Wa zai maye gurbin Mourinho a Old Trafford?

Zidane Zidane da Pochettino na Tottenham da Simone na Atletico Madrid ake tunanin za su maye gurbin Jose Mourinho a Old Trafford bayan ya raba gari da Manchester United.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau

  1. Shin Mourinho zai sake samun wani Kulub?, Mourinho ya bar Manchester

    Wasu na ganin salon kwallon Mourinho yanzu ya sauya, inda yake amfani da wasu dubarun taka leda da aka daina amfani da su.

    Masharhanta na ganin yana da wahala ya iya sake samun wani babban kulub.

    A baya wasu rahotanni sun danganta shi da cewa Real Madrid za ta sake daukar shi bayan ta kori kocinta.

    Jose Mourinho

    Asalin hoton, Reuters

  2. Martanin Chelsea, Mourinho ya bar Manchester

    Mourinho ya lashe kofuna uku a Chelsea a karo biyu da ya yi aiki a Stamford Bridge. A watan Disemban 2017 Chelsea ta kore shi kafin ya koma Old Trafford.

    Mataimakin manajan Chelsea Gianfranco Zola ya ce bai ji wa Mourinho dadi ba musamman mutumin da ya lashe kofuna a Chelsea.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Evra ya ce gyara Manchester ke bukata yanzu, Mourinho ya bar Manchester

    Patrice Evra ya nuna damuwa kan yadda mutane suka damu da sakon Pogba da kuma korar Mourinho. Ya ce yanzu gyara mai dorewa ya kamata a mayar da hankali a kai.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. 'Yan wasan da Mourinho ya saya a Manchester, Mourinho ya bar Manchester

    Mourinho ya kashe jimillar kudi fam miliyan £358.8 wajen sayen 'yan wasa tun zuwansa Manchester United.

    Eric Bailly – Dan wasan baya - daga Villarreal - £30m

    ·Zlatan Ibrahimovic – Dan wasan gaba - daga Paris St-Germain - ya zo a son kansa

    ·Henrikh Mkhitaryan – Dan wasan tsakiya- daga Borussia Dortmund - £26.3m

    ·Paul Pogba - Dan wasan tsakiya - daga Juventus - £89m

    ·Victor Lindelof – Dan wasan baya - daga Benfica - £31m

    ·Romelu Lukaku – Dan wasan gaba - daga Everton - £75m

    ·Nemanja Matic - Dan wasan tsakiya - daga Chelsea - £40m

    ·Alexis Sanchez – Dan wasan gaba - Arsenal - musaya da Mkhitaryan

    ·Diogo Dalot – Dan wasan gaba - daga Porto - £19m

    ·Fred - Dan wasan tsakiya - daga Shakhtar Donetsk - £47m

    ·Lee Grant – Mai tsaron gida - daga Stoke £1.5m

  5. Shin Mourinho bai zo da sa’a ba ne a Old Trafford?

    Mourinho ya horar da kungiyoyi a Portugal da Ingila da Spain da Italiya.

    Ya lashe kofuna a kungiyoyin da ya horar a Porto da Real Madrid da Inter milan da Chelsea.

    Sai dai kuma a Manchester United ya fuskanci kalubale duk da cewa ya lashe kofin kalubale da Europa League.

    Amma wasu na ganin tun zuwansa ya kasa sauya abubuwa a Old Trafford.

    Mourinho

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Mataki ne da ya dace – Owen, Mourinho ya bar Manchester

    Tsohon dan wasan Manchester United Michael Owen ya ce korar Mourinho mataki ne da ya dace, domin 'yan wasansa sun kasa tabuka komi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Abin da Gary Lineker ya ce

    Tsohon dan wasan Ingila Gary Lineker ya ce Mourinho ya kashe miliyoyin kudi wajen sayen ‘yan wasa amma ba amfani.

    Tazarar maki 19 Liverpool ta ba Manchester a tebur bayan buga wasa 17. Kuma yawancin ‘yan wasan ba su taka leda yadda ya dace, in ji shi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Abin da ya faru

    Manchester ta kori Mourinho

    Za a nada kocin rikon kwarya

    Carrick zai jagoranci atisaye

    Paul Pogba ya yi gaggawar goge sakon da ya tura a Twitter bayan korar Mourinho.

  9. Mourinho ya bar Old Trafford

    Manchester United ta raba gari da Jose Mourinho bayan shekara biyu da rabi yana horar da kungiyar.

    Mourinho mai shekara 55, ya lashe kofin kalubale na Ingila da Europa League a Old Trafford.

    Amma United tana matsayi na shida a teburin Premier, tazarar maki 19 tsakaninta da Liverpool da ke saman teburin kuma wacce ta lallasa Mourinho 3-1 a ranar Lahadi.

    Manchester ta gode wa Mourinho tare da ma shi fatan alheri.

    Jose Mourinho

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Mourinho ya fito aiki kafin a kore shi

    Mourinho ya fito aiki da safiyar Talata bayan ya san cewa Manchester United za ta kori shi.

    Jose Mourinho

    Asalin hoton, Zenpix

  11. Muna maku maraba, Mourinho ya bar Manchester

    Barkarmu da kasancewa a cikin wannan shafin inda za mu kawo ma ku sharhi da bayanai bayan Manchester United ta kori Jose Mourinho a matsayin kocinta.

    Jose Mourinho

    Asalin hoton, Getty Images