Shafi ne da ke kawo maku abubuwan da suke faruwa a Najeriya da Nijar da Ghana da kuma Kamaru, har ma da makwabtansu.
Rahoto kai-tsaye
Halima Umar Saleh and Umar Mikail
Yau Abba Gida-Gida zai san matsayinsa a kotu
Asalin hoton, Others
A yau Juma'a ne Kotun Daukaka Kara da ke birnin Kaduna take yanke hukunci kan karar da Abba kabir Yusuf, dan takarar gwmnan jihar Kano a jam'iyyar PDP, ya daukaka yana kalubalantar nasarar Gwamna Abdullahi Umar Ganguje na jam'iyyar APC a zaben watan Fabarairu.
Tun farko dai Mai shari'a Halima Shamaki ta kotun sauraron kararrakin zabe ta kori karar farko da Abba Gida-Gida ya shigar gabanta a ranar 2 ga watan Oktoba.
Ku kasance da mu domin sanin yadda za ta kaya a kotun.
Shugaban Babban Zauren MDD na ziyara a Najeriya
Asalin hoton, NAN
Shugaban Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya yana ziyarar aiki a Najeriya irinta ta farko tun bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban zauren.
Muhammed-Bande wanda dan Najeriya ne kuma na biyu da yake rike irin wannan mukami, ya sauka a Abuja ne da karfe 11:45 na daren Alhamis, inda yake ziyarar kwana hudu.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, Muhammad-Bande ya bayyana abin da ya kawo shi sannan kuma ya ce yana farin ciki da saukarsa a gida Najeriya.
"Lallai na ji dadin kasancewata a gida kuma na kagu na ji abubuwan da ke faruwa. Amma abin da ya kawo mu shi ne mu tattauna yadda dattijai ke gudanar da rayuwarsu da kuma yadda za mu saukaka wa rayuwar tasu," in ji shi.
NAN ya ce ziyarar tasa wani bangare ne na taron da za su yi mai taken Regional Expert Conference on the Human Rights Situation of Older Persons in Africa - game da rayuwar dattijai a nahiyar Afirka - wanda za a gudanar a Abuja babban birnin Najeriya ranar Litinin mai zuwa.
'Yar shekara 15 ta lashe lambar zaman lafiya a Kamaru
Asalin hoton, Getty Images
Wata matashiya mai shekara 15 da ake kira Divina Maloum ta lashe lambar karramawa ta zaman lafiya game da kokarinta na hana tauye hakkokin yara da yaki da ci da guminsu.
Kungiyar KidsRights ta kasar Netherlands ta ce ta bai wa Davina Maloum wannan lambar yabo saboda kokarinta wajen kare yara fadawa tarkon masu cin zarafinsu.
A 2014 ne wannan matashiya ta kafa kungiyarta ta “Children For Peace” domin aiki da iyayen yaran da ake amfani da su a hanyar ta’addanci.
Sanata Ali Ndume bai yarda da karin haraji ba a Najeriya
Bayanan sautiSanata Ali Ndume bai amince da kara haraji ba a Najeriya
Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hirar Ali Ndume
Ba dukkan 'yan Majalisar Dattijan Najeriya ne suka yarda da kudurin karin harajin kayayyaki ba, wanda majalisar ta sahhale a jiya Alhamis bisa yunkurin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na kara harajin daga kashi 5% zuwa 7.5%.
Sanata Ali Ndume, dan Majalisar Dattawan daga jihar Borno, ya ce "sam bai dace a kara harajin ba sannan kuma duk abin da aka ce dokar ba za ta shafa ba ya kamata a fade shi a cikin dokar".
Yayin da yake gabatar da kasafin kudin shekara ta 2020, Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta gina kasafin ne a kan kudin harajin kayayyaki, a saboda haka za ta kara yawan harajin daga kaso 5 zuwa 7.5.
Buhari ya ce: " Dokar harajin VAT ta tsame magunguna da kayan koyo da karantarwa da kayan more rayuwa....."
"Sashe na 46 na dokar kudi ta 2019 ta kara yawan kayayyakin da karin harajin ba zai shafa ba da suka hada da:
Burodi fari ko ruwan kasa
Masara da shinkafa da alkama da gero da dawa
Kifi da danginsa;
Fulawa da abinci mai sitati;
Kayan marmari da abubuwa masu kwanso da ganyaye
Doya da gwaza da dankalin gida da na turawa
Nama da kwai
Madara;
Gishiri da kayan kamshi
Ruwa."
Assalamu Alaikum
Jama'a barkanku da Juma'atu babbar rana, barkanku da salke shigowa wannan shafi namu na rahotanni kai-tsaye.
Ku biyo Umar Mikail da kuma Halima Umar Saleh.
