Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin yana kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. An hana matar mataimakin shugaban kasa ganin 'ya'yanta

    Wata kotu a Zimbabwe ta hana matar mataimakin shugaban kasar Constatino Chiwenga, Marry Mubaiwa, ganin 'ya'yansu da ma shiga gidan da suke ciki.

    Babbar kotu ta yi watsi da bukatar Ms Mubaiwa da ke son a ba ta dama ta rika shiga gidan tana ganawa da 'ya'yansu.

    Kotun ta bukaci ta rika zama a gidan iyayenta har sai ta kammala yanke hukunci a kan shari'ar da suke yi.

    A bara ne aka kama Ms Mubaiwa ana tuhumarta da yunkurin kashe Mr Chiwenga da yin mu'amala da kudaden haramun.

    An bayar da belinta ranar shida ga watan Janairu sannan aka bukaci ta mika fasfo dinta na difilomasiyya da kuma takardun gidajen mahaifinta.

    Tun daga wancan lokacin take neman kotu ta ba ta damar shiga gidan Mr Chiwenga domin ganawa da 'ya'yansu.

  2. An yi gobara a gidan su Obasanjo

    Rahotanni daga jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya na cewa an yi gobara a gidansu tsohon shugaban kasar cif Olusegun Obasanjo da ke Ita-Eko a Abeokuta.

    Wani dangin tsohon shugaban kasar ya shaida wa jaridar TheCable cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da misalin karfe tara na dare, ko da yake gobarar ta shafi bangaren da matasa maza ke kwana ne kawai.

    ”A gidan ne mahaifan Obasanjo suka yi rayuwarsu har suka rasu. Tsohon gida ne. Ba shi ne babban gidan da Obasanjo ke ciki ba,” in ji mutumin.

    Ya kara da cewa tuni aka kashe gobarar.

    Jaridar ta ce cif Obasanjo ba ya Najeriya lokacin da lamarin ya faru, kuma yana kan hanyarsa ta komawa gida daga taron kasashen Afirka da ya halarta a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

  3. Tarayyar Turai ta soki Mozambique kan 'magudin zabe'

    Kungiyar tarayyar Turai ta bayyana matukar mamakinta kan 'magudin' da aka yi a zaben shugaban kasar da gudanar a Mozambique a watan Oktobar da ya gabata.

    A rahotonsu na karshe kan zaben, wanda aka fitar ranar Laraba, masu sanya ido kan zabe na tarayyar Turai sun yi alla-wadai kan yadda aka gudanar da shi suna masu cewa an tafka magudi a kusan dukkan matakan zaben.

    Jam’iyyar Frelimo mai mulkin kasar ce ta lashe zaben – wanda aka yi tsammani zai wanzar da zaman lafiya a kasar ta Kudancin Afirka.

    Tarayyar Turai ta ce an tafka magudi musamman a yankunan da ‘yan hammaya ke samun boyon baya sosai, wanda ta ce an yi shi ne domin jam’iyya mai mulki ta yi nasara.

    Sai dai da alama duk da wannan suka da tarayyar turai ta yi, da wahala a samu wani sauyi nan take kan harkokin siyasar Mozambique.

  4. Janar Murtala Mohammed ya cika shekara 44 da rasuwa

    Ranar Alhamis, 13 ga watan Fabarairun 2020 tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Murtala Ramat Mohammed ke cika shekara 44 da rasuwa.

    Wasu sojoji da suka yi yunkurin juyin mulki ne suka kashe tsohon shugaban Najeriyar ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 1976 a Lagos.

    An harbe shi ne a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa wurin aiki.

    Murtala Mohammed shi ne mutum na hudu da ya zama shugaban Najeriya tun bayan samun ‘yancin kanta daga turawan mulkin mallakar Birtaniya a 1960.

    Akasarin ‘yan kasar na tuna irin jajircewar da ya yi wajen yaki da rashawa da cin hanci da kawo tsari ga aikin gwamnati da son ci gaban kasa.

