Karanta yadda aka yi zaben gwamnan Osun

Labarai da sharhi game da yadda ake zaben gwamna a Osun wanda ake ganin zai nun irin yadda zaben 2019 zai kasance a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Abdulwasiu Hassan

  1. Dan takarar ADP ya kada kuri'a

    Dan takarar jam'iyyar ADP, Moshood Adeoti, ya kada kuriarsa.

    Moshood Adeoti
    Bayanan hoto, Moshood Adeoti bayan ya kada kuri'arsa
  2. BBC ta yi tir da yadda magoya bayan dan takarar jam'iyyar ADP suka saka rigarta

    BBC ta yi tir da yadda maogaya bayan 'dan takarar jam'iyyar ADP, Moshood Adeoti, suka saka rigarta zuwa wajen zabe.

    Sun samu rigunan ne a lokacin da aka yi wata muhawara da BBC ta shirya wa 'yan takarar gwamna a jihar domin mutane su san manufofin 'yan takarar da ke neman mukamin gwamnan jihar.

    Zabe
  3. Dan takarar jam'iyyar APC ya kada kuri'arsa

    Oyetola
    Bayanan hoto, Gboyega Oyetola ya kada kuri'a

    Dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan da ake yi a jihar Osun, Alhaji Gboyega Oyetola ya kada kuri'arsa.

    Oyetola ya kada kuri'a

    Asalin hoton, bb

  4. PDP ta yi zargin cewar APC na raba kudi

    Babbar jam'iyyar adawar Najeriya, PDP, ta yi zargin cewa jami'an jam'iyyar APC mai mulkin kasar da jihar Osun inda ake zaben gwamna sun raba kudi wa masu zabe a rumfar zabe ta 8 a mazaba ta uku a karamar hukumar Olorunda da ke jihar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Me ya sa ake zaben gwamna a jihar Osun a lokaci na daban?

    Zaben osun

    Bayan an gama zaben gwamnan jihar a shekarar 2007, sai Rauf Aregbesola ya kai kara a kotu.

    Ranar 26 ga watan Nuwambar shekarar 2010 ne kotun daukaka kara ta ce Rauf Aregbesola ne gwamnan jihar.

    Kuma ranar 27 ga watan Nuwamba ne aka rantsar da Rauf a matsayin gwamnan jihar Osun.

    A halin yanzu Rauf ya kammala wa'adinsa na biyu. Kuma lokaci ya yi da zai mika wa wani ragamar mulki.

  6. Dan takarar jam'iyyar ADC, Fatai Akinbade, ya fito da daga Iwo

    A halin yanzu dai an fara zabe a Iwo
  7. Masu sayar da abinci na ciniki

    Osun

    A lokacin da dai ake wanan zabe na gwamna masu abinci sun fito domin sayar wa mutane abinci.

    Osun
  8. Ba a bar masu larura a baya ba

    A zaben na jihar osun ba a bar masu larura a baya ba domin su ma sun fito zabe.

    Bayanan bidiyo, Wani mai larurar tawaya bai yarda tawayarsa ta hana shi yin zabe ba
  9. Ministan lafiyar Najeriya ya isa rumfar zabe

    Ministan Lafiyar Najeriya, Isaac Adewole, ya isa rumfar zaben da ke mazabarsa.

    Adewole
  10. An fara da duba sunaye a rijista

    Masu zabe dai a jihar ta Osun sun fara duba sunayensu ne dai a rijistar zaben da ke rumfunar zabensu da sanyin safiyar Asabar.

    Duba sunaye a rijista
  11. Masu sa'ido a zabe suna nan

    Jami'ai masu sa ido zabe na kasa-da-kasa suna nan a jihar ta Osun don ganin yadda ake gudanar da zaben.

    Observers
  12. Dan takarar PDP ya kada kuri'a

    Dan takarar PDP a zaben Sanata Nuruddeen Adeleke ya kada kuri'a.

    Adeleke
    Bayanan hoto, Adeleke kenan yana kada kuri'arsa a Ede
  13. Barka da zuwa

    Jama'a, barka da shigowa wannan shafin inda za mu kawo muku yadda ake zaben gwamna a jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya.