Wata mata da take samun kulawa sakamakon kamuwa da coronavirus a wurin killace masu cutar da ke Yaoundé, babban birnin Kamaru, ta haifi jaririya a karshen mako, likitan da ya karbi haihuwar ya shaida wa BBC.
Matar, mai shekara 19 mai suna Marie, ta haihu ne salin-alin ko da yake tuna aka dauke jaririyar daga gabanta.
An sanya mata wani na'urar da ke sanya ta yin numfashi a lokacin da ta soma nakuda.
Likitan mata da ya karbi haihuwar, Dr Yaneu Ngaha Bondja Junie, ya shaida wa BBC cewa: “Mun samu dakin da muka kai ta ta haihu a can ko da yake sanye take da na'urar da ke taimaka mata wurin yin numfashi."
Jaririyar bakwanini ce inda nauyinta bai wuce 2.1kg kuma yanzu tana sashen kula da jarirai. Ba a sani ko ko jaririyar ta kamu da coronavirus domin kuwa har yanzu ana jiran sakamakon gwajin da aka yi mata.