Yadda ake gudanar da muhawara tsakanin 'yan takara biyar da ke neman kujerar gwamnan jihar Gombe.
Rahoto kai-tsaye
Nasidi Adamu Yahya and Mustapha Kaita
Zan bai wa tsaro da bunkasa ilimi muhimmanci - Inuwa Yahaya
Dan takarar APC Inuwa Yahaya ya ce tsaro da bunkasa ilimi da magance matsalar yawan mace macen mata da yara kanana da bunkasa harkar noma ne zai sa gaba. Ya ce Gombe ta koma baya a fannin ilimi, yana mai cewa wasu alkaluma sun nuna koma bayan ya nuna kashi uku bisa hudu na 'yan jihar na fama da wannan matsala. A cewarsa, zai bunkasa ilimi a matakin farko.
Zan bai wa zaman lafiya da ruwan sha fifiko - Bayero Nafada
Dan takarar PDP Bayero Usman Nafada ne ya fara gabatar da kansa. Ya ce tsaro da zaman lafiya da ruwan sha da kiwon lafiya da habaka masana’antu ne zai sa gaba.
Ya ce zai inganta rayuwar malamai, zai yi kokarin ganin iyaye sun tura yaya makaranta, zai bunkasa ilimi malaman sakamdare da jamioi da sauran makarantu na gaba da sakandare, ya ce burinsa Gombe ta zama ta daya a fannin ilimi.
Masu larurar nakasa ma ba a bar su a baya ba
Daya daga cikin masu lalurar nakasa ke nan da suka hallarci wajen wannan muhawarar.
Bayanan bidiyo, Dakin muhawara ya fara cika
, Kun san wanda zai jagoranci muhawarar?
Ibrahim Isa dai zai jagoranci muhawarar yana jaddada gargadi ga mutanen da suka halarci zauren muhawarar za su bada hadin kai ga ka'idoji da sharudda da aka shata a zauren muhawarar da suka hada da kai kawo tsakanin mutane domin daukar hotuna da bidiyo ko kuma kokarin gaisawa da yan takara. Ko kuma daukar tsarabar da aka tanadar a kan ko wace kujera fiye da daya.
Bayanan bidiyo, Kun san wanda zaya jagoranci muhawarar?
'Yan takara sun iso
'Yan takara hudu da za su fafata a wurin muhawarar da BBC Hausa ta shirya a gombe sun isa inda za a yi muhawarar. Suna jira a soma tafka muhawa da misalin karfe goma na safe a agogon Najeriya da Nijar.
Zauren muhawara ya fara cika
Zauren da za a gudanar da muhawara a Gombe ya fara cika domin kuwa mutane suna ta tururuwar shigowa zauren domin gane ma idonsu yadda wannan muhawarar za ta kaya.
Wali Ahmed Modibbo
An haifi
Wali Ahmed ne a Kumo dake karamar hukumar Dukku dake jihar Gombe. Ya yi difiloma
a Management Studies, sai kuma digiri a fannin akanta (accountant) da kuma
digiri na biyu a fannin karatun addinin Islama.
Yayi aiki a matsayin magatakarda na babbar
kotu dake Bauchi.
Yayi retire
a matsayin mataimakin shugaban hukumar hana shige da fice ta Najeriya. Yayi takarar gwamna a 2015 a karkashin
jam’iyyar APGA. Hakazalika shine mawallafin mujallar Karatu wace aka fi sani da Karatu magazine. Wali Ahmed na daya daga cikin ‘yan kungiyar bada agaji ta Red
Cross da kuma kungiyar Zabi Sonka ta RTK.
Inuwa Yahaya
An haifi
Inuwa Yahaya a Jekadafari a jihar Gombe a ranar 9 ga watan Octoba 1961. Ya
karanta fannin akanta a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria inda ya gama a 1983.
Yahaya ya yi kwasakwasai da dama domin sanin makamar aiki a Najeriya da ma wasu
kasashen ketare. Ya fara aikinsa a matsayin akanta a ma’aikatar state
investment and property development dake Bauchi, sai daga baya ya koma kamfanin
Nasara motors inda ya zama manajan gudanarwa da hada-hadar kudade. Inuwa ya
shiga siyasa ne a 2003 a lokacin mulkin Danjuma Goje. Ya zama kwamishinan kudi
da ci gaban tattalin arziki a lokacin mulkin Goje. Inuwa dai ya shafe fiye da shekaru
bakwai a matsayin comissioner.
