Yadda aka yi jana'izar Shehu Shagari

Karanta bayanai da labarai game da jana'izar tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Aliyu Shagari, shugaba na farko mai cikakken iko wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Juma'a.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Haruna Shehu Tangaza

  1. Gawar Shehu Shagari ta isa Sakkwato daga Abuja, Shehu Shagari ya rasu

    Gawar tsohon Shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari ta iso jiharsa ta Sakkwato domin yi masa jana’iza.

    Gawar Shehu Shagari
  2. Yadda Shagari ya fara shiga siyasa, Alhaji Shehu Shagari ya rasu

    Alhaji Shehu Shagari ya fara harkokin siyasa ne tun shekarun 1950 gabanin samun ‘yancin kan Najeriya lokacin da ya jagoranci wata kungiyar matasa da ta taimaka wajen kafuwar jam’iyyar NPC wadda Ita ce jam’iyyar da ta fara mulkin kasar a jamhuriyya ta farko.

    Ya kwashe kusan shekaru talatin yana taka rawa a fagen siyasar kasar abin har ya kai shi ga zamowarsa zababben shugaban farar hulla na farko a Najeriya.

    Tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari
  3. Najeriya ta yi rashin Uba - Dogara

    Kakakin majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara a sakon ta'aziyarsa ya ce Najeriya ta yi rashin uba mai son zaman lafiya da kishin kasa tare da cewa an rasa dan kasa nagari.

    shehu Shagari

    Asalin hoton, Family

  4. Sakon ta'aziyar Sanata Bukola Saraki

    A sakon da ya fitar ta shafinsa na twitter Shugaban Majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki ya roki Allah ya jikan marigayi Alhaji Shehu Shagari.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Shagari ba ya da kabilanci - Atiku

    Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya ce bayyana Shagari a matsayin wanda ba ya da kabilanci wanda ya bauta wa Najeriya tun yana matashi da malami da har ya zama shugaban kasa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Shagari ya yi siyasa ba da gaba ba - IBB, Tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari ya rasu

    A sakon da ya aika kan rasuwar Shagar, tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce za a tuna mamacin a matsayin wanda ya gudanar da harkokin siyasa ba tare da gaba ba, kuma wanda bai nuna bambanci tsakanin al'ummar kasar ba.

    IBB
  7. Shagari ya yi wa Najeriya aiki da gaskiya - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a sakon ta'aziyarsa ya ce yana alhinin mutuwar dan kasa nagari da ya yi wa Najeriyta aiki da gaskiya. Ya ce Shagari mutum ne da ke da daraja ga 'yan Najeriya ko bayan ya bar mukamin shugaban kasa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Kakannin Shagari sun taimaka wa Dan Fodio yin Jihadi, Tsohon Shugaban Najeriya Shehu Shagari ya rasu

    Alhaji Bello Idris shugaban gidan ajiye kayan tarihi na Waziri Junaidu da ke Sakkwato ya shaida wa BBC cewa kakannin Alhaji Shehu Shagari suka kafa garin Shagari wadanda Fulani ne da suka taso daga Kauran Namoda yanzu a Jihar Zamfara suka shiga cikin rundunar mujaddadi Shehu Usman Dan Fodio lokacin jihadi inda suka kafa garin da suka kira Shagari da ke jihar Sakkwato.

    Shehu Shagari

    Asalin hoton, Family

  9. Wane ne Shehu Shagari?

    - Dan asalin jihar Sakkwato ne a arewa maso yammacin Najeriya

    - An haife shi a shekarar 1925 a garin Shagari

    - Shi ne na shida ga maifinsa Aliyu

    - Dan siyasa ne Manomi kuma makiyayi

    - Malamin Makaranta ne marubucin wakoki da tarihi

    - Ya zama shugaban kasa ne karkashin jam’iyyar NPN

    - Ya shugabanci Najeriya daga 1979 zuwa 1983

    - Bayan sojoji sun hambarar da gwamnatinsa, Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa a mulkin soja

    - Kafin Shagari ya zama shugaban kasa ya taba zama sakataren majalisar Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa

    - Ya rike mukaman minista daban-daban

    - Ya taba zama ministan ci gaban tattalin arziki a shekarar 1960

    -Ya taba zama ministan kula da harkokin cikin gida a shekarar I962

    - Ya taba rike ministan ayyuka da safiyo (1965).

    - Shagari ne Turakin Sakkwato, wanda babban wakili ne a majalisar koli ta fadar Sarkin Musulmi.

    Tsohon Shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari

    Asalin hoton, Family

  10. Za a yi jana'izarsa a Shagari, Allah Ya yi wa Shehu Shagari rasuwa

    Tsohon shugaban ya rasu ne ranar Juma'a a asibitin kasa da ke Abuja bayan fama da jinya.

  11. Barkanmu da warhaka

    Muna maku barka da rana a wannan lokacin da za mu kawo maku bayanai kai-tsaye game da jana'izar tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari da Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Juma'a.

    Tsohon Shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari

    Asalin hoton, Family