Salva Kiir da Riek Machar za su sake zama
Idan anjima ne a yau shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir da madugun 'yan tawaye, Riek Machar za su sake komawa teburin sulhu a fadar gwamnatin kasar da ke birnin Juba.
A jiya ne dai shugabannin biyu suka amince da su kafa gwamnatin hadaka a watan Fabrairu, bayan karewar kwanaki 100 da aka deba na cimma zaman lafiya.
Kasashen duniya dai na ci gaba da matsa wa bangarorin biyu lamba wajen ganin sun zartar da yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma domin kawo karshen shekaru biyar na yakin basasa.
A ranar 15 ga watan Disamban 2019 dai Amurka ta kakaba wa manyan jami'an gwamnatin Sudan ta Kudu da take zargi da yi wa shirin zaman lafiya tuggu, takunkumi.