Buhari ya ba Sheikh Pantami Ministan Sadarwa

A ranar Larabar nan ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ke rantsar tare da bai wa sabbin ministoci 43 ma'aikatun da za su jagoranta, a sabon zangon mulkinsa na biyu.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Bikin rantsar da ministoci, Fuskokin ministoci

    Wasu sabbin ministoci tare da tsohon shugaban ma'aikatan Najeriya, Alhaji Yayale Ahmed lokacin yi wa ministocin bitar kama aiki a Abuja.

    Buhari
  2. Bikin rantsar da ministoci, Fuskokin ministoci

    Babatunde Raji Fashola, tsohon ministan ma'aikatar lantarki da ayyuka da gidaje a zangon mulkin Buhari na farko wanda kuma ya sake dawowa.

    Buhari

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Bikin rantsar da ministoci, Fuskokin ministoci

    Rotimi Amaechi a taron majalisar ministoci a zangon farko

    ministoci

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Bikin rantsar da ministoci, Fuskokin sabbin ministoci

    Hadi Sirika tshon ministan sufurin jiragen sama da Rotimi Amaechi tsohon ministan sufuri tare da Shugaba Buhari a jirgin kasa.

    Buhari

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ministoci goma sha biyu ne suka dawo zangon mulki na biyu
  5. Bikin rantsar da sabbin ministoci, Sharhi

    Tun bayan kawo karshen wa'adin mulkinsa na farko, Shugaba Buhari ya yi ikirarin cewa ministocinsa sun taka rawar gani, kuma shi ne dalilin da ya sa ya ci gaba da tafiya da su har tsawon shekara uku da rabi wato zuwa karshen wa'adinsa ba tare da ya sauya su ba.

    Buhari ya yi ikirarin cewa sun samu nasarar cika alkawuran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe, kuma ministocin sun taka rawa ga samun nasarar.

    Dakta Abubakar Kari, mai sharhi kan lamuran yau da kullum a Najeriya ya shaida wa BBC cewa akwai ministoci da dama da ba su taka rawar gani ba, wadanda ya ce "ba su cancanta a sake tafiya da su ba."

    "Idan ka yi maganar ma'aikatu kamar na lafiya da sadarwa da na jiragen sama, ayyukan da ministocin suka yi bai gamsar da 'yan Najeriya ba."

    "Sun kuma yi alkawura da dama kamar na magance matsalar wuta da kuma hanyoyi da suka kasa aiwatarwa," a cewarsa.

    Dakta Kari ya jaddada cewa wadannan abubuwan da ya lissafo, ba wai yana nufin cewa ba su tabuka komai ba, "mutane dai ba su ga ayyukan da suka yi tunanin za a yi ba."

    Buhari
    Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya sha rantsuwar kama aiki a zango na biyu ranar 29 ga Mayu, 2019
  6. Bikin rantsar da ministoci, Sabbin ministoci maza

    • Sheikh Isa Ali Pantami - Gombe
    • Sanata Godswill Akpabio - Akwa Ibom
    • Alhaji Sabo Nanono - Kano
    • Rauf Aregbesola tsohon gwamnan - Osun
    • George Akume - tsohon gwamnan - Benue
    • Timipre Sylva - tsohon gwamnan - Bayelsa
    • Sanata Olorunnibe Mamora - Legas
    • Sunday Dare - Oyo
    • Festus Keyamo - Delta
    • Sanata Tayo Alasoadura - Ondo
    • Mustapha Buba Jedi Agba -
    • Olamilekan Adegbite - Ogun
    • Mohammed Dangyadi - Sokoto
    • Abubakar Aliyu - Yobe
    • Sale Mamman - Taraba
    • Muhammed Mamood - Kaduna
    • Uce Ogar - Abia
    • Emeka Nwajuiba - Imo
    • Akpa Udo
    • Clement Abam
    • Zubair Dada
    • Adeniyi Adebayo - Ekiti
    • Mohammed Abdullahi
    • Osagie Ehenere
    • Bashir Salihi Magashi - Kano
    ministoci

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wasu ministocin da aka yi wa bita gabanin rantsar da su ranar Laraba
  7. Bikin rantsar da ministoci, Tsaffin ministoci maza da suka dawo

    • Babatunde Fashola - Tsohon Ministan lantarki da Ayyuka da Gidaje
    • Rotimi Amaechi - Tsohon Ministan Sufuri
    • Ogbonnaya Onu - Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha
    • Adamu Adamu - Tsohon Ministan Ilimi
    • Sanata Chris Ngige - Tsohon Ministan Kwadago H
    • Hadi Sirika - Tsohon Karamin Ministan Sufurin Jiragen Sama
    • Zainab Ahmad - Tsohuwar Ministar Kudi
    • Lai Mohammed - Tsohon Ministan Watsa Labarai
    • Musa Bello - Tsohon Minsitan Abuja
    • Abubakar Malami - Tsohon Ministan Shari'a
    • Sulaiman Adamu - Tsohon ministan ruwa
    • Baba Shehuri - Tsohon karamin ministan lantarki da ayyuka da gidaje
  8. Bikin rantsar da ministoci, Ministoci mata bakwai

    • Sharon Ikeazor daga Anambra
    • Ambasada Maryam Katagum daga Bauchi
    • Gbemi Saraki daga Kwara
    • Ramatu Tijani daga Kogi
    • Pauline Tallen daga Filato
    • Zainab Ahmed daga Kaduna
    • Sadiya Farouq daga Zamfara.
    Ministoci

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wani bangare na sabbin ministocin da aka yi wa bita
  9. Bikin rantsar da ministoci, Abuja

    A ranar Laraban nan Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai rantsar da majalisar ministocinsa, don fara aiki gadan-gadan a wa'adi na biyu na mulkinsa, bayan lashen zaben watan Fabrairu.

    Sabbin ministocin 43 da majalisar dattawa ta tantance sun hada da mutum 12 da aka yi wa'adin farko da su, da kuma mata guda bakwai.

    Ministocin su ne za su taimaka wa Buhari wajen tsarawa da aiwatar da alkawurran zabe da ya yi wa 'yan Najeriya, a matsayinta na kasa mafi girman tattalin arziki a Afirka.

    Ana sa ran shugaban zai sanar da ma'aikatar da kowanne minista zai yi aiki.

    Wannan na zuwa bayan shugaban ya jagoranci taron bitar sanin makamar aiki ga ministocinsa a ranar Talata.

    Ana sa ran bayan bikin rantsar da ministocin, shugaban kuma zai kaddamar da majalisar zartarwa ta hanyar jagorantar zaman farko da sabbin ministocin nasa.

    Kusan wata uku kenan aka shafe ana tafiyar da gwamnati ba ministoci tun rantsar da Buhari a ranar 29 ga Mayu.

    Ko da yake, a wa'adin mulkinsa na farko, shugaban bai nada ministoci ba sai bayan kusan watanni shida da karbar ragamar mulkin kasar.

    Ministoci

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya yi wa sabbin ministoci bitar kwana biyu kafin rantsar da su ranar Laraba