Karin mutum 8 sun kamu da coronavirus a Najeriya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Jama'armu karshen rahotannin kenan. BBC na fatan mu kwana lafiya.

  2. Labarai da dumi-dumi, An kai Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson asibiti

    An kai Firai Ministan Birtaniya, Boris Johnson, asibiti domin yin gwaji kwana 10 bayan ya kamu da cutar coronavirus, a cewar fadar shugaban.

    An kai shi wani asibiti a Landan a daren Lahadi dauke da alamomin cutar ciki har da zafin jiki.

    An ce matakin na riga-kafi ne bayan likitansa ya bayar da shawarar yin hakan, amma sakataren harkokin waje ne ake sa ran zai jagoranci wata ganawa kan coronavirus a ranar Litinin.

  3. Labarai da dumi-dumi, Wasu mutum 8 sun kamu da coronavirus a Najeriya

    Hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya ta ce an samu karin mutum takwas da suka kamu da coronavirus.

    Biyar daga cikinsu suna Jihar Legas, biyu a Abuja da kuma daya a Kaduna.

    Jumullar wadanda suka kamu da cutar sun zama 232 kenan, a cewar hukumar - 33 daga cikinsu sun warke, biyar sun mutu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Kayan gwajin coronavirus daga China ba sa dauke da cutar - NCDC

    Hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya ta yi watsi da ikirarin da wasu ke yi cewa kayayyakin gwajin cutar coronavirus da aka kawo daga China suna dauke da kwayar cutar.

    A wani sako na tambaya da amsa kan cutar Covid-19 da ta wallafa a shafin Twitter, hukumar ta ce "babu wata hujja da ke tabbatar da cewa akwatinan suna dauke da kwayar cutar.

    Ta kara da cewa "lafiyarsu kalau idan ma'aikatan lafiya suka yi amfani da su ta hanyar da ta dace".

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. 'Birtaniya za ta yi nasara a yaki da coronavirus'

    Sarauniya Elizabeth

    Asalin hoton, BUCKINGHAM PALACE

    Sarauniya Elizabeth ta ce Birtaniya "za ta yi nasara" a yakin da take yi da annobar coronavirus a jawabin da ta yi wa kasa.

    A cikin jawabin da ba kasafai take yi ba, Sarauniya ta gode wa mutane bisa bin dokar da gwamnati ta saka ta zaman gida sannan ta yaba wa "wadanda suka fito domin taimakon wasu".

    Kazalika ta yi godiya ga ma'aikata, tana cewa "kowacce sa'a" ta aiki "tana kusanta mu da komawa cikin kwanciyar hankali".

    Jawabin na zuwa ne yayin da adadin wadanda suka mutu a kasar sakamakon cutar ya kai 4,934.

    Jawabin da ba a saba gani ba

    Ban da jawabin ranar Kirsimeti na shekara-shekara, sau hudu kacal Sarauniya ta taba yin wani jawabi a tsawon shekara 68 da ta yi a kujerar sarautar Birtaniya.

    Sauran lokutan da ta yi jawabi sun hada da; bayan gama yakin yankin Gulf, bayan mutuwar gimbiya Diana, mutuwar Yariman Wales, mutuwar mahaifiyarta, sai kuma lokacin cikarta shekara 60 a kan karaga.

  6. A jawabin Sarauniya...

    Saurauniya Elizabeth II ta yi wa jama'ar Birtaniya alkawarin cewa kwanaki masu dad na zuwa, tana mai cewa "za mu sake ganawa".

    Ta ce: "Ya kamata mu nutsu yayin da har yanzu akwai abin da ke tafe na alhini, kwanaki masu kyau na nan tafe; za mu sake haduwa da abokanmu; za mu sake haduwa da iyalanmu; za mu sake ganawa."

  7. Coronavirus ta kashe wasu mutum 357 a Faransa

    Faransa ta bayyana mutum 357 da suka rasa rayukansu sakamakon annobar coronavirus a cikin awa 24 da suka gabata - bayan adadin 441 na ranar Asabar.

