Karin mutum 8 sun kamu da coronavirus a Najeriya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita and Umar Mikail

  1. Coronavirus: An samu raguwar mutuwa a Sifaniya

    Mutum 674 ne suka mutu a Sifaniya a rana guda, wanda hakan ya kawo jumullar mace-macen da aka samu a kasar sakamakon coronavirus zuwa 12,4189.

    Wannan adadin da aka samu a yau shi ne mafi karanci a wannan makon inda har aka samu raguwa da mutum 135 kan mutuwar da aka samu a ranar Asabar.

    A jiya dai mutum 809 ne suka mutu a kasar.

    Sifaniya na daga cikin kasashen da coronavirus ta fi addaba a fadin duniya.

  2. Labarai da dumi-dumi, Mutum 10 sun sake kamuwa da coronavirus a Najeriya

    Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta tabbatar da cewa mutum 10 sun sake kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya.

    Hukumar ta ce mutum shida a Legas suke sai biyu a Abuja da kuma biyu a jihar Edo.

    An kuma kara samun mutum daya da ya mutu biyu kuma da suka warke wanda a halin yanzu mutum biyar ne suka mutu, an kuma sallami 27.

    Tun bayan fara bullar cutar, mutum 224 ne cutar ta harba a fadin Najeriya.

    Ga jerin jihohin da cutar ta bulla da kuma yawan mutanen da ta harba:

    • Lagos- 115
    • Abuja- 45
    • Osun- 20
    • Oyo- 9
    • Akwa Ibom- 5
    • Ogun- 4
    • Edo- 9
    • Kaduna- 4
    • Bauchi- 6
    • Enugu- 2
    • Ekiti- 2
    • Rivers-1
    • Benue- 1
    • Ondo- 1
    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Covid-19 ta kama mutum 8, 536 a Afirka

    Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka ta ce akalla mutum 8, 536 sun kamu da coronavirus a kasashe 50 mambobin kungiyar tarayyar Afirka ya zuwa Lahadi, 5 ga watan Afrilun 2020.

    A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta kara da cewa cutar ta kashe mutum 360, yayin da mutum 710 suka warke a nahiyar. Hakan na nufin ya zuwa yanzu Afirka ce nahiyar da cutar bata yi wa illa sosai ba.

    Sai dai masana harkokin lafiya sun gargadi mutane su ci gaba da zama a gidajensu sannan su bi shawarwarin kiwon lafiya irin su yawaita wanke hannu da sabulu ko man goge hannu na sanitizers, da barin tazara tsakaninsu da gujewa shiga taron jama'a da killace kai ga masu dauke da cutar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Kaduna da Kano na yunkurin koyar da dalibai ta rediyo da talabijin

    .

    Asalin hoton, @contactkdsg

    Jihohin Kaduna da Kano na yunkurin ci gaba da ilmantar da dalibai musamman 'yan ajin karshe a sakandare ta hanyar kafofin watsa labarai na Rediyo da Talabijin sakamakon annobar coronavirus da ta hana zuwa makaranta.

    Rahotanni daga jihar Kano na cewa tuni wani dan majalisar tarayya a jihar ya dauki nauyin fara karatun a rediyo, haka zalika wasu rahotanni na cewa ita ma gwamnatin jihar za ta bi sawun wannan yunkuri da dan majalisa ya yi domin daukar nauyin karatun a wasu gidajen redyio da talabijin.

    A jihar Kaduna kuma, tuni gwamnatin jihar ta fitar da jadawalin karatun dalibai na ajin karshe na sakandare inda ta ce za a fara koyar da karatun ta rediyo da talabijin.

    Ma'aikatar ilimi ta jihar ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter inda ta ce za a rinka koyar da karatun ga 'yan aji shida na sakandare.

  5. Akwai marasa bin shawara a Birtaniya – Sakataren Lafiya

    .

    Asalin hoton, Press Association

    Sakataren lafiya na Birtaniya Matt Hancock ya koka kan cewa har yanzu akwai wasu tsirarun mutane da ba su bin shawarwarin da gwamnatin kasar ta bayar na zama gida a yunkurin dakile coronavirus.

    Jawabin nasa na zuwa ne bayan hukumomi a kasar sun bayyana cewa har yanzu akwai masu zuwa wuraren shakatawa su taru da kuma masu zuwa bakin teku domin yin wanka da rana.

    Ko a watan da ya gabata sai da sakataren lafiyar wanda shi ma ya kamu da cutar ya bayyana cewa akwai mutanen da ba su bayar da tazarar a tsakaninsu wanda hakan kan iya jawo kamuwa da cutar cikin sauki.

    A yanzu haka dai sama da mutum 4,000 ne suka mutu sakamakon coronavirus a Birtaniya

  6. Coronavirus ta bulla a rukunin gidajen NNPC na Abuja

    .

    Asalin hoton, @NNPCgroup

    An samu bullar coronavirus a rukunin gidajen NNPC da ke unguwar Garki a Abuja babban birnin Najeriya.

    A wata sanarwa da ya fitar a shafin Twitter, kamfanin man fetir na Najerya ya tabbatar da bullar cutar, sai dai ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa jama'a da dama mazauna gidajen sun kamu.

    Kamfanin ya bayyana cewa wanda ya kamu da cutar ba ma'aikacin kamfanin bane, amma an gane cewa yana dauke da cutar bayan ya dawo daga Birtaniya a kwanakin baya, sai ya fara nuna alamomin cutar wanda hakan ya sa aka yi masa gwajin cutar.

    Kamfanin ya bayyana cewa tuni aka killace duka mazauna gidan da aka samu bullar cutar domin gujewa bazuwarta, haka zalika kamfanin ya shaida cewa tuni aka yi feshin magani a yankin da lamarin ya faru.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Mutum nawa suka kamu da coronavirus a Najeriya?

    Adadin mutanen da suka kamu da cutar matsalar numfashi ta coronavirus a Najeriya ya kai 214, kamar yadda hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasar NCDC ta bayyana.

    A daren jiya Asabar, hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ce an sake samun mutum biyar da suka kamu da cutar - uku a Bauchi sai biyu a Abuja, babban birnin kasar.

    Ga jerin jihohin da cutar ta bulla da kuma yawan mutanen da ta harba:

    • Lagos- 109
    • Abuja- 43
    • Osun- 20
    • Oyo- 9
    • Akwa Ibom- 5
    • Ogun- 4
    • Edo- 7
    • Kaduna- 4
    • Bauchi- 6
    • Enugu- 2
    • Ekiti- 2
    • Rivers-1
    • Benue- 1
    • Ondo- 1
    .

    Asalin hoton, @NCDCgov

  8. Farawa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin barkanmu da wannan rana ta Lahadi. Wannan shafin zai rinka kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya musamman kan coronavirus.