Ku duba kasa domin karanta labaran jiya Alhamis.
Karshen rahotannin
Masu sauraro nan muka kawo karshen rahotannin kai-tsaye.
Halima Umar ce da Umar Mikail ke cewa mu hadu gobe Juma'a.
Ku duba kasa domin karanta abubuwan da suka faru a yau.
Ahmed Musa zai dauki nauyin dalibai 100 a jami'a
Asalin hoton, ahmedmusa718
Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya sanar da cewa zai dauki nauyin dalibai har 100 a wata jami'a mai zaman kanta da ke birnin Kano a Najeriya.
Musa ya bayyana haka ne a yayin wata ganawa da ya yi da wakilan jami'ar Skyline University Nigeria, inda ya saka hannu kan wata yarjejeniyar zama wakilin jami'ar na musamman.
Ahmed Musa ya ce yana matukar kaunar harkokin ilimi kuma dalilin da ya sa ya shiga yarjejeniyar kenan.
"Saboda haka nake shaida maku cewa zan dauki nauyin dalibai 100 a wannan jami'ar. Kwarai kuwa, 100!" Musa ya rubuta a shafinsa na Instagram.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
'Dalibai 'yan Najeriya sun fi na ko'ina yawa a Amurka'
Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoto da cibiyar Open Doors 2019 ta fitar, wanda kuma ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa, ya nuna cewa 'yan Najeriya sun fi 'yan kowace kasa zuwa karatu kasar ta Amurka.
Rahoton ya nuna cewa an samu karin daliban da kashi 5.8%, inda yanzu suka kai 13,423 a shekarar karatu ta 2018/2019 wadanda suke karatu yanzu haka a Amurka.
Kazalika wannan lamba (13,423) ta nuna cewa kashi 33% na dalibai 'yan kasashen Afirka a kasar 'yan Najeriya ne kuma hakan ya sa 'yan Najeriya sun zama kan gaba wajen shiga Amurka karatu sama da kowace kasa a duniya.
Daliban Najeriya suna karatu a manyan makarantu har 1,000 a jihohi 51, wadanda kashi 18% daga cikinsu suna jihar Texas.
Kazalika, sababbin dalibai na shekarar 2019 sun samu tallafin karatu na dala miliyan $16.
Majalisa ta amince da dokar kara harajin kayayyaki a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin gwamnatin Buhari na kara harajin kayayyaki wanda ake kira Value Added Tax (VAT).
Kudirin mai suna Finance Bill 2019 ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar a yau Alhamis, abin da ke nufin ta amince da a fara aiwatar da shi, wanda kuma a cikinsa ne kudirin na kara harajin kayayyaki yake.
Yanzu Shugaba Muhammadu Buhari za a mika wa dokar ya sanya mata hannu, inda kuma ake sa ran ta fara aiki nan take.
Yayin da yake gabatar da kasafin kudin shekara ta 2020, Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta gina kasafin ne a kan kudin harajin kayayyaki, a saboda haka za ta kara yawan harajin daga kaso 5 zuwa 7.5.
Buhari ya ce: " Dokar harajin VAT ta tsame magunguna da kayan koyo da karantarwa da kayan more rayuwa....."
"Sashe na 46 na dokar kudi ta 2019 ta kara yawan kayayyakin da karin harajin ba zai shafa ba da suka hada da:
Biredi fari ko ruwan kasa
Masara da shinkafa da alkama da gero da dawa
Kifi da danginsa;
Fulawa da abinci mai sitati;
Kayan marmari da abubuwa masu kwanso da ganyaye
Doya da gwaza da dankalin gida da na turawa
Nama da kwai
Madara;
Gishiri da kayan kamshi
Ruwa."
Kwamitin jami'ar Ghana ya kama malamanta da laifin lalata
Kwamitin bincike da Jami'ar Ghana ta kafa kan malamanta guda biyu da ake zargi da lalata da dalibai ya ce ya gano "aikata ba daidai ba".
A watan Oktoba ne Jami'ar Ghana ta dakatar da Farfesa Ransford Gyampo da Dr. Paul Butakor bayan wani binciken kwakwaf da BBC ta gudanar ya nuna su a bidiyo suna yunkurin cin zarafin 'yar jarida, wadda ta badda kama a matsayin dalibar jami'ar.
An yi wa binciken lakabi da 'sex for grades' wato 'bai wa dalibai maki a madadin jima'i'.
Kwamitin wanda tsohon alkalin Kotun Kolin Ghana Vida Akoto-Bamfo yake jagoranta, ya ce "an samu hujja kan zargin da ake yi wa Gyampo da Dr. Butakor, abin da ya saba wa sakin layi na shida na dokar malaman Jami'ar Ghana."