  5. Barkanmu da sake saduwa

    Da fatan kun wayi gari lafiya. Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da ake ciki a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da wasu sassan duniya. Sunana Nasidi Adamu Yahaya, kuma za ku iya bi na a shafin Twitter: Nasidi_Kura

  6. Rufewa

    A nan muka kawo karshen labaran kai tsaye.

    Sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu.

    Za ku iya duba kasa don karanta abubuwan da suka faru a Najeriya da sauran sassan duniya ranar Laraba.

  7. MDD ta fitar da jerin kamfanonin 112 da ke da alaka da matsugunan Yahudawa

    Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da rahoton da aka dade ana jira kan kamfanonin da ke da alaka da matsugunan yahudawa a West Bank.

    Rahoton ya ambaci bangarorin kasuwanci 112 da ofishin ya ce yana da dalilai masu gamsarwa cewa sun shiga ayyukan da suka shafi matsugunan.

    Kamfanonin sun hada da Airbnb da Booking.com da Expedia Group da Motorola Solutions.

    Falasdinawa sun ce rahoton "nasara ce ga dokokin kasa da kasa", amma Isra'ila ta kira shi "abin kunya".

    Kimanin Yahudawa 600,000 ne ke zaune a cikin matsuguni kimanin 140 da aka gina tun lokacin da Isra'ila ta mamaye West Bank da gabashin Kudus a shekarar 1967.

    Falasdinawa sun dade suna kira da a cire matsugunan, suna jayayya cewa kasancewar su a wajen suna ganin barazana ne ga ikirarin ganin kasar Falasdinu mai zaman kanta.

  8. Gwamnan Borno ya bai wa Buhari shawara kan Boko Haram

    Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya ce akwai bukatar a sauya salon yakin da ake da Boko Haram.

    A cewar wata sanarwa da Isa Gusau mai magana da yawunsa ya aike wa BBC, gwamnan ya bayyana haka ne a Fadar Shehun Borno yayin da yake jawabi a gaban Shugaba Buhari lokacin da ya kai ziyara birin Maidugurin ranar Laraba.

    Buhari ya je Maiduguri ne domin mika ta'aziyyarsa bisa hare-haren da Boko Haram ta kai a Auno wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 30 tare da kona motoci 18 da kuma gidaje.

  9. Majalisar Turai ta amince da kuduri kan matakan tataunawa da Birtaniya

    Majalisar Turai ta amince da wani kuduri kan matakan da ya kamata Kungiyar Tarayyar Turai ta bi kan batun tataunawa da Birtaniya game da dangantakar da za su kulla nan gaba bayan ficewar kasar daga EU.

    Majalisar Turan yi kira ga Biritaniya da ta yi aiki da irin manufofin Turai, tare da nufin abin da ake kira saukakawa jadawalin aiki, wanda hakan ke nufin Burtaniya ta karbi sabbin ka'idodin Turai a wasu yankuna.

    Kuri'ar ba mai tsauri ba ce amma wani yunkuri ne na sauke nauyin babban mai shiga tsakani na kungiyar Tarayyar Turai Michel Barnier, wacce a baya-bayan gwamnatocin kasashen kungiyar suka tattauna a kan batun.

    Ana sa ran ministocin kungiyar tarayyar turan za su amince da matakan a wani taro da za su yi a wannan watan.

  10. Za a ci gaba da rage farashin biredi a Sudan

    Sudan ta ce za ta ci gaba da rage farashin biredi yayin da suke cikin lokacin sauyin mulki.

    Ministan kasuwanci, Madani Abbas Madani ya ce kasar tana da alkama da za ta isa a yi amfani da ita har zuwa watan Mayu.

    Akwai rahotanni da ke cewa jami'an tsaro sun kashe mutum daya a garin Kosti.

    Zanga-zangar da aka yi a 2018 saboda hauhawar farashin biredi ta juye rikicin siyasa da ya kai ga hambarar da gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir.

  11. 'Rahoton Zahra Buhari ta samu aiki da hukumar PPRA ba gaskiya ba ne'

    Fadar shugaban Najeriya ta karyata rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa 'yar Shugaba Buhari, Zahra ta samu aiki da hukumar kula da albarkatun mai da kuma kayyade farashin man fetur wato PPRA.

    Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan kafafen yada labarai Femi Adesina ya fitar yau Laraba, ta ce yayin da Zahrah take da ikon yin aiki a duk inda ta samu aiki, amma rahoton da wata kafar yada labarai ta intanet ta fitar ba gaskiya ba ne.

    Sanarwar ta ce rahoton ba shi da tushe kuma an yi ne domin bata sunan iyalan shugaban kasar musamman yadda kafar ta ce an samu aikin ne ta hanyar da ba ta kamata ba.

    A karshe sanarwar ta bukaci jama'a su yi watsi da rahoton.

  12. Buhari ya sha alwashin samar da tsaro a Najeriya

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya jaddada alkawarinsa na inganta tsaro a fadin kasar.

    Buhari ya bayyana haka ne bayan ziyarar ta'aziyyar da ya kai jihar Borno domin jajanta wa gwamnati da jama'ar jihar game da kashe mutum kusan 30 da kungiyar Boko Haram ta yi.

    A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan ziyarar, Buhari ya ce:

    "Ina tabbatar wa dukkan 'yan Najeriya cewa muna daukar matakan inganta tsaro a fadin kasar.

    "A jihar Borno, sojoji za su ci gaba da aiki tukuru domin magance masu tayar da kayar baya.

    Ina rokon shugabannin al'umma da jama'a da su taimaka wa sojoji da bayanai da goyon baya da ya dace."

  13. An nada Joseph Yobo mataimakin kocin Najeriya

    Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta nada Joseph Yobo a matsayin mai taimaka wa kocin tawagar kwallon kafar kasar.

    Yobo, tsohon dan wasan Super Eagles zai maye gurbin Imama Amapakabo.

    Yobo ya buga wa Najeriya wasa 100, bayan da ya fara buga mata tamaula a Afrilun 2001 a wasan shiga gasar kofin Afirka da kasar ta yi da Zambia.

  14. Labarai da dumi-dumi, An yi wa Buhari ihu a Maiduguri

    Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin Borno na cewa an yi wa Shugaba Muhammadu Buhari ihun ''ba ma yi, ba ma yi'' yayin ziyarar da ya kai yau Laraba.

    Wasu kwararan majiyoyi sun tabbatar wa BBC faruwar lamarin.

    Hakan kuma ya faru ne lokacin da Buhari yake barin fadar Shehun Borno zuwa gidan gwamna a wani waje da ake cewa 'Yan Nono.

    Buhari dai ya ziyarci Maiduguri ne domin jajanta wa gwamnati da al'ummar jihar bisa hare-haren da Boko Haram ta kai kan wasu matafiya abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

    Tuni wani bidiyo da ake masa ihun ya bazu tamkar wutar daji a shafukan sada zumuntar Najeriya.

    Sannan sunan Buharin na daga cikin mafiya tashe a shafukan a yau Laraba.

  15. Biri ya sace zaki a Afirka Ta Kudu

    Wani jami’in yawon bude ido a Afirka Ta Kudu wanda ya dauki hoton wani biri yana renon zaki a wani wajen shakatawa a Kruger, ya ce ba a ji motsin dabbobin ba tun bayan daukar hoton a makon da ya gabata.

    A wata sanarwa da ya aike wa BBC Kurt Schultz, daraktan wajen shakatawar na Kurt Safari, ya ce yanayin damina ya sa ba a iya gano dabbobin ba.

    Hoton dai ya ja hankalin jama'a da dama.

    Mr Schultz ya ce jaririn zakin wanda birin ya kama na cikin hadari.

    Mr Schultz ya kara da cewa bai ga alamun jaririn zakin zai rayu ba.

  16. Dubban yara ba sa zuwa makaranta a Nijar kan hare-haren ta'addanci

    A jamhuriyar Nijar dubban yara na jihar Tillabery ne ba sa zuwa makatu, bisa hare-haren ta'adanci da yan bindiga ke kai wa makarantun, suna cinna masu wuta.

    Malaman sun bayyana cewa suna aikin ne cikin fargaba ganin hukumomin kasar sun ki amincewa da wata bukata da kungiyar malaman ta mika masu.

    Wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou ta duba mana wannan batu ga kuma rahotonta daga Yamai:

  17. Syria za ta dandana kudarta kan hare-haren da ta kai wa sojin Turkiyya

    Shugaban Turkiyya ya gargadi gwamnatin Siriya cewa za ta dandana kudarta da gasken-gasken bisa hare-haren da ta kai a kan sojin Turkiyyar a arewa-maso-yammacin Siriyar.

    Rajib Tayyib Erdowan ya ce sojin Turkiya za su kai hari a kan na Siriyar a ko ina idan har aka sake aka yi aibi ga sojin Turkiyyar komai kankantarsa a lardin Idlib.

    Sojin Turkiyar biyar aka kashe a lardin yayin da sojin Siriyar ke ci gaba da kai farmaki.

  18. Dakarun Amurka sun yi artabu da mayakan sa kai a Syria

    Rahotanni na cewa an kashe wani mutum a wani artabu da ya barke a arewa maso gabashin Syria tsakanin dakarun hadin gwiwa mai samun goyon bayan Amurka da mayakan sa kai na gwamnati.

    Kamfanin dillancin labarai na Syria, Sana ya ce wani farar hula ya mutu lokacin da dakarun Amurka suka yi harbi kan dandazon mutane domin hana su ketare wani wajen binciken motoci da ke birnin Qamishli.

    Wata kungiyar sa ido ta ce ba bu tabbacin ko mutumin da ya mutu ya na rike da makami ko a'a.

    Dakarun hadin gwiwar sun ce wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun kai musu hari abin da ya sa suka yi harbi domin kare kansu.

    Kimanin dakarun Amurka 500 ne a arewa maso gabashin Syria domin taimakawa mayakan SDF wajen yaki da IS.

  19. INEC za ta yi zaben cike-gurbi a Jigawa, Niger, Kwara da Sokoto

    Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta ce za ta gudanar da zabukan cike-gurbi a wasu jihohin kasar ranar Asabar, 14 ga watan Maris, 2019.

    Sanarwar da kwamishinan yada labarai na INEC, Festus Okoye, ya sanyawa hannu wacce kuma aka wallafa a shafukan sada zumunta na hukumar ta ce za a gudanar da zabukan ne a jihohin Jigawa, Naija, Kwara da Sokoto.

    Wasu daga cikin zabukan na kujerun 'yan majalisar dokokin tarayya ne, yayin da wasun su na 'yan majalisar dokokin jiha ne.

    A Jigawa, za a gudanar da zaben kujerar majalisar dokokin tarayya don maye gurbin, Adamu Muhammadu Fagen Gawo, dan majalisar da ke wakiltar mazabun Babura/Garki, wanda ya mutu.

    Kazalika za a yi zaben cike-gurbi a mazabun Magama/Rijau a jihar Naija, yayin da za a yi zaben 'yan majalisar dokokin jiha a mazabun Kebbe a jihar Sokoto da kuma Patigi a jihar Kwara.

  20. Gwamnatin Ogun ta amince da kudirin kafa Amotekun

    Gwamnatin jihar Ogun ta amince da kudirin da ke neman a kirkiri hukumar tsaro ta yammacin Najeriya mai suna Amotekun.

    Jaridar Punch ta ruwaito an ba da amincewar samar da hukumar a taron majalisar zartarwar gwamnatin jihar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abeokuta.

    Sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Kunle Somorin ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar yau Laraba.

    Sanarwar ta ce kwamishinan shari'a na jihar, Mr Adegbolahan Adeniran, ya ce gabatar da kudirin gaban majalisar zartarwar ya biyo bayan amincewar kwamishinonin shari'ar jihohin kudu maso yammacin Najeriya shida.

    Tun a watan Janairu ne dai gwamnatin Najeriya ta haramta shirin na Amotekun da wasu jihohin shiyyar kudu suka samar.

    Gwamnatin ta soke shirin saboda a cewarta, jihohin ba su da hurumin kafa Amotekun lamarin da ya janyo cece-kuce a kasar.

    Sai dai kuma Jagoran jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu ya ce ba a fahimci shirin Amotekun ba.