Kotu ta yi watsi da karar APC a Sokoto

Muna kawo muku bayanai dangane da zaman kotun musamman mai sauraron korafe-korafen zaben a jihohin Kano da Sokoto wadanda za su yanke hukunci kan wanda ya lashe zaben jihohin.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Rayyan

  1. Zaben Kano, Ganduje/Abba Gida-Gida

    Mai shari'a Halima Shamaki sanye da Hijab ta isa kotu domin fara zaman sauraron kara.

    APC/PDP
    Bayanan hoto, Mai shari'a Shamaki ta isa kotu
  2. Zaben Kano, Ganduje/Abba Gida-Gida

    Kotun da ke zaman sauraron karar a Kano ta fara zama kuma tuni ta yi cikar kwari. Jama'a sun yi wa kotun tsinke.

    APC/PDP

    Asalin hoton, BB

    Bayanan hoto, Jama'a na tsaye har a farfajiyar kotun da ke zaman sauraron karar gwaman a birnin Kano
    kano
    Bayanan hoto, Jami'an tsaro a kofar kotun da ke zama a birnin Kano
    Knao
    Bayanan hoto, 'Yan jarida sun yi cirko-cirko a wajen kotu lokacin da jami'an tsaro suka hana su shiga kafin daga bisani a ba su iznin shiga ciki
    APC/PDP
    Bayanan hoto, Shugaban Hukumar Karota mai kula da ababan hawa a jihar Kano, Baffa Babba Dan Agundi lokacin da yake shiga kotu
    Bayanan bidiyo, Barkwanci tsakanin shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas da shugaban PDP, Rabi'u Sulaiman Bichi a bakin kotu
  3. Zaben Sokoto, Tambuwal/Ahmed Aliyu

    A jihar Sokoto ma, kotun sauraron koke-koken zaben na dab da yanke hukunci kan shari'ar da dan takarar jam'iyyar APC Ahmed Aliyu ya shigar, inda ya kalubalanci zaben gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

    Tambuwal ya yi nasara a zaben Sokoton da kuri'u 512,002, bayan da ya doke abokin hamayyarsa, Ahmed Aliyu da ya samu kuri'u 511,660.

    Duk wanda hukuncin da ake sa ran bayyanawa a yau bai yi wa dadi ba to yana da damar daukaka kara.

    PDP/APC
    Bayanan hoto, Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC na kalubalantar Gwamna Aminu Tambuwal na PDP
  4. Zaben Kano, Ganduje/Abba Gida-Gida

    A shari'ar da ta shafi zaben Kano na ranar 9 ga watan Maris, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da 'Abba-Gida-Gida' ne ke fafatawa a gaban kotun karkashin mai shari'a Halima Shamaki.

    Dan takarar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ne ya shigar da karar, inda yake kalubalantar nasarar da Abdullahi Umar Ganduje ya samu a matsayin wanda ya ci zaben gwamna da aka yi bana.

    Ganduje ya ci zaben ne na biyu da tazarar kuri'a 35,637 inda jam'iyyarsa ta APC ta samu kuri'a 45,876 yayin da PDP ta samu 10,239.

    Idan aka hada sakamakon zaben na farko da na biyu, jimilla APC ta samu kuri'a 1,033,695, yayin da PDP ta samu jimilla 1,024,713. Hakan na nufin Ganduje ya ci zaben ne da tazarar kuri'a 8,982.

    Hukumar zaben Najeriya INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar Kano na ranar Asabar 9 ga watan Maris, a matsayin wanda bai kammala ba, lamarin da ya kai ga zagaye na biyu.

    PDP/APC
    Bayanan hoto, Abba Gida-Gida na kalubalantar Gwamna Ganduje
  5. Zaben Sokoto, Tambuwal/Ahmed Aliyu

    A jihar Sokoto ma, kotun sauraron koke-koken zaben na dab da yanke hukunci kan shari'ar da dan takarar jam'iyyar APC Ahmed Aliyu ya shigar, inda ya kalubalanci zaben gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

    PDP
    Bayanan hoto, Aminu Tambuwal
  6. Zaben Kano, Ganduje/Abba Gida-Gida

    A ranar Laraba ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a jihar Kano za ta yanke hukunci kan shari'ar da ake tsakanin Gwamna Ganduje mai ci da Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP.

    Ganduje
    Bayanan hoto, Abba Gida Gida
    APC
    Bayanan hoto, Abdullahi Umar Ganduje