Shugaban jami'ar wanda ya karbi rahoton kwamitin, ya mika shi gaban kwamitin ladabtarwa na jami'ar, inda shi kuma zai dauki matakan da suka dace kan lamarin.
Labarai da dumi-dumi, Kotu ta soke dokar kirkirar sabbin masarautu a Kano
Kotu ta rushe dokar da ta bai wa majalisar jihar Kano damar kirkiro sabbin masarautun a Kano.
Babbar
kotun jihar ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudirin neman kirkirar masarautun ba bisa ka'ida ba.
Ga
dukkan alamu dai wannan hukunci na babbar kotun na nufin yanzu sarki daya ne a
Kano ba biyar ba kamar yadda aka kirkira a 'yan watannin da suka gabata.
Barista
Ibrahim Mukhtar shi ne lauyan bangaren gwamnatin jihar, kuma ya shaida wa BBC
cewa kotu ta yanke hukunci ne ba tare da tsayawa ta yi bincike yadda ya kamata
ba.
Bangaren gwamnati sun ce za su koma teburin shawara domin daukar matakin da ya dace kan hukuncin kotun.
Asalin hoton, Others
'Ana aikata laifuka a hukumar raya Niger Delta'
Asalin hoton, NAN
Shugaban kwamitin da ke kula da hukumar raya yankin Niger Delta (NDDC) a Majalisar Wakilan Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya ce hukumar ta yi ta kashe kudi ba bisa ka'ida wato ba tare da yin kasafinsu ba a cikin kasafin kudi na tsawon wata 11.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito shi yana cewa NDDC ta sha aikata laifuka kan kasafin kudinta a cikin wata 14 da suka wuce sannan kuma har yanzu ba ta mika sabon kasafin ba ga Majalisar tun Satumban shekarar 2018.
Ya kara da cewa tun bayan da aka saka hannu kan kasafin kudin 2018 hukumar take kashe kudi ba tare da izini ba. Kazalika har yanzu ba ta mika kudirin kasafin kudinta na 2020 ga Majalisa ba, abin da ya kamata ta yi watanni da suka wuce.
"Labari ne maras dadin ji amma na ji dadi ganin cewa Majalisa ta tara tana bakin kokarinta wurin kula da jin dadin 'yan Njaeriya," in ji Olubunmi Tunji-Ojo, wakili daga jihar Oyo a jam'iyyar APC.
Ya ci gaba da cewa: "Za mu yi bincike kuma mu bayar da shawarwari masu karfi a kan ko su wane ne suka aikata hakan.
"Muna sane da cewa NDDC har yanzu tana aiki ne da kasafin kudi na 2018, wanda Majalisa ta takwas ta sahhale. Muna cikin Nuwamba amma har yanzu ba ta gabatar da kudirin kasafin 2020 ba.
"Wannan saba wa doka ne. Ba mu saba gani ba saboda tsara kasafi da kuma mika wa Majalisa ba wani abu ne mai wuya ba."
Malaman jami'ar Ghana za su gurfana kan zargin lalata da dalibai
Malaman jami`ar Ghanar nan guda biyu, Farfesa Ransford Gyampo da Dr. Bukator, da wani binciken kwakwaf na BBC Africa Eye ya bankado da zargin lalata da dalibai za su gurfana gaban kwamitin ladabtarwa na jami`ar ta Ghana.
Binciken da aka gudanar ya kuma samar da wasu hujjojin cewa sun karya dokokin jami`ar.
Tun a watan oktoba ne aka dakatar da malaman kafin a gudanar da cikakken bincike.
Najeriya ta bukaci a yi watsi da hukuncin kotu kan P&ID
Bayanan sautiNajeriya ta bukaci a yi watsi da hukunci kan P&ID
Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hirar BBC da ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami
Gwamnatin Najeriya ta bakin ministan shari'arta kuma babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami, ta ce ta gabatar wa da kotu bukatarta a birnin Landan ta a yi watsi da hukuncin da ya bukaci gwamnatin ta biya kamfanin P&ID sama da dala biliyan 9.
Malami ya ce a da sun bukaci da a jinkirta hukuncin ne amma yanzu sun gano cewa hukuncin baki dayansa bai dace ba, kuma saboda haka ne suka bukaci da a yi watsi da shi baki daya.
Najeriya dai tana jira ne kotun ta fara sauraron daukaka karar da ta yi a kan hukuncin, wanda Malami ya ce komai na iya faruwa daga yanzu zuwa mako mai zuwa.
Gafaranku dai abokanmu
Abokan huldar BBC Hausa barkanku da safiyar Alhamis. Halima Umar Saleh da Umar Mikail ne ka maku barka da shigowa wannan shafi.
