Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya kan coronavirus

Wannan ne karon farko da aka samu coronavirus a jihar Katsina.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    A nan muke sallama inda za mu dakatar da kawo bayanai kai tsaye da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus da ma wasu labarai a duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu gobe domin ci gaba da kawo muku labarai da dumu-duminsu.

    Sai gobe.

  2. Coronavirus: Karin mutum 16 sun kamu a Najeriya

    Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta ce an kara samun mutum 16 da suka kamu da coronavirus a Najeriya.

    Kuma a karon farko an samu mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar Katsina.

    An kara samun mutum 10 a Legas, 2 a Abuja, 2 a Oyo 1 a Delta.

    Yanzu jimillar mutum 254 suka kamu da cutar a Najeriya, yayin da 44 suka warke. Shida kuma suka mutu

  3. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus ta kashe Likita a Daura - Masari

    Mahukunta a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar wani likita sakamakon harbuwa da cutar coronavirus.

    Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ne ya tabbatar da BBC cewa cutar Covid 19 ce ta kashe likitan

    Ya ce bayyana cewa Likitan mazaunin birnin Daura ne da ya yi bulaguro zuwa Legas, kuma bayan dawowarsa ya kwanta jinya, wadda ta yi masa sanadi.

    Gwamna Masari ya ce jami`ai sun dukufa wajen bin diddigin mutanen da likitan ya yi mu`amala da su domin gaggawar dakile bazuwar cutar a jihar.

  4. ‘Coronavirus ta hana miliyoyin mutane samun na abinci’

    Kungiyar kwadago ta duniya ILO ta ce barkewar cutar coronavirus ta yi mummunan tasiri ga ma’aikata da kuma abin da suke samu a duniya.

    Kungiyar tace mutum hudu cikin biyar na rayuwa a kasashen da aka kafa dokar hana fita, abin da ya ke janyo barazana ga rayuwar ma'aikata sama da biliyan daya.

    Ta ce duk da kasashe masu arziki sun samar da tallafi ga ‘yan kasuwa da ma’aikata, amma a kananan kasashe miliyoyan mutanen da ke sana’a ba a samar masu wata kariya ba.

    ILO ta bukaci gwamnatoci su hada kai domin gaggauta daukar matakai ga karuwar rashin ayyukan yi da kuma talauci

  5. An gurfanar da hukumar man fetur ta Ghana a kotu

    Kungiyoyin masu amfani da albarkatun man fetur na Ghana sun gurfanar da hukumar man fetur ta kasar saboda kara kudin gas ba tare da bin doka ba.

    A takardar karar da lauyoyin da ke wakiltar The Chamber of Petroleum Consumers Ghana (COPEC) da the Consumer Protection Agency (CPA) suka shigar a kotun ranar Talata, sun nemi ta yi watsi da harajin da hukumar man fetur din ta sanya, suna masu cewa bai kamata a dauki irin wannan mataki ba, sai da amincewar majalisar dokokin kasar.

    Lauyoyin, karkashin jagorancin kamfanin lauyoyi na Martin Kpebu, sun kuma bukaci kotun ta tilasta wa hukumar ta biya mutane harajin da aka soma cire musu na gas din.

    A ranar 1 ga watan Afrilu ne hukumar man fetur ta Ghana ta sanya harajin pesewas 13.5 kan ko wanne kilogiram daya na gas, lamarin da bai yi wa kungiyoyin dadi ba.

  6. Coronavirus: Kotu ta ki bayar da belin R Kelly

    Alkalin wata kotu a Illinois a Amurka ya yi watsi da bukatar shahararren mawakin nan R Kelly ta neman beli saboda tsoron cutar coronavirus,

    R Kelly ya nemi beli ne yana mai cewa cutar Covid 19 barazana ce ga al’umma

    Mawakin da ake tuhuma da laifin da ya shafi lalata da yara yana jiran shari’a ne a Chicago.

    Lauyan da ke kare R Kelly ya ce tilasta wa mawakin ci gaba da zama a gidan yari kamar tursasa masa ne ya sha guba.

    Masu fafutikar kare ‘yan gidan yari sun ce gidajen yari na cikin wuraren da za a iya kamuwa da cutar coronavirus saboda matsalar daukar matakai da suka shafi ba da tazara tsakanin mutane da kuma kula da tsabta.

  7. Coronavirus: Adadin masu mutuwa a Birtaniya a rana daya ya karu

    Yawan wadanda coronavirus ta kashe a asibitocin Birtaniya a rana ya kai 6,159 – inda aka samu karin 786 a rana daya.

    Bangaren kula da lafiya ya ce mutum 213,181 aka yi wa gwajin coronavirus a ranar Talata, inda gwajin ya tabbatar da mutum 55,242 na dauke da cutar.

