Ranar Dimokradiyya, Ranar Dimokradiyya
Yanzu haka ana gabatar da tarihin Shugaba Muhammadu Buhari, yayin da shi kuma yake zagaya filiun ytaron yana daga wa mahalarta hannu.

Asalin hoton, Channels TV
Labarai da rahotanni kai tsaye game da Ranar Dimokradiyya a Najeriya, inda a bana kasar take bikin cika shekara 20 da komawa tafarkin dimokradiyya.
Naziru Mikailu, Umar Rayyan and Umar Mikail
Yanzu haka ana gabatar da tarihin Shugaba Muhammadu Buhari, yayin da shi kuma yake zagaya filiun ytaron yana daga wa mahalarta hannu.

Asalin hoton, Channels TV





Shugaba Muhammadu ya karaso wurin taron, wanda dama shi ne babban bako na musamman kuyma ake jira.

Asalin hoton, Channels TV
Paul Kagame shugaban kasar Rwanda ya iso filin taro.
Ana ci gaba da jiran karasowar Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne babban bako na musamman.

Asalin hoton, Channels TV
A ranar Laraba ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kaddamar da ranar dimokradiyya a karon farko, bayan mayar da ita zuwa bikin 12 ga watan Yuni maimakon 29 ga watan Mayu kamar yadda aka saba a baya.
Bikin ranar 12 ga watan Yuni, na tunawa ne da zaben shugaban Najeriya na 1993, wanda akasarin mutane suka yi imani cewa sanannen dan siyasar kasar marigayi Cif MKO Abiola ne ya yi nasarar ci, kafin gwamnatin mulkin soja ta lokacin Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ta soke zaben.

Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya karaso filin taro yayin da ake ci gaba da jiran Shugaban kasar Buhari.

Asalin hoton, Channels TV
Jagoran jam'iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Tinubu ya ce 12 ga watan Yuni ta fi dacewa da Ranar Dimokradiyya sama da ranar 29 ga watan Mayu.
Tinubu ya bayyana haka ne a wani bayani da ya aike wa manema labarai wanda kuma jaridar PM News ta buga mai taken:12 ga Yuni: Gaskiyar da ta tabbatar da 'yancin dimokradiyya a kasarmu.
Ya kara da cewa 29 ga watan Mayu ba ta nuna wani hoto mai muhimmanci game da dimokradiyyar Najeriya kamar 12 ga watan Yuni.
"Ba don wadanda suka tsaya kai-da-fata ba a ranar 12 ga Yuni (1993) suka sadaukar da rayuwarsu da 'yancinsu da kuma tunaninsu a yayin yaki da mulkin kama-karya da ba a samu mika mulki ba ga gwamnatin farar hula a 29 ga watan Mayun 1999."

Asalin hoton, Premium Times
Yanzu haka an fara gabatar da fareti a wurin taron.

Asalin hoton, Channels TV
Bisa al'ada a kan yi bukukuwa a irin wannan rana don tunawa da irin nasarar da Najeriya ta samu game da mulkin dimokradiyya, kuma bikin na yau za a yi shi ne a filin Eagle Square da ke Abuja.
A yau ana sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga 'yan kasa a matsayin wani bangare na bikin, wanda kara'i ne na ranar 29 ga watan Mayu bayan rantsar da shi a karo na biyu.
Babu tabbaci ko Shugaabn zai bayyana sunayen ministocin da zai yi aiki da su a sabuwar gwamnatinsa, domin kuwa ya bayyana a watan da ya gabata cewa bai tattauna da kowa ba game da mininstocin.
Za a yi faretin girmamawa yayin bikin.
A jihohi ma ana sa ran za a yi bukukuwa, sai dai babu tabbas ko za a ji sabbin abubuwa daga gwamnonin jihohin ganin cewa wasunsu sun gabatar da jawabai tun ranar da suka sha rantsuwar kama aikin.
Kwamitin shirya bikin Ranar Dimokwaradiyya a Najeriya ya bayyana wasu tituna da aka killace a babban birnin tarayya Abuja saboda bikin ranar ta 12 ga watan Yuni.
Shugaban tsare-tsare na kwamitin kuma Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya bayar da sanarwar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito, inda ya ce killacewar za ta fara aiki tun daga daren Talata zuwa karfe 3:00 na ranar Laraba.
Titunan da canjin ya shafa su ne:
Diversion ‘B’ Aso Drive by DSS Headquarters-DPO Mpape;
Diversion ‘C’ FCDA by Finance Headquarters;
Diversion ‘D’ Bayelsa House;
“Diversion ‘D’ Gana-Transcorp Hilton;
Diversion ‘F’ NITEL Junction by Ahmadu Bello Way; Diversion ‘G’ Kur Mohammed by Benue House;
Diversion ‘H’ NNPC Tower;
Diversion ‘I’ Federal Secretariat Phase III under the bridge;
“Diversion ‘J’ Behind Foreign Affairs under the bridge;
Diversion ‘K’ FCDA by POWA
Diversion ‘L’ Goodluck Ebele Jonathan Expressway (Inter Section into 3 Arm Zone) and Diversion ‘M’ Flyover by Jaiz Bank
Yau Laraba ne Najeriya take cika shekara 20 da komawa bin tafarkin dimokradiyya, inda ta yi shugabanni hudu a tsawon wadannan shekaru.

Yau take Ranar Dimokradiyya!
Jama'a barka da shigowa wannan shafi wanda zai rika kawo maku labarai da rahotanni kai tsaye game da Ranar Dimokradiyya a Najeriya, inda a bana kasar take bikin cika shekara 20 da komawa tafarkin dimokradiyya.
Umar Mikail da Umar Rayyan da Naziru Mika'ilu ne ke maku fatan an tashi lafiya.