Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin yana kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Tsohon jami'in gidan yari ya kashe kansa a kotu

    Wani tsohon ma'aikacin gidan yari a Rasha ya kashe kansa a kotu bayan da aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara uku.

    Viktor Sviridov ya taba zama shugaban sashen sufuri na hukumar kula da gidajen yarin kasar.

    An same shi da laifin karbar £121,000 daga hannun tsohon mataimakin shugaban hukumar.

    Mintuna kadan bayan alkalin kotun ya umarci a mika shi gidan yari, Sviridov ya harbi kansa da bindiga.

    An rawaito mai magana da yawun kotun tana cewa ana zargin Sviridov ya shiga harabar kotun da bindiga a jikinsa.

    Tuni 'yan sanda suka isa wajen kuma hukumomi sun sanar da fara bincike kan lamarin a cewar kamfanin dillancin labarai na RIA.

    Wasu rahotannin kuma na cewa Sviridov yana fama da cutar kansa inda ake tsare da shi a gida kafin shari'ar.

  2. Yadda wata mata ta kashe jaririnta a jihar Jigawa

    'Yan sanda a Najeriya sun ce suna ci gaba da bincike don gano dalilin mutuwar wani jariri da aka haifa aka kuma binne shi a daren haihuwarsa.

    Lamarin da ya auku a karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa a arewa maso yammacin kasar, ya janyo ce-ce ku-ce a tsakanin jama’a, har ta kai ga an tono gawar jaririn domin aiwatar da bincike.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar DSP Audu Jinjiri ya ce mahaifiyar jaririn ce ta halaka shi.

    ''Ta hada baki da wata kishiyar babarta kuma bayan ta je an yi mata allura a wani kauye da ke Sankara ta haifi yaron da ransa amma suka kashe shi suka shiga bayan gari kuma suka binne,'' in ji Jinjiri.

  3. Birtaniya ta dakatar da bai wa Commonwealth kudi

    BBC ta fahimci cewa gwamnatin Birtaniya ta dakatar da bai wa sakatariyar kungiyar kasashen rainon Ingila kudi.

    Birtaniya ce ta kafa kungiyar wacce ke da hedikwata a birnin London.

    Jami'an difilomasiyya na kasar sun shaida wa Lady Scotland, sakatariyar kungiyar Commonwealth, cewa Birtaniya ta dakatar da £4.7m da take bai wa kungiyar don radin kanta har sai sakatariyar ta inganta yadda take gudanar da harkokin kudinta.

    Sakatariyar ta dage cewa tana aiwatar da shawarwarin da masu binciken kudin da ke zuwa daga waje suka ba ta.

  4. Labarai da dumi-dumi, Shugaba Buhari ya kai ziyara Maiduguri bayan harin Boko Haram

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Maiduguri babban birnin Borno bayan ya dawo daga Addis Ababa.

    Mai bai wa shugaban kasar shawara kan kafafen yada labarai Garba Shehu ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

    Ya ce Buhari ya je ne domin jajanta wa gwamnati da al'ummar Borno kan harin ta'addancin da aka kai jihar a baya-bayan nan.

    Harin wanda Boko Haram ta kai ya halaka matafiya da dama.

  5. Kotu ta bukaci gwamnatin Buhari ta biya Sowore N200,000

    Babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeriya ta dage sauraron shari'ar Omoyele Sowore da Olawale Bakare zuwa 13 ga watan Fabrairu.

    Mai shari'a Ijoema Ojukwu ce ta dage karar bayan da ta ce lauyan gwamnati Kayode Alilu na janyo tsaiko a batun sauraron karar.

    Mai shari'ar ta kuma bukaci lauyan gwamnatin ya biya naira dubu dari biyu ga wadanda ake kara saboda jan kafar da suka haifar.

    Rahotanni na cewa bayan da Ijeoma Ojukwu ta fara sauraron karar, lauya mai gabatar da kara ya tashi ya yi bayanin cewa tun da babban atoni na kasar ya karbi ragamar karar suka yanke hukuncin yin gyare-gyare a tuhumar da ake yi wa Sowore.

  6. Nissan na neman diyyar $90m daga tsohon shugabansa Carlos Ghosn

    Kamfanin kera motoci na Nissan ya shigar da kara kan tsohon shugabansa Carlos Ghosn.