Abdul-Ghaniy Bello Akko
An haifi Barrister Abdul-ghaniyu Bello na
jam’iyyar PRP a gombe a kuma ranar 16 ga watan Satumba 1995.
Yayi makarantar firamare a central primary
school dake Gombe, sai kuma sakandare a GSS Kazaure sai kuma ya garzaya Jami’ar
Ahmadu Bello dake Zaria. Yayi aiki a matsayin Alkali a kotun Magistare,
sa’annan yayi aiki a matsayin lauyan gwamnati mai shigar da kara a tsohuwar jihar
Bauchi bayan nan ne ya zama lauyan kamfanin hako ma’adinai na NIOMCO, dake
Itakpe.
Yayi ritaya da kansa a 2007. Ya dai taba
zama shugaban kungiyar lauyoyi musulmai ta Najeriya. Yanzu haka dai
Abdul-ghaniyu lauya ne mai zaman kansa kuma dan siyasa.
Usman Bayero Nafada
An haifi Usman Bayero Nafada a 2 ga watan
Junairu 1961 a jihar Gombe.
Yayi karatun firamari a Nafada Central
Primary School dake Nafada, sai kuma makaranatar horar da malamai ta gwamnati a
Gombe.
Ya hallarci jami'ar Maiduguri inda ya samu
digiri a
fannin akanta (accountant.)
An zabi Nafada a matsayin dan majalisar jiha
mai wakiltar Dukku/Nafada daga 1999-2003 a karkashin jam'iyyar ANPP.
A 2007, Nafada ya zama mataimakin kakakin
majalisar wakilai ta tarayya.
Haka dai a 2015 ne ya zama dan majalisar
dattijai mai wakiltar Gombe ta Arewa.
Asalin hoton, Bangies Kabasha
Takaitaccen tarihin jihar Gombe
Gombe
jiha ce da ke arewa maso gabashin Najeriya, haka kuma babban birnin jihar shi ne Gombe.
Gombe dai jiha ce da ke cikin jihohi 36 na kasar.
An kirkiri Gombe ne a lokacin mulkin soji
na General Sani Abacha inda aka cire garin daga jihar Bauchi a 1996.
Gombe tana da iyaka da jihohin Borno,
Yobe, Taraba, Adamawa da kuma Bauchi.
A 2006, an kidaya yawan mutanen jihar da
yawan su ya kai 2,365,000.
Gombe dai jiha ce da ke da kabilu daban-daban
amma kabilar Fulani sune
mafi rinjaye,
musamman a arewacin jihar.
Akwai 'yan kabilar Tangale wadanda sune suka
mamaye kudancin jihar, sai kuma sauran kabilun da ke cikin jihar sun hada da
Hausa, Tera. Waja, Bolewa da kuma Kanuri.
Kabilar Tera a jihar na daga cikin Kabila mai
yawan jama'a idan aka cire Fulani da Hausa, domin kuwa kabilar Tera ne suka
mamaye karamar hukumar Deba.
Gombe dai tana da kananan hukumomi 11 da suka
hada da Akko, Balanga, Billiri, Dukku, Funakaye, Gombe, Kaltungo, Kwami,
Nafada, Shongom, Yamaltu/Deba.
A yanzu haka dai, gwamnan jihar shine Ibrahim
Hassan Dankwambo.
Gombe tana da 'yan majalisar jiha 24 sai na
tarayya 6, sai kuma 'yan majalisar dattawa 3.
Gwamnonin jihar Gombe a baya sun hada da
Group Captain Joseph Orji1996-1998
Mohammed Bawa1998-1999
Abubakar Habu Hashidu1999-2003
Mohammed Danjuma Goje 2003-2011
Masu bibiyar wannan shafi, Nasidi Adamu Yahaya da Mustapha Kaita ne ke yi muku barka da wannan safiya. Da fatan za ku kasance tare da mu domin samun labarai da rahotanni da hotuna da bidiyo kan muhawarar da 'yan takarar gwamnan jihar Gombe ke fafatawa, wacce BBC Hausa ke gabatarwa kai-tsaye.