An fara kada kuri'a a Osogbo

An fara kada kuri'a a karamar hukumar Osogbo ne da misalin karfe takwas da minti biyar.
Labarai da sharhi game da karashen zaben gwamnan Osun inda dan takarar jam'iyyar PDP da na APC suka kara.
Abdulwasiu Hassan

An fara kada kuri'a a karamar hukumar Osogbo ne da misalin karfe takwas da minti biyar.

Mutane sun fito sosai domin kada kuri'u a rumfunar zabe bakwai din da ake zaben a yau.

Jama'a, barkanku da shigowa wannan shafi inda za mu kawo muku yadda ake karasa zaben gwamnan jihar Osun da aka fara ranar Asabar.
Ranar Lahadi ne dai hukumar zabe ta INEC ta yanke hukuncin cewar ba a kammala zaben ba, kuma za a karasa zabe a wasu rumfunar zabe bakwai da ba a yi zabe ba ko kuma aka soke zabensu.