    Karar da aka shigar a kotun Yokohama na neman diyyar dala miliyan 90.

    Kamfanin ya ce ya na son ''mayar da asarar da ya yi ta sanadiyyar tsohon shugaban.''

    A yanzu dai Mr Ghosn na Lebanon bayan da ya ki bayyana gaban kotu a Japan inda yake fuskantar tuhume-tuhumen almundahana.

    Nissan ya ce yana fatan kudin da aka karba ya "karu a nan gaba" yayin da yake kokarin maido da tarar da yake tsammanin biya sakamakon abin da ake zargin Ghosn da aikatawa.

    Kamfanin ya kuma ce zai iya shigar da wata kara kan abin da ya kira kalaman ''bata suna'' da Mr Ghosn ya yi a wani taron 'yan jarida da aka gudanar a Beirut.

  7. An kwashe ma'aikata 300 daga banki saboda coronavirus

    An kwashe kimanin ma'aikata 300 daga babban bankin Singapore, DBS, bayan wani mutum ya kamu da cutar coronavirus a cikin bankin.

    Dukkan ma'aikata 300 na aiki ne a hawa na 43 da ke cikin bankin, kuma an gaya musu su tafi gida ranar Laraba.

    A baya dai Singapore ta bayar da rahoton samun mutum 47 da suka kamu da cutar - inda ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fi fama da cutar baya ga China.

    Baki daya, mutum 44,000 suka harbu da cutar a China, inda kuma kashe fiye da 20 suka ce suna fama da ita.

    An yi wa ma'aikacin banki na DBS gwaji ranar Talata inda aka tabbatar ya kamu da cutar ranar Laraba.

  8. 'Yan bindiga sun kone mutum 16 da ransu a Kaduna

    'Yan bindiga sun kone kimanin mutum 16 'yan gida daya lokacin da suka ka hari a kauyen Bakali da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna ta arewacin Najeriya.

    Wakilin jaridar Daily Trust, ya ce an kai harin ne ranar Talata da misalin karfe hudu na asubahi inda suka banka wa buhunhunan hatsi da ababen hawa da babura wuta.

    Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun kulle mutanen 16 a cikin daki sannan suka banka masa wuta.

    Wani mazaunin garin, Alhaji Sani Bakali, ya shaida wa jaridar cewa kimanin 'yan bindiga 100 suka yi wa kauyen dirar mikiya.

  9. 'Matan Liberia ba su cancanci shiga soja ba'

    Mata da dama da suka nemi shiga aikin soja a Laberiya basu yi nasara ba saboda ba su da azamar iya aikin, a cewar hukumomin sojin kasar.

    Masu daukar aikin basu dauki kashi takwas cikin dari na matan da suka nemi aikin ba.

    Hafsan sojin kasa na kasar, Manjo Janar Prince C Johnson, ya ce: ''Dole duk wanda ke neman aikin ya iya yin wani adadin motsa jiki da kuma gudun mil biyu.''

    Mata daga yankunan karkara sun samu maki mai yawa a wajen iya atisayen, amma a wajen jarrabawa kuma ba su ci da kyau kamar matan birane ba, a cewarsa.

    Janar din ya ce ''Ba na kaskantar da kowane addini, amma wannan ne abin da bincikenmu ya tabbatar mana.''

    Tun bayan yakin Laberiya, sai mai neman aikin soja yana da a kalla takardun kammala sakandire.

    Ya ce rundunar sojin ta yanke shawarar yi wa matan da ke son shiga soji wani dan gwajin atisaye kafin babbar jarrabawar.

    Bayan matan sun haye gwajin lafiya sai kuma sun yi wani atisaye mai tsauri.

    Hafsan sojin ya ce: ''Za mu dauki mako hudu muna gwada mutum.''

  10. Matawalle ya sha alwashin kwato naira biliyan 90 daga hannun Yari

    Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya rantse cewa sai ya karbo naira biliyan 90 daga hannun tsohon gwamnan jihar Abdul'aziz Yari wadanda ake zargi ya karkatar da akalarsu ta hanyar yin aringizon kwantaragi, a cewar jaridar Punch.

    Matawalle, wanda ya bayyana haka lokacin gabatar da wani rahoton kwarya-kwarya na kwamitin da aka dora wa alhakin tantance ayyyukan jihar, ya ce ba zai karaya ba har sai ya kwato dukkan kudin da aka karkatar da akalarsu daga jihar.