    Kasar wadda ke cikin dokar hana fita tsawon mako uku, yanzu tana da jumullar mutum 5,889 da suka mutu a asibiti, asu 2,189 sun mutu a gidajen kula da gajiyayyu, a cewar hukumomi.

    Baki dayan wadanda suka mutu ya kama 8,078. Wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar kuwa sun kai 90,864.

  8. Sarauniyar Ingila za ta yi jawabi kan coronavirus

    Sarauniya Elizabeth

    Asalin hoton, Getty Images

    Nan gaba kadan Saurauniya Elizabeth za ta yi wa 'yan Birtaniya jawabi game da yakin da ake yi da annobar coronavirus - abin da ba a saba gani ba.

    Za a yada shi ta kafar talabijin da rediyo da karfe 8:00 agogon Najeriya da Nijar.

    Ban da jawabin ranar Kirsimeti na shekara-shekara, sau hudu kacal Sarauniya ta taba yin wani jawabi a tsawon shekara 68 da ta yi a kujerar sarautar Birtaniya.

    Sauran lokutan da ta yi jawabi sun hada da; bayan gama yakin yankin Gulf, bayan mutuwar gimbiya Diana, mutuwar Yariman Wales, mutuwar mahaifiyarta, sai kuma lokacin cikarta shekara 60 a kan karaga.

  9. A wani labarin daban...

    Hansi Flick

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai horas da Bayern Munich, Hansi Flick ya amince ya tsawaita kwantiragin ci gaba da jan ragamar kungiyar zuwa karshen kakar 2023.

    Mai shekara 55, ya koma Munich a farkon kakar bana a matsayin mataimakin Nico Kovac.

    Sannan watakila hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta kara shekarun 'yan kwallon da suka cancanci buga gasar Olympics daga 23 zuwa 24.

    Fifa na fatan daukar wannan matakin a lokacin Olympics da birnin Tokyo na Japan zai karbi bakunci a 2021.

  10. Mai shekara 104 ta warke daga coronavirus

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Tun farko akwai rahotannin da ke cewa adadin masu harbuwa da annobar coronavirus a Italiya ka iya raguwa - a ranar Lahadi, an samu adadi mafi kankanta na wadanda suka mutu a tsawon sati biyu.

    A karshen makon nan kuma sai ga labarin wata dattijuwa mai shekara 104 da ta warke ras daga cutar.

    Ada Zanusso tana zaune ne a Lessona da ke arewacin Italiya a wani gidan kula da gajiyayyu - mutum 20 ne suka mutum a gidan.

    Likitanta mai suna Carla Furno Marchese ya fada wa jaridar La Republica cewa: "Tana cikin hayyacinta da tunaninta. Warkewarta wani lada ne ga duk wadanda suka kula da ita a irin wannan lokacin."

    Ba ita kadai ce tsohuwa tukuf da ta warke daga cutar ba, amma labarinta zai karfafa gwiwa yayin da ake ta samun rahotannin mutuwa a kodayaushe.

  11. Funke Akindele na shan suka kan bikin da ta shirya a gidanta duk da dokar hana fita

    Funke Akindele

    Asalin hoton, Funke Akindele

    Duk wanda ya leka shafin Twitter a yau Lahadi zai ga an yi wa shahararriyar tauraruwar fina-finan kudancin Najeriya wato Funke Akindele ca, inda sunanta ke cikin manyan maudu'an hira.

    Dalili shi ne; ta hada bikin murnar ranar haihuwar mijinta, JJC Skillz.wanda shi ma mai bayar da umarni ne, a gidanta da ke Legas duk da dokar hana fita da aka saka a Jihar.

    Funke Akindele na cikin wadanda suka dinga wayar da kai a kan coronavirus a cikin wani bidiyo da hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa ta shirya.

    Sai dai tauraruwar ta ce baki dayan mahalarta bikin sun shafe sati biyu a gidan nata kafin shagalin.

    Amma fa tuni ta goge sakon na Twitter da ta wallafa.

