Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

DSS ta sake kama Sowore

Wannan shafi ne da ke kawo maku rahotanni kai-tsaye game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da wasu makwabtansu a yau.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. DSS ta bankado shirin 'tayar da hargitsi' lokacin Kirsimati a Najeriya

    Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta ce ta gano wasu shirye-shirye da wasu gungun mutane ke yi da ke nufin haifar da yamutsi a sassan kasar ciki har da babban birnin kasar Abuja.

    Shirin na ingiza mutane su fito zanga-zanga da kuma haifar da hargitsi da tashin hankali don tabarbara al’amura a kasar.

    Cikin wata sanarwa da Peter Afunanya jami'in hulda da jama'ana hukumar DSS ya fitar ta ce ta bankado shirin wadda aka tsara gudanar da tashin hankali a manyan biranen shiyoyin Najeriya cikin makonni masu zuwa.

    Masu wannan shirin son aiwatar da wannan mugun nufin ne a lokutan bukukuwan Kirsimati a cewar sanarwar.

  2. Dahiru Bauchi ya roki Ganduje ya bar batun dawo da sabbin masarautu

    Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya Sheikh Dahiru Bauchi ya roki gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje cewa ya janye aniyarsa ta dawo da sabbin masarautun jihar.

    Malamin ya bayyana hakan ne a wani sakon murya da ya aiko wa BBC Hausa.

    A cikin sakon malamin ya ce: ''Ina rokon Ganduje don Allah don Annabi ya bar batun nan kamar yadda kotu ta soke shi.''

    A ranar Litinin ne Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta sake aikawa da wani sabon kudiri ga majalisar jihar, domin kafa sabbin masarautu.

    Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata kotu a Kano ta soke sabbin masarautun da aka kafa a baya, inda ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka'ida ba.

    Ku latsa lasifikar da ke kasa don sauraron bayanin Malam.

  3. 'Yan bindiga sun kashe mutum 20 a Burkina Faso

    Rahotanni daga Burkina Faso na cewa 'yan bindiga sun kashe a kalla mutane 20 da sojoji uku a wasu hare-hare da suka kai lokaci guda a iyakar kasar da Mali.

    A daya daga cikin hare-haren, wasu da ake zargin masu ikirarin jihadi ne sun afkawa wani sansanin sojoji a garin Toeni da ke arewacin kasar.

    A tsallaken iyakar kasar da Mali, a kalla sojoji biyu ne aka kashe aka kuma raunata guda bakwai sakamakon wani bam da aka dasa kan hanya wanda ya tashi da su.

    Wasu guda tara kuma sun samu raunuka sakamakon harin bam a kusa da Burkina Faso.

    Yankin dai na fama da hare-hare daga kungiyoyin masu ikirarin jihadi da kuma wasu kungiyoyi na 'yan bindiga.

  4. Hotunan yadda gobara ta cinye shaguna 15 a kasuwar Owode-Oniri ta jihar Legas

    Gobarar ta tashi ne a kasuwar karafa ta Owode-Oniri wanda take unguwar Ikorodu da safiyar ranar Lahadi kuma cinye shaguna akalla 15 ne kuma aka tafka asarar dukiya mai yawa.

  5. Mutum 15 sun mutu a gobara wata masana'anta a Sudan

    Mutane 15 ne suka mutu wasu 48 suka ji rauni a lokacin da wani abu ya fashe tare da haddasa mummunar gobara a wata masana’anta da ke birnin Khartoum a Sudan.

    Kungiyar likitocin Sudan ita ce ta tabbatar da hakan tare da kiran likitocin kasar su kai agaji asibitin da aka kai wadanda suka kone.

    Ganau sun wallafa bidiyon yadda wutar ke ci ganga-ganga a shafin Twitter, yayin da hayaki ya turnuke sararin samaniya a arewacin birnin Khartoum da wutar ta kama.

  6. Shugaban Laberiya 'na so majalisa ta ba da izinin buga kudin kasar dala biliyan 35'

    Shugaban kasar Laberiya George Weah ya bukaci 'yan majalisar dokoki su dakatar da hutun da suke yi su koma majalisar don tattauna wasu ''batutuwa masu muhimmanci'' da suka shafi kasar.

