Hausa Aliyu Abdullahi Tanko ya tattauna da wani dan Najeriya wanda a makonni biyun da suka wuce likitoci suka ce masa yana dauke da cutar coronavirus, amma kuma a gwajin baya-bayan nan an sake gwada shi ba ya dauke da cutar.
Mutumin wanda har yanzu yake asibitin gwamnati da ke Gwagwalada a Abuja inda ake kula da masu cutar Covid 19, ya yi wa Aliyun karin bayani yadda lamarin ya faru da shi:
Gwamnatin Morocco ta ce za a soma daurin wata uku ko cin tarar $126 ga duk mutumin da ya fita waje ba tare da sanya takunkumnin rufe fuska ba.
Wannan dokar za ta soma aiki ne ranar Talata ga dukkan mutanen da aka amince su rika fita daga gidajensu bayan da aka sanya dokar hana fita saboda dakile coronavirus, wacce ta soma aiki a tsakiyar watan Maris.
Gwamnati ta sanar da daukar matakin ne ranar Litinin bayan wani taro da aka gudanar kan yadda za a dakile yaduwar cutar.
Ana sayar da kowanne takunkumin rufe fuska kan $0.08.
Amurka ta soma kwashe 'yan kasarsa daga Najeriya a yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar coronavirus.
Sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata, ya ce tun ranar Litinin aka kwashe Amurkawa 376 daga kasar zuwa birnin Washington.
Ofishin ya kara da cewa za a ci gaba da kwashe Amurkawa daga Najeriya zuwa Washington.
A makon jiya Amurka ta sanar cewa za ta soma kwashe 'ya'yanta daga Najeriya, jim kadan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da rufe jihohin Lagos da Ogun da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Alkaluma dai sun nuna cewa coronavirus ta fi yin illa a Amurka inda ya zuwa ranar Talata mutum fiye da 360, 000 suka kamu da cutar yayin da mutum sama da 10,000 suka mutu.
A Najeriya, alkaluma sun nuna cewa mutum 238 ne suka kamu da cutar yayin da mutum biyar suka mutu.
'Yan sandan Uganda sun ce an samu karuwar cin zarafi a gidaje tun lokacin da aka sanya dokar hana fita a kasar domin dakile yaduwar coronavirus mako biyu da suka wuce.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Fred Enanga ya ce an kama mutum hudu da ake zargi da kisan kai.
Kafafen watsa labaran kasar sun ambato Mr Enanga yana cewa ana samun karuwar cin zarafin ne saboda mutane "suna zama a gida fiye da kima".
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewa an samu karuwar cin zarafi a duniya baki daya a yayin da ake fama da annobar coronavirus.
Ya nemi gwamnatoci su hanzarta kama da kuma hukunta duk mutumin da aka samu da laifin cin zarafi.
Alkaluman da jami'an lafiyar Chicago suka fitar sun nuna cewa coronavirus na ci gaba da kashe Amurkawa bakaken fata a birnin.
Bakaken fata 'yan Chicago su ne rabin mutanen da coronavirus ta fi kamawa a birnin kuma su ne kashi 70 cikin 100 na mutanen da suka mutu, duk da yake bakar fata basu fi kashi 30 na mazauna birnin ba.
Kazalika coronavirus ta yi kamari a sauran biranen da bakaken fata suka fi yawa irin su Detroit, Milwaukee, New Orleans da kuma New York.
An samu mutum kusan 370,000 da suka kamu da cutar a Amurka yayin da kimanin mutum 11,000 suka sheka barzahu.
An bai wa tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre hutun wata biyu daga gidan yari a Senegal, inda yake daure bayan an same shi da laifukan yaki da na keta hakkin bil adama, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Ana amfani da gidan yarin domin killace sabbin mutanen da aka daure a yayin da ake killace masu dauke da coronavirus, in ji AFP.
An samu Habre da laifukan keta hakkin dan adam a 2016 inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan kaso a Senegal. An kama shi da laifin yin fyade da bautarwa da kuma sanya a kashe mutane a lokacin mulkinsa tsakanin 1982 zuwa 1990.
Ya musanta aikata laifin bayar da umarni wurin kashe mutum 40,000 lokacin mulkinsa.
Shi ne karon farko da wata kotu da kungiyar tarayyar Afirka ke mara wa baya ta yanke hukunci kan tsohon shugaban kasa bisa laifukan keta hakkin dan adam.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito cewa lauyoyin tsohon shugaban kasar sun bukaci a ba shi hutun kwana 60 dsaboda "yana cikin mutanen da za su iya kamuwa da" coronavirus.