Ku duba kasa domin karanta labaran Laraba.
Daga yanzu zuwa yammaci kuma za mu mu ci gaba da kawo maku rahotannin na yau.
Birtaniya ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da 'yan kasuwar Najeriya
Sashen kasuwanci na kasa da kasa na gwamnatin Birtaniya ya karbi bakuncin wasu 'yan kasuwa daga Najeriya kusan 100, inda suka fitar da sashen noma da makamashi da lafiya da ayyukan raya kasa da kuma fasahar sadarwa wato ICT a cikin yarjejeniyar.
Taron ya zo ne yayin da ake shirin gudanar da taron zuba jari tsakanin Birtaniya da kasashen Afirka na 2020 da za a yi ranar 20 ga Janairun 2020. Taron zai duba hanyoyin guduwa da kuma tsira tare da kuma kirkirar ayyukan yi.
Yayin da yake jawabin bude taron a yau Laraba, magajin birnin Landan Sir Charles Bowman, ya bayyana cewa da ma can Birtaniya babbar kawar kasashen Afirka ce a fannin zuba jari.
Ba jami'anmu ne suka haddasa yamutsi a Kogi ba - Sufeton 'yan sanda
Babban Sufetan 'yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya ce jami'an 'yan sandan da ake zargin sun haddasa yamutsi a zabukan da aka gudanar a jihohin Kogi da Bayelsa ba 'yan sandan da aka tura jihohin don aikin zabe ba ne.
Lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban Najeriya jim kadan bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja, ya ce duk jami'an tsaron da aka tura jihohin suna dauke da wata shaida ta musamman ta yadda zaka iya gane su.
Asalin hoton, Nigeria police
Kamfanonin sadarwa na yin taro a Nijar
Asalin hoton, Getty Images
A jamhuriyar Nijar kungiyar shugabannin kamfanonin sadarwa na kasashen yankin UEMOA (kungiyar kasashen Yammacin Afirka masu amfani da kudin Sefa) ne wato COFTEL ke gudanar da taronsu
na shekara-shekara karo na 10, inda suke tattaunawa kan matsalolin sadarwa a yankin.
Ministan sadarwa na kasar Nijar Sani Mai Goshi ya ce burinsu shi ne su samar wa da 'yan kasashen kungiyar layukan sadarwa masu inganci.
"Mu burinmu shi ne duk dan kasa a wannan kungiya tamu shi ne ya samu damar buga waya ko ya saurari rediyo ko talabijin domin kuwa hakan yana da amfani sosai.
"A yanzu haka akwai wadanda ba su da wayoyin salula ko rediyo ko talabijin. Saboda haka idan wadannan kungiyoyi suka hada karfi wuri guda sai a yi doka domin su habaka aikinsu ta yadda duk dan Adam din da ke cikin kasashen zai samu damar mallakar rediyo."
Duk da kokarin da kungiyar ke cewa tana yi har yanzu
akwai jan aiki a gabanta.
An tube rawanin sarakuna 21 a jihar Oyo
Asalin hoton, @PULSEAFRICAMAG
Gwamnatin jihar Oyo ta tube rawanin sababbin sarakuna 21 daga a yunkurinta na sasantawa a wajen kotu tsakanin Olubadan, Oba Saliu Adetunji da kuma sarakunan bayan da aka shafe lokaci ana shari'a kan nadin nasu.
Gwamna Abiola Ajimobi ne dai ya nada sarakunan lokacin da yake daf da barin gadon mulkin jihar, kuma gwamnatin jihar ce ta nemi da a sasanta a wajen kotu bayan kotun daukaka kara ta mayar da shari'ar gaban wata karamar kotu a jihar.
Gwamna mai-ci Seyi Makinde ya dauki matakin ne domin sasanta wa tsakanin Olubadan da kuma sabbin sarakunan.
Abin da ya sa ba mu saki Sowore ba – Gwamnatin Najeriya
Asalin hoton, Sowore Facebook
Hukumar Tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS, ta magantu kan dalilin da ya sa har yanzu ba ta saki jagoran zanga-zangar #RevolutionNow ba, Omoyele Sowore.
Mai magana da yawun hukumar Peter Ifunaya, ya shaida wa manema labarai cewa dole sai masu tsayawa Sowore sun yi abin da ake bukata sannan a sake shi, idan ba haka ba za a ci gaba da tsare shi.
Mista Ifunaya ya ce sai dai har yanzu ba a samu masu tsaya masa din ba, maimakon haka ma sai wadanda suka shiga zanga-zangar tasa ce suke son tsaya masa, amma DSS tana da matakan da take bi kafin ta sake shin.