Abubuwan da suka faru ranar Juma'a

Shafin da ke kawo labaran abubwan da ke faruwa kai tsaye a Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da Chadi da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Sagiru Kano Saleh and Halima Umar Saleh

  1. Mutum biyar sun mutu a harin Gwoza, Wasu mutum tara kuma sun jikkata kuma suna samun kulawa a asibiti.

    @

    Asalin hoton, Getty Images

    Yawan mutanen da suka rasu a harin kunar bakin wake da ake kai garin Gwoza a jihar Bornon Najeriya ya karu zuwa biyar, a cewar ma’aikatan ceto.

    Wasu mutum tara kuma sun jikkata kuma suna samun kulawa a asibiti.

    Mamatan sun hada da da wasu mutum biyu da suka mutu nan take da wani mutumin da ya mutu a asibiti sai kuma ‘yan mata biyu da suka kai harin. Wadanda suka samu raunuka kuma na samun kulawa.

    Rahotanni da aka samu da farko sun ce ‘yar kunar bakin waken ta tayar da bam din da ke nade a jikinta ba bayan kutsa cikin masallatan da ke sallar Subahi.

    Babu wata kungiya da ta iya ikirarin kai harin amma kungiyoyin Boko Haram da ta ISWAP sun saba kai hare-hare ayankin.

  2. Labarai da dumi-dumi, Kotu ta samu Maryam Sanda da laifin kashe mijinta

    Maryam Sanda

    Wata babbar kotu a Abuja ta samu Maryam Sanda da laifin kashe mijinta.

    A ranar Litinin ne kotun ta yanke hukunci a kan shari’ar Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta Bilyaminu Bello a 2017.

    Da farko dai Maryam ta musanta zargin inda ta ce zamewa mijin nata ya yi inda ya fadi a kan kuttun shisha wanda ya yi ajalinsa.

    An gurfanar da ita a gaban kotu tare da dan uwanta da mahaifiyarta da ‘yar aikinta da ake zargi da lalata shedun da ke nuna ta aikata laifin da ake zargin ta a kai.

    Bayan sauraron bangarorin da ke shari’ar a ranar 25 ga watan Nuwamban 2019, alkali Yusuf Halilu ya sanya ranar 27 ga watan Janairun 2020 a matsayin ranar yanke hukunci.

  3. Mene ne sunan wannan dabbar da Hausa

    Cheetah

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Farawa

    Masu bibiyarmu barkanku da warhaka. barka da sake saduwa a shafinmu da muke kawo muku baynanan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Niger da sauran sassan duniya. Da fatan za ku kasance da mu a wanna rana domin ci gaba da kawo muku bayanai kai tsaye.