Gwamnatin Najeriya ta shaida wa BBC cewa, ta na shirin shigar da
korafinta ga kungiyar tarayyar turai matukar ba a dawo mata da wasu dalibai
biyu 'yan kasarta da yanzu haka suke a Bosnia ba.
Gwamnatin ta ce
tana dakon a dawo mata da 'yan kasar ta ta a cikin wannan makon ko kuma
ta dauki matakin. An dai kai daliban ne bisa kuskure zuwa Bosnia da ga Croatia,
inda suka halarci gasar wasan kwallon tennis da aka shirya.
Da ta ke yi wa BBC karin
bayani, shugabar hukumar da ke kula da 'yan Najeriya da ke zaune a kasashen
waje, ta ce yakamata ace an dawo da daliban gida Najeriya tun a ranar
Jumma'a, amma kuma har yanzu suna Bosnia.
Ta ce "muna fatan za su dawo gida a cikin wannan makon, dole su
dawo, idan kuma har aka ci gaba da rike su to zamu dauki mataki na shigar da
korafinmu a kungiyar tarayyar Turai da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam.
Croatia da Bosnia ba su da ikon rike mana 'yan kasarmu, kai ko da ma ace sun
aikata wani laifi ne to a dawo da su gida mana tun da suna da takardun
izinin shiga kasar Croatia, kuma a dawo da su gida ma na."
Abike Dabiri Erewa, ta ce ta tattauna da daliban wato Alexandro
Abia da Kenneth Eboh, sun kuma shaida mata cewa suna cikin mummunan yanayi.
Ta
kara da cewa, daya daga cikinsu har suma ya yi a wani sansanin 'yan gudun hijra
da ke Bosnia.
A cewar Mrs Dabiri, ofishin jakadan Najeriya da ke Croatia
bai san da kasancewar 'yan Najeriyar a Bosnia da Croatia ba.