    Funke Akindele

    Asalin hoton, Twitter/Funke Akindele

    Babu tabbas ko adadin wadanda suka halarci shagalin sun wuce 20, wanda shi ne adadin da dokar zaman gida ta ayyana a Jihar a matsayin haramtacce - duk da haka mutane sun soke ta saboda koya wa wasu abin da bai dace ba.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Wani ya ce ya zaci kamar akwai dokar hana fita, "amma ta yaya wannan cincirindon mutanen suka kai kansu wurin?"

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Shi kuwa wani mamaki ne ya turnuke shi; "ta yaya za a ce Naira Marley ya yi sati biyu a gidanta!"

    Kauce wa X, 3
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 3

  12. Cibiyoyin gwajin coronavirus a Legas sun zama 9

    Legas

    Asalin hoton, @LSMOH

    Hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a Najeriya ta sake kaddamar da wani dakin gwajin cutar Covid-19 a Jihar Legas.

    Wani dakin gwajin Biosafety Level-3 aka yi wa kwaskwarima zuwa na gwajin Covid-19, a cewar hukumar.

    Wannan ya sa adadin cibiyar gwajin cutar ya zama tara kenan a Legas.

    Hukumar ta ce yanzu jihohin Kano da Borno da Sokoto da Fatakwal da Filato da Kaduna ta saka a gaba domin bude irin wadannan cibiyoyi.

    Zuwa yanzu mutum 224 ne suka kamu da annobar cutar Covid-19 a Najeriya.

    Mutum biyar ne suka mutu, an kuma sallami 27 bayan sun warke daga cutar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Za a ci gaba da harkokin kasuwanci "marasa hadari" a Iran

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Iran ta ce za ta kyale harkokin kasuwanci "marasa hadari sosai" su ci gaba a kasar daga 11 ga Afrilu yayin da wadanda ke harbuwa da coronavirus ke raguwa cikin kwana biyar a jere.

    Shugaba Hassan Rouhani ya fada ranar Asabar - a wani rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP: "Ci gaban harkokin ba ya nufin miun bar maganar zama a gida."

    Shugaban wanda kasarsa ke fama da takunkuman tattalin arziki da Amurka ta sanya mata, bai bayyana harkokin da ya kira "marasa hadari" ba amma ya ce makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe da kuma hana taron jama'a.

    A babban birnin kasar kuwa na Tehran, Rouhani ya ce za a dawo da harkokin kasuwanci "marasa hadari" daga ranar Asabar 18 ga watan Afrilu.

    Mutum 58,226 ne suka kamu da coronavirus a Iran, 3,603 suka mutu.

  14. Najeriya ta ware naira biliyan 500 don yakar coronavirus

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Nigerian Government

    Gwamnatin Najeriya na shirin kirkirar wata gidauniya ta kudi naira biliyan 500 domin inganta sashen lafiya a kasar a yakin da take yi da annobar cutar coronavirus, kamar yadda hukumomi suka bayyana a ranar Asabar.

    Ministar Kudi Zainab Ahmed ta gana da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan da takwaransa na Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, inda suka amince cewa za a tattaro kudin ne daga asusun ma'aikatu daban-daban na kasar.

    Kazalika za a ciyo bashin wasu kudin daga cibiyoyin bayar da bashi na kasashen duniya, kamar yadda suka bayyana a wani bayani wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

  15. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus ta kashe tsohon firai ministan Libya

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafafen yada labarai a Libya sun ruwaito cewa Tsohon Firai Ministan kasar Mahmoud Jibril ya mutu bayan ya yi fama da jinyar cutar coronavirus a wani asibiti da ke Masar.

    Jam'iyyar Mista Jibril wato National Forces' Alliance ta bayyana cewa an yi wa tsohon firai ministan gwajin cutar a ranar 26 ga watan Maris inda aka gano yana dauke da ita.

    Kafin rasuwarsa, Jibril na daga cikin 'yan tawayen da suka jagoranci hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a 2011.

  16. Japan na azamar ninka yawan wata kwaya don yaki da coronavirus

    Japan

    Asalin hoton, Getty Images

    Japan na kara yawan wata kwayar magani da masana suka yi imanin cewa za a iya amfani da ita wurin jinyar masu dauke da Covid-19.