  8. Shirin 'coronavirus ina mafita' kai-tsaye a Facebook

    BBC na nuna shirin 'coronavirus ina mafita' kai tsaye a shafin Facebook.

    Ana tattauna annobar cutar coronavirus tare da masana da kuma jin ra'ayoyin jama'a kan yadda cutar ta shafe su.

  9. Amurka ta ce ta kashe babban kwamandan al-Shabab

    Amurka ta ce ta kashe daya daga cikin wadanda suka assasa kungiyar al-Shabab Yusuf Jiis a wani harin sama da ta kai a Somalia.

    Al-Shabab dai ba ta ce komi ba kawo yanzu.

    Babban kwamandan Amurka a Afirka, Janar Stephen Townsend, ya bayyana Jiis a matsayin mai hatsari kuma babban mai kisa wanda ya rike manyan mukamai a kungiyar al-Shabab.

    Amurka ta tsawwala kai hare-hare a Somalia tun lokacin da shugaba Trump ya zama shugaban kasa.

  10. Coronavirus: Buhari ya yi wa Boris Johnson jaje

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike wa Firai Minsitan Burtaniya Boris Johnson sakon jaje kan rashin lafiyar da yake fama da ita ta coronavirus.

    A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar a aranar Talata, Buhari ya ce yana yi wa firai ministan fatan samun sauki da gaggawa.

    ''Shugaba Buhari na mika sakon jaje da na goyon baya ga shugaban Burtaniya a yayin da yake fama da cutar Covid-19, da kuma mutanen Burtaniya da ke cikin matsanancin yanayin da cutar ta sanya su ciki,'' in ji sanarwar

    Shugaba Buhari ya kuma yi addu'ar fatan samun sauki ga Mista Johnson don ya koma bakin aikinsa na ci gaba da jagorantar kasarsa a wannan hali da duniya ke cikin tashin hankali.

  11. Mai dauke da Coronavirus ta haihu a gidan killace jama'a

    Wata mata da take samun kulawa sakamakon kamuwa da coronavirus a wurin killace masu cutar da ke Yaoundé, babban birnin Kamaru, ta haifi jaririya a karshen mako, likitan da ya karbi haihuwar ya shaida wa BBC.

    Matar, mai shekara 19 mai suna Marie, ta haihu ne salin-alin ko da yake tuna aka dauke jaririyar daga gabanta.

    An sanya mata wani na'urar da ke sanya ta yin numfashi a lokacin da ta soma nakuda.

    Likitan mata da ya karbi haihuwar, Dr Yaneu Ngaha Bondja Junie, ya shaida wa BBC cewa: “Mun samu dakin da muka kai ta ta haihu a can ko da yake sanye take da na'urar da ke taimaka mata wurin yin numfashi."

    Jaririyar bakwanini ce inda nauyinta bai wuce 2.1kg kuma yanzu tana sashen kula da jarirai. Ba a sani ko ko jaririyar ta kamu da coronavirus domin kuwa har yanzu ana jiran sakamakon gwajin da aka yi mata.

  12. Covid-19: 'Za a kai lokacin da mutane za su soma faduwa suna mutuwa a Najeriya'

    Masana harkara lafiya a Najeriya sun fara nuna damuwa kan yadda jama'a ke daukar batun coronavirus, inda suke kunnen kashi da shawarwarin da jami'an lafiya ke bayarwa.

    Farfesa Usman Yusuf wanda shi ne tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta Najeriya ya ce abin da suke gani yana tayar wa da duk wani masanin harkokin lafiya hankali.

    A tattaunawarsa da Yusuf Ibrahim Yakasai, Farfesa Usman ya ce idan jama'a ba su sauya yadda suke daukan cutar ba, to za ta iya yin mummunar illa.

    Yusuf din Ya fara da tambayarsa yadda likitoci ke kallon ciwon.

  13. Covid-19: Masu karya dokar hana zirga-zirga sun yi tsallen-kwado

    Wani dan sanda lokacin da yake hukunta wasu da suka karya dokar hana zirga-zirga saboda Coronavirus a birnin Jabalpur na kasar Indiya ranar Talata.

    Ya zuwa ranar Talata, mutum 4908 ne suka kamu da cutar a India yayin da mutum 137 suka mutu, ko da yake mutum 382 sun warke daga cutar.

  14. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: An sallami karin mutum daya a Lagos

    Gwamnan jihar Lagos da ke Najeriya, Babajide Sanwo-Olu, ya ce an sallami karin mutum daya, wata mace, wacce ta warke daga coronavirus.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata.

    "Ina mai cike da farin ciki a yayin da nake sanar da ku cewa an sallami karin mutum (mace) daya wacce ta warke daga wurin da ake killace mutane a Yaba. Hakan na nufin mutanen da suka warke daga cutar jumulla sun kai 32 daga Lagos."