    Mai magana da yawun majalisar Isaac Redd bai yi karin haske kan ko wadanne ne batutuwan ba, amma rahotanni na cewa shugaban kasar, wanda tsohon dan kwallo ne na so majalisar ta yi gaggawar bayar da izinin buga kudin kasar kimanin dala biliyan 35 ne.

    Ana so za a biya ma'aikat ne da kudin gabanin bikin Kirsimeti.

    Sai dai mai magana da yawun ofishin shugaban kasa Smith Toby, ya ce ba a ambaci wani abu mai kama da hakan ba a wasikar da shugaban ya aike majalisa.

    Laberiya na fama da matsalar karancin kudi a kasar, abin da ya janyo 'yan majalisa da ma'aikatan gwamnati ba sa samun albashinsu da wuri.

  7. 'Yan Sudan na rokon Amurka ta cire kasar daga jerin kasashen da ke tallafawa 'yan ta'adda

    Manyan shugabannin Sudan sun rattaba hannu kan wata budaddiyar wasika tare da rokon shugaban Amurka Donald Trump ya cire kasar daga jerin kasashen da ke tallafawa 'yan ta'adda.

    Wasikar wadda 'yan siyasa da malaman jami'a da masu fafutuka da kwararru kan harkokin kasashen waje suka rubuta, ta ce bai kamata a hukunta Sudan kan laifin da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir ta aikata ba, wanda aka hambarar da gwamnatinsa bayan kazamar zanga-zangar da aka yi a daukacin kasar.

    A shekarar 1993 ne Amurka ta sanya Sudan a jerin kasashen da ke daukar nauyin 'yan ta'adda, bayan an zarge kasar da tunzura masu ikirarin jihadi.

  8. Buhari ya aika sunan sabon shugaban Hukumar Alhazai Majalisar Dattijai

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sunan sabon shugaban hukumar alhazai ta Najeriya da mambobinta ga majalisar dattijan kasar.

    Majalisar dattawan kasar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta karanta wata wasika da Shugaban kasa ya turo mata kan nada sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya.

    Sai dai majalisar ba ta yi karin bayani kan ko waye sabon shugaban NAHCOn din da mambobinta ba.

    A yanzu dai Abdullahi Mukhtar ne shugaban hukumar mai ci.

  9. Majalisar Kano za ta fara nazari kan dokar kafa sabbin masarautu

    Nan gaba a yau ne ake sa ran majalisar dokokin jihar Kano a Najeriya za ta fara nazari kan kudurin dokar kafa sabbin masarauta hudu, da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mika mata a jiya Litinin.

    A watan jiya ne wata babbar kotu a jihar ta soke dokar da ta kafa sabbin masarutun Rano, da Karaye, da Gaya, da kuma Bichi.

    Ku saurari hirar da BBC ta yi da shugaban masu rinjaye na majalisar, Labaran Abdu kan batun:

  10. An gano farfesoshin boge 100 a jami'o'in Najeriya

    Hukumar da ke kula da jami'o'in Najeriya NUC ta ce ta gano farfesoshi na boge kusan 100 a jami'o'in da ke fadin kasar.

    Shugaban NUC Farfesa Abubakar Rasheed ne ya bayyana hakan a mujallar da hukumar ke fitar wa duk wata ta watan Nuwamba.

    Shugaban ya ce an wallafa bayanan farfesoshin bogen a shafin hukumar na intanet.

  11. An kashe manyan 'yan sanda biyu a arangama da kungiyar IPOB

    Ana zargin wasu mambobin kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a Najeriya sun kashe wasu manyan jami'an 'yan sanda biyu, a yayin wata arangama tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar a jihar Anambra.

    A ranar Litinin ne rikicin ya barke a lokacin da jami'an 'yan sanda suka isa yankin Oraifite domin kama wani mutum mai suna Mr Ifeanyi Ejiofor, wanda lauyan jagoran kungiyar IPOB ne Nnamdi Kanu.