    Kwayar maganin wadda ake kira da Avigan ko favipiravir, wasu likitoci a China sun yi amfani da ita domin kula da wadanda suka fara kamuwa da cutar a birnin Wuhan na China, inda cutar ta fara bayyana.

    Gwaji har karo biyu da aka yi ya nuna cewa kwayar tana rage yawan kwanakin jinyar coronavirus. Wata kafar yada labarai a kasar ta ce Japan na fatan samar da ninki biyar na kwayar domin a samu damar bai wa mutum miliyan biyu.

    Wani bangare na kamfanin kera kyamara mai suna Fujifilm ne ya kirkiri kwayar. Zai fara yin gwaji da zai kai har zuwa karshen watan Yuni.

    Kwayar na da tata illar, in ji kwararru, amma dai har yanzu tana daya daga cikin wadanda ake da su domin yakar annobar cutar.

  17. 'Yan Kenya na korafin rashin tausayi a cibiyar killace masu coronavirus

    Mutanen da aka killace a Kenya sakamakon harbuwa da coronavirus na kokawa dangane da yadda ake gallaza musu a wurin da ake kula da su.

    Sama da mutum 2,000 ne ciki har da 'yan kasar da kuma baki aka tilasta wa zama a otel da kuma wuraren killlacewa na gwamnati.

    Tun a baya dai gwamnatin kasar ta saka doka ga duk wanda ya shiga kasar da a killace shi na tsawon kwana 14.

    A halin yanzu, ana kara wa'adin zaman masu dauke da cutar a duk wurin killacewar da aka tabbatar da bullarta daga mako biyu zuwa wata daya.

    Wasu daga cikin mazauna wuraren killacewar sun bayyana cewa ana kula da su tamkar 'yan fursuna.

    Tun a baya dai sun koka kan cewa ba sa samun kayayyakin amfani kamar ruwa da sabulu.

    Sai dai Ministan Lafiya na kasar Mutahi Kagwe ya zargi wadanda aka killace da cewa suna karya dokokin da aka gindaya musu, inda har wasu daga cikinsu ke zuwa gidajen rawa.

  18. Labarai da dumi-dumi, Mutum 621 sun mutu a rana guda a Birtaniya

    Mutum 621 ne suka mutu a rana guda a Birtaniya sakamakon cutar coronavirus.

    A halin yanzu, adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar a kasar sun kai 4,934 daga 4,313 a jiya Asabar.

    Mutum 47,806 ne aka tabbatar sun kamu da cutar tun bayan da ta bulla a kasar.

    .

    Asalin hoton, Getty Images

  19. Adadin masu coronavirus na karuwa a Afirka ta Kudu

    Adadin wadanda suka kamu da coronavirus a Afirka ta Kudu na kara karuwa inda a yanzu haka mutum 1,585 suka kamu da cutar.

    Hukumomi a kasar sun gano wani asibiti a lardin Kwa-Zulu wanda ake zargi a matsayin matattara ta cutar.

    Mutum tara ne suka mutu a halin yanzu sakamakon cutar ta Covid-19.

    Mutum shida cikin tara da suka mutu a kasar sun fito ne daga lardin na Kwa-Zulu.

  20. Labarai da dumi-dumi, Ma'aikata za su koma aiki ranar Litinin a jihar Neja

    Gwamnatin jihar Neja a Najeriya ta umarci ma'aikatan gwamnati a jihar daga mataki na daya zuwa na 12 da su koma bakin aiki ranar Litinin.

    Sai dai duk da haka dokar takaita zirga-zirga a jihar na nan daram kamar yadda gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ya tabbatar.

    Sai dai a halin yanzu an sassauta dokar takaita zirga-zirga a jihar inda mazauna jihar za su iya gudanar da hidimominsu daga 8:00 na safe zuwa 2:00 na rana.

    Gwamnatin ta jaddada cewa duka sauran dokokin da aka saka na hana taro da zuwa makaranta da zuwa wuraren ibada na nan daram.