    Gwamna Matawalle ya ce: “Zan aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar ta hanyar tabbatar da ganin an hukunta duk mutumin da aka samu da laifi.”

  11. ‘Yan ta’adda na amfani da shafukan zumunta don samun mambobi – Pantami

    Ministan sadarwa da tattalin arzikin intanet na Najeriya, ISA Ali Pantami, ya yi ikirarin cewa ‘ya ta’adda na amfani da shafukan sada zumunta na zamani domin daukar sabbin mambobi da kuma tsara yadda za su kai hare-hare.

    Jaridar Daily Trust, wacce ta ambato ministan yana wadannan kalamai a wurin taro kan yadda za a dakile ta’addanci da aka gudanar a Abuja, ta ce Malam Pantami ya ce akwai bukar samar da hanyoyin hikima wajen dakile ta’addanci da kuma hana faruwarsa baki daya.

    “A fili yake cewa ‘yan ta’adda na amfani da shafukan sada zumunta, da hanyar boye yadda ake sadarwa wajen watsa farfaganda da kuma samun sabbin mambobi,” in ji ministan.

    Ya yi kira ga jami’an tsaro su yi amfani da fasaha wurin shawo kan ‘yan ta’adda da kuma dakile hare-haren da suke kai wa jama’a.

  12. An gargadi bangarorin da ke fada da juna a Sudan ta Kudu

    An gargadi bangaren gwamnati da na 'yan hamayyar Sudan ta Kudu a kan yin "gaban kansu" bayan tattaunawar sulhun da suka yi don kawo karshen fadan da aka kwashe fiye da shekara shida ana yi a kasar ta ci tura a wannan makon.

    Amurka da Birtaniya da Norway sun bukaci Shugaba Salva Kiir da abokin hamayyarsa Riek Machar su amince kan yawan jihohin kasar, kamar yadda aka shata a yarjejeniyar da aka kulla a baya, ko kuma a kama su da laifin yin kafar-ungulu ga yarjejeniyar.

    An bai wa Shugaba Kiir da Mr Machar wa'adin ranar 22 ga watan Fabrairu domin su cimma matsaya kan kafa gwamnatin hadin-gwiwa.

    Taron da shugabannin biyu suka yi a farkon makon nan a Addis Ababa, babban birnin Habasha, ya gaza cimma matsaya. Gwamnatin Sudan ta Kudu tana so a kafa jihohi 32 yayin da bangaren Riek Machar ke son a dawo kan jihohi 10 kamar yadda yake a baya.

    Amurka da Birtaniya da Norway sun yi gargadin ne a wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba.

  13. Cocin Katolika ta ce an yi magudi a zaben Kamaru

    Kungiyar limaman cocin katolika a Kamaru ta bayyana matsayinta game da zabukan 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a kasar makon jiya.

    A wani taron manema labarai, Abraham Kome, ya yi zargin tafka magudi a mazabu da dama.

    A cewarsa, masu sa ido 17 da kungiyar limaman cocin ta aika yankin rainon Ingila basu samu damar gabatar da aiki ba saboda rashin tsaro da ya tsananta masamman a ranar zabe.

    Amma gwamnatin kasar ta ce zaben ya tafi yadda ya kamata.

    Ana sa ran za a fitar da sakamakon zaben nan da mako uku.

  14. Omoyele Sowore ya sake gurfana a kotu

    Mawallafin jaridar nan ta Sahara Reporters da ake buga wa a intanet, Omoyele Sowore, ya sake gurfana a gaban wata kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya ranar Laraba domin ci gaba da shari'ar da ake yi masa kan zargin cin amanar kasa.

    Wanna ne karon farko da Mr Sowore yake gurfana a gaban kotu tun bayan da hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta sake shi ranar 25 ga watan Disambar 2019.

    Kafin sakin nasa, DSS ta tsare Mr Sowore tsawon kwana 125 duk da umarnin kotuna daban-daban na sakinsa.

    Sai dai gada bisani matsin lsamba daga gwamnatin Amurka ya sa an saki mawallafin jaridar ta intanet, ko da yake a wancan lokacin ministan shar'ar Najeriya, Abubakar Malami, ya ce sun sake shi ne ba tare da fuskantar matsin lamba ba.

