Covid-19: Ghana ta yafe wa mutane kudin ruwa na wata uku
Gwamnatin Ghana ta ce ba za ta karbi kudin ruwan famfo daga 'yan kasar ba tsawon wata uku domin ta rage musu radadin da suke ciki sakamakon hana su fita daga gidajensu saboda covid-19.
Shugaba Nana Akufo-Addo ne ya bayyana haka ranar Lahadi a jawabin da ya yi wa 'yan kasar ta gidajen talbijin.
Ya ce gwamnati za ta tabbatar 'yan kasar sun rika samun ruwan sha da na amfanin gida akai-akai.
Wasu yankunan kasar ta Ghana na fama da karancin ruwan famfo a daidai lokacin da hukumomin lafiya suka bukaci mutane su yawaita wanke hannayensu da yin tsafta a mataki na hana yaduwar coronavirus.

Asalin hoton, Getty Images