    'Yan sanda sun ce ana nemansa ne ruwa a jallo saboda munanan laifukan da yake aikatawa kuma ya ki amsa gayyatar da suke masa.

    A hannu guda kuma, rahotanni na ambato Nnamdi Kanu yana cewa jami'an tsaron sun kashe mayakan IPOB uku a yayin arangamar.

  12. Mugabe ya bar kudi dala miliyan 10m lakadan

    Jaridar Herald ta kasar Zimbabwe ta ruwaito cewa Tsohon Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya bar Dala miliyan 10 a banki da wasu gidaje masu yawa a Harare, babban birnin kasar.

    Mugabe wanda ya mutu a watan Satumba yana mai shekara 95 bai bar wasiyya ba, kuma wannan ya sa hukumomi kiran taro a wannan makon don nada wanda zai jagoranci rarraba kadararsa.

    Tsohon shugaban ya bar motoci 10 a cewar jaridar.

    Mugabe ya yi mulkin Zimbabwe tun da ta samu 'yanci a 1980 a matsayin Firayim Minista kuma Shugaba kafin a tsige shi daga mulki a 2017.

    Ya mutu ya bar matarsa ta biyu Grace Mugabe da 'ya'ya hudu. Karkashin dokokin Zimbabwe, su za su gaji dukiyarsa.

  13. Buhari ya tafi taron manyan hafsoshin sojin kasan Najeriya

    A yau ne shugaban Najeriya muhammadu Buhari ya tafi jihar Kaduna domin halartar taron manyan hafsoshin sojin kasa.

    Shugaban ya tafi Kaduna ne daga Katsina bayan barin mahaifarsa Daura inda ya aza harashin gina Jam'iar Sufuri a jiya Litinin.

  14. EFCC ta gano wajen da ake bai wa masu zambar intanet horo a Najeriya

    Jami'an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gano wani gini da wasu da ake zargin masu zamba ta intanet ne suke amfani da shi wajen bai wa mutane horo kan yadda za su kware a harkar zambar intanet. Wajen yana kauyen Ikot Ibiok da ke karamar hukumar Eket ne ajihar Akwa Ibom akudancin Najeriya. A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwajaren ya fitar, ta ce an kama wadanda ake zargin masu zamba ta intanet ne har 23.

  15. Za a gudanar da zabukan 'yan majalisar dokoki a Kamaru a watan Fabarirun 2020

    Gwamnatin Kamaru ta sake tabbatar da cewa za a gudanar da tagwayen zabukan ‘yan Majalisar dokoki da na kananan Hukumomi a ranar 9 ga watan Fabrairu na badi.

    A wani taron maneman labarai na hadin gwiwa, Kakakin Gwamnati Minista Rene Emmanuel Sadi da takwaranshi na harkokin cikin gida Paul Atanga Nji, sun ce dage zabe zuwa wani lokaci ba zai yiwu ba, saboda an yi la’akari da duk wasu dokokin da suka wajaba.

    Sakamakon haka kuma sun yi alkawarin tabbatar da tsaro domin bai wa jama’a damar fita su kada kuri’a.

    Ministocin biyu sun bayar da amsa ne ga wasu jam’iyyun adawa suke yi na a daga lokacin zabe, ko kuma a kara wa ‘yan takara wa’adin hada takardun takara.

    A yayin da wasu kira suka yi da a kaurace wa zaben saboda rashin tsaron da yankin rainon Ingila yake fuskanta.

    8

  16. Barka

    Masu bin mu a wannan shafi Assalamu alaikum barkanmu da safiya.

    Ku biyo mu don karanta labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru dsa Chadi da Ghana da sauran makwabtan kasashe a yau.

  17. Babu ranar bude iyakokin Najeriya - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce har yanzu bai sa ranar bude iyakokin kasar da aka rufe ba, har sai an shawo kan matsalar shigo da kayan da aka haramta kasar.

    Shugaban Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya gana da wata tawagar Dattijan Jihar Katsina a mahaifarsa ta Daura.

    Ya kuma ce yawan man fetur da ake amfani da shi a kasar ya ragu da kusan kashi 30 cikin 100 bayan da aka rufe iyakokin kasar.