'Yan Najeriya ne neman a bi wa wata mata hakkinta wacce ''ta mutu a asibiti bayan da suka ki duba ta'' sakamakon caka mata wuka da aka yi a wuya.'
Asibitin sun yi watsi da zargin da ake musu na kin kula da ita.
Rahotanni sun ce wani barawo ne ya caka wa Moradeun Balogun wuka a wuya a kan hanyarta ta koma wa gida.
An garzaya da ita asibiti inda ta yi ta zubar da jini har ta mutu.
'Yar uwar marigayiyar Molad, ta ce asibitin sun ki karbarta don duba ta suka ce sai an kawo rahoton 'yan sanda.
Sai dai asibitin da aka kai Ms Balogun sun ce ba su ki karbarta ba.
Daraktan Asibitin Jolad, Funso Oladipo ya shaida wa Jaridar Premium Times cewa likitoci sun karbi Ms Balogun amma sai suka fahimci cewa tana bukatar dubawar kwararru.
''Ba mu karbe ta a asibitin ba. Nan da nan muka mayar da ita Gbagada bayan da muka fahimci cewa ba za mu iya ba ta taimakon da take bukata ba kuma wadanda suka kawo ta sun yi tafiyarsu,'' a cewarsa.
Sai dai 'yan Najeriya suna ta magana a shafukan sada zumunta cewa an ki a duba ta ne, sannan batun nemar mata hakkinta na ci gaba da tashe.
Ana ta amfani da maudu'in #JusticeForMoradeun, abokai da iyayen marigayiya Moradeun Balogun sun zargi asibitin da nuna halin ko in kula.