  15. An kashe 'masu shan jini da yada coronavirus'

    Mozambique ta bayyana rashin jin dadinta game da abin da ta kira kisan 'yan kasarta biyu a makwabciyar su Malawi.

    Ministar harkokin wajen kasar Veronica Macamo ta ce an kashe su ne bayan an zarge su da laifin shan jini da watsa coronavirus.

    Ta ce an kama wadanda ake zargi da yin kisan amma tana jiran takwaranta na Malawi ya tabbatar mata da hakan a hukumance.

    'Yan sanda sun ceto wani dan Mozambique kuma yanzu haka ana ba shi kariya.

    Mutanen uku suna kan hanyarsu ta zuwa Tanzania ne inda suka ratsa ta Malawi.

  16. Covid-19: Babban Bankin Najeriya ya yi gargadi kan 'yan damfara

    Babban Bankin Najeriya ya gargadi 'yan kasar bisa wasu bata-gari da ke amfani da halin da aka fada ciki na annobar coronavirus wajen damfarar mutane.

    Sanarwar da mai magana da yawun Babban Bankin, Isaac Okorafor, ya aike wa manema labarai ranar Talata ta "ja hankalin mutane cewa 'yan damfarar intanet suna amfani da wannan dama ta annobar “COVID-19” wajen damfarar 'yan kasa da sace bayanansu ko kuma yin kutse a kwamfyuta ko wayoyin salularsu ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa daban-daban."

    Babban Bankin ya ce 'yan damfarar suna yin amfani da hanyoyin sadarwa wurin aika wa da sakon imel ga mutane suna ikirarin cewa daga Hukumar Lafiya ta Duniya ko Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ne inda suke neman mutane su latsa mashigin shafin, amma da zarar sun yi hakan za su kai su shafin da za su damfare su.

    Ya kara da cewa babban burin Bankin shi ne ya wayar da kawunan masu hulda da shi game da wannan mugunyar dab'a domin kada su bari a damfare su.

  17. 'Ba a saka wa Boris Johnson na'urar taimakawa shan numfashi ba'

    Fadar gwamnatin Burtaniya ta ce Firai Minista Boris Johnson yana samun sauki bayan da ya shafe dare guda a bangaren kulawar gaggawa a asibiti sakamakon coronavirus.

    Mai magana da yawun fadar da ke Lamba 10 a Titin Dawning, ya ce firai ministan mai shekara 55 ya kasance cikin hayyacinsa da daren Litinin kuma an sa masa abin kara iska - amma ba a sa masa na'urar taimakawa shan numfashi ta ventilator ba.

    Wannan na zuwa ne bayan da wani daga cikin ministocinsa Michael Gove ya zamo na baya-bayan nan da ya killace kansa bayan da wani daga cikin ahalin gidansa ya nuna alamun cutar.

    Mista Gove ya ce bai nuna alamun cutar ba amma zai ci gaba da aiki daga gida.

    An kwantar da Mr Johnson a Asibitin St Thomas' a tsakiyar Landan bayan da alamun cutar suka ci gaba da bayyana a ranar Lahadi, daga nan aka kai shi wajen kulawa ta musamman a ranar Litinin da misalin karfe 7 na yamma agogon kasar, bayan da jikin ya yi tsanani.

  18. Coronavirus: Yadda mutane ke killace kansu a kan bishiya a India

    Dubban mutane a Indiya sun bar birane inda suka koma kauyukansu a yayin da aka sa dokar hana zirga-zirga, wacce ta janyo rudani da damuwa.

    A yanzu wasu mutanen a kauyuka suna killace kawunansu a kan bisihyoyi saboda gudun yada cutar ga danginsu da suka fi fuskantar hadarin kamuwa da ita.

    Latsa hoton da ke kasa don kallon bidiyon:

  19. Masu dauke da coronavirus a Saudiyya sun kai 2,752

  20. Coronavirus: A karon farko ba a samu wanda ya mutu a China ba tun Janairu

    A karon farko ba a samu rahoton mutuwa a China sakamakon coronavirus ba a ranar Talata, karon farko tun bayan da kasar ta fara wallafa mace-macen da ake samu a kullum tun a watan Janairu.

    Hukumar Lafiya Ta Kasar ta ce ta samu karin mutum 32 da suke dauke da cutar daga asubahin ranar Litinin.

    Hakan na zuwa ne a lokacin da kasar ke fuskantar zargi kan cewa tana boye alkaluma kan cutar.

    Gwamnatin kasar ta ce fiye da mutum 3,331 ne suka mutu sannan mutum 81,740 ne suka kamu da cutar.

    Dukkan wadanda aka gano suna dauke da cutar na ranar Talata sun koma kasar ne daga kasashen wajen.