    Wasu fitattun 'yan Najeriya, irinsu marubuci Farfesa Wole Sonyinka da Sanata Shehu Sani da kuma masu rajin kare dimokrayya ne suka yi wa Mr Sowore rakiya kotun.

  15. 'Kalubalen yawan al'umma tamkar na ta'addanci ne'

    Kidayar da aka yi a kasar Masar ta nuna cewa yawan ‘yan kasar ya kai mutum miliyan 100, inda ake haifar jariri daya a kowacce dakika 18.

    Firai Minista Mostafa Madbouly ya bayyana cewa yawan al’umma shi ne babbar matsala daya kacal da ke addabar Masar.

    Shugaba Abdul Fattah al-Sisi ya kwatanta kalubalen yawan al’umma da cewa tamkar na ta’addanci ne.

    Kwanakin baya, hukumomi a kasar sun dauki matakan da za su sanya mutane su rika haifar ‘ya’ya kadan.

    An samu karuwar matan da ke haihuwa a kasar cikin shekara 30 – daga mutum 57 m a 1990.

  16. Shin Buratai ya ce zai fallasa masu daukar nauyin ta’addanci?

    Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta bayyana labarin da ake yadawa cewa shugabanta ya sha alwashin fallasa masu daukar nauyin ta’addanci da cewa labarin karya ne.

    Wata jarida ce ta wallafa labarin ranar Talata da ke cewa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya ce ‘yan kasar za su yi matukar kaduwa idan ya fallasa masu daukar nauyin ‘yan ta’adda.

    Amma a wani sako da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce “Wannan labarin karya ne. Wannan labarin karya ne.”

    Hare-haren ‘yan ta’adda dai na ci gaba da karuwa a kasar, lamarin da ya sa ‘yan Najeriya suka kara kaimi wurin yin kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya cire hafsoshin sojin kasar, ciki har da Mr Buratai.

  17. Barkanmu da sake saduwa

    Barkanmu da sake saduwa a wannan shafi da ke kawo muku labarai da rahotanni da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da wasu sassan duniya.

  18. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi a nan muka kawo karshen rahotanni da labaran wannan rana ta Talata 11 ga watan Fabrairun 2020.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

    Kuna iya duba kasa don karanta duk labaran da muka kawo muku yau har ma da na jiya.

    Asuba ta gari.

  19. Jam'iyyar BJP mai mulkin kasar Indiya na gab da shan kaye a babban zabe

    Jam'iyyar BJP mai mulkin kasar Indiya na gab da shan kaye a babban zaben da aka gudanar a Delhi babban birnin kasar.

    Rahotanni daga hukumar zaben sun nuna cewa jam'iyyar Firai Minsita Narendra Modi tana fafutukar ganin ta sami kujeru goma a a majalisar dokokin kasar.

    Jam'iyyar Aam Aaadmi mai sassaucin ra'ayi karkashin jagorancin Arvind Kejriwal tana kan gaba da kujeru sama da 60.

    Batutuwan ci gaban kasar, da suka hadar inganta tsarin Ilimi, kiwon lafiya, ga alama sun taka rawa sosai wajen aiwatar da ayyukan jam'iyyar.

    Da yake jawabi ga magoya bayansa, Mista Kejriwal ya ce Indiya a shirye take da sabon tafarkin da zai samar da ci gaba.

    "Mutanen Delhi sun bullo da wani sabon tsari na siyasa.

    ''Wannan sako ne mai kyau ga kasarmu kuma irin nau'in siyasar da za ta ciyar da Indiya gaba a karni na 21."

    Masu suka sun ce yakin nenam zaben da aka yi ya haifar da rarrabuwar kawuna daga wasu shugabannin jam'iyya mai mulki ta BJP.

  20. Atiku ya yi kiran hadin kai kan ayyukan Boko Haram

    Dan takarar jam'iyyar Adawa ta PDP a zaben Fabarairun 2019 a Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya jaddada kiran hada kai tsakanin Musulmi da Kirista game da ayyukan kungiyar Boko Haram.

    Atiku ya yi wannan kira ne sakamakon harin da kungiyar ta kai a daren ranar Lahadi, inda ta kashe kusan mutum 30 ta hanyar kona wasunsu a cikin motocin da suke kwance a kan hanyar shiga garin Maiduguri.

    Shi ma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Alllah-wadai da harin.