Habre zai yi hutun ne a gidansa da ke Ouakam, a wani yanki da ke Dakar, babban birnin Senegal kuma za a mayar da shi gidan yari idan ya kammala hutun.
Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka, Africa CDC, ta ce mutum fiye da dubu goma ne coronavirus ta kama a kasashe 52 na kungiyar tarayyar Afirka ya zuwa safiyar Talata, 7 ga watan Afrilun 2020.
A sakon da ta wallafa a Twitter, Africa CDC ta ce cutar ta yi ajalin mutum 487 yayin da mutum 913 suka warke.
Duk da wadannan alkaluma, Afirka na cikin nahiyoyin da ke da karancin mutanen da suka kamu da cutar, amma masana na ci gaba da kira ga mutane su dauki matakan kare kansu, ciki har da bayar da tazara a tsakansu, da yawaita wanke hannuwa da kaurace wa shiga taron jama'a da kuma killace kai ga mutanen da suka ga alamar kamuwa da cutar.
Rundunar sojin Mali ta ce mayakan da ke ikirarin jihadi sun kashe akalla soji 20 a birnin Gao da ke arewacin kasar.
Mutanen da ke yakin sun ce mayakan sun shiga yankin ne a ckin motoci wasu kuma a kan babura inda suka kai hari kan sansanin sojin kasar da safiyar Litinin.
Sun kara da cewa maharan sun lalata sansanin wanda ke kusa da garin Bamba sannan suka sace makamai.
wani jami'in sojin Mali ya ce an kashe masu ikirarin jihadin amma ba zai yiwu a san adadin wadanda suka mutu ba saboda 'yan uwansu sun dauke gawarwakinsu suka tafi da su.
Hare-haren masu ikirarin jihadi na ci gaba da karuwa a yankin Sahel a baya bayan nan.
Gwajin da aka yi wa ministan tsaron Ivory Coast Hamed Bakayoko ya tabbatar da cewa ya kamu da kwayar cutar ronavirus.
Mr Bakayoko ya ce bai nuna alamomin kamuwa da cutar ba kafin a yi masa gwajin sannan ya bukaci ‘yan kasar su dauki matakan kiyaye lafiyarsu.
Tuni dai aka killace ministan.
Ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a turancin Faransa .
Ya zuwa yanzu Ivory Coast ta tabbatar mutum 323 sun kamu da coronavirus yayin da mutum uku suka warke.
Gwamnati ta sanya dokar hana fita a babban birnin kasar Abidjan sannan ta tilasta wa dukkan kasar bin dokar hana fita daga karfe and enforced nationwide 9 na dare zuwa karfe 5 na safe agogon kasar.
Ranar Asabar, jami'an lafiyar kasar sun bukaci mutane su rika sanya takunkumin rufe fuska da zummar dakile yaduwar cutar.
Ghana ta tabbatar da karin mutum 73 da suka kamu da coronavirus, inda jumulla kasar take da mutum 287 da suka harbu da cutar.
An sanar da sabbin mutanen da suka kamu da cutar ne ranar Talata da safe.
Hukumar kula da lafiya ta kasar ta ce an samu karin mutanen da suka kamu da coronavirus ne saboda samun "ingantattun kayan gano masu dauke da ita da kuma gwada su".
Ta kara da cewa an kawo karshen tsarinta na tilasta wa dukkan mutumin da ya dawo daga kasashen waje killace kansa wanda aka soma tsakanin 21 da 22 ga watan Maris.
An killace kimanin mutum 1,030 a lokacin inda aka gano 105 na dauke da cutar a gwaje-gwaje da aka gudanar a lokuta biyu daban-daban.
Ma'ikatar yada labaran Ghana ta yi bayani dalla-dalla a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter:
Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka da ke bin diddigin yaduwar annobar coronavirus, ta ce akalla mutum 285,000 sun warke daga cutar a fadin duniya zuwa safiyar ranar Talata 7 ga watan Afrilu, 2020.
Jami’ar ta kara da cewa mutum kusan da miliyan daya da dubu dari uku ne suka kamu da coronavirus.
A cewarta, kusan mutum 75,000 ne suka mutu.
Daga nan Sashen Hausa na BBC muke yi muku barka da wannan safiya. Da fatan za ku kasance tare da mu domin sanin halin da duniya ke ciki dangane da coronavirus, cutar da ta addabi kasashen duniya.
Baya ga lamarin wannan cuta, za kuma mu kawo muku sauran labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman daga kasashen Najeriya da Nijar da ma sassan duniya.
Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.