Yadda Faransa ta lashe kofin duniya

Labarai da sharhi game fa da wasan karshe na gasar kofin duniya na shekarar 2018 da ake yi a birnin St Petersburg na Rasha

Rahoto kai-tsaye

Abdulwasiu Hassan

  1. Wasa ya fara zafi

    Croatia na neman ramawa yayin da Fransa ke naman hana su ko kuma kara musu.

  2. GOAL, Faransa 2-1 Croatia

    Antoine Griezmann ne ya ci wa Faransa ta hanyar fenareti.

    Griezmann

    Asalin hoton, Reuters

  3. Faransa ta samu fenareti, Faransa 1-1 Croatia

    Faransa za ta iya ci kuwa?

  4. Faransa nea neman Fenareti, Faransa 1-1 Croatia

    Faransa nea neman Fenareti. Lafiri zai je dubawa.

  5. GOAL, Faransa 1-1 Croatia

    Ivan Perisic ne ya ci wa Croatia kwallon

  6. GOAL, Faransa 1-0 Croatia

    Antoine Griezmann ya kawo kwallo mai kyau kuma Varane ya kusa samun kwallon, amma kafinnan,Mario Mandzukic, ya tura kwallon cikin ragar kasarsa da kai.

    Wannan ya ci karo da yadda ake wasa a wannan wasan karshe na gasar kofin duniyar!

    Croa

    Asalin hoton, Reuters

  7. Wasa mafi muhimmanci a rayuwarsa, Faransa 0-0 Croatia

    Sau daya ne Antoine Griezmann ya taba kwallo cikin mintuna 12 na farko...

    Faransa

    Asalin hoton, Opta

  8. Crotai ta fara da karfinta, Faransa 0-0 Croatia

    Croatia ta fara wasan da karfinta - kawo yanzu sun fi Faransa rike kwallo a gidanta.

    Faransa

    Asalin hoton, Opta

  9. Hankalin Croatia a kwance, Faransa 0-0 Croatia

    Faransa da Croatia

    Asalin hoton, Getty Images

    Da alama hankalin Croatia na a kwance . Faransa kuma tana kokarin gano kan wasan ne tukunna.

    Croatia na amfani da 'yan wasan gefenta wajen kai wa Faransa farmaki.

  10. Ko tarihi zai maimaita kansa?, Faransa 0-0 Croatia

    Faransa ba ta taba sha kaye a wasan da aka ta fara da Pogba da Kante ba. Amma hakan zai iya faruwa a yau kuwa?

    Pogba da Kante sun sako Hazard a gaba

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Pogba da Kante sun sako Hazard a gaba
  11. Croatia na kai farmaki, Faransa 0-0 Croatia

    Croatia ta fara wasan ne da rige kwallo da kai farmaki. Shin Faransa za ta zauna a gida ne kawai ta rinka aika wa Mbappe kwallo?

  12. An fara wasa, Faransa 0-0 Croatia

    An fara wasan karshe na gasar kofin duniya ta shekarar 2018.

  13. Ba a son sa a gida?

    Modric

    Asalin hoton, Getty Images

    Luka Modric, keftin da kuma madugun tawagarsa, shi ne tauraron tawagar kwallon kafa ta Croatia.

    Ya samu kyautar gwarzon wasa a wasanni uku cikin shidan da ya buga a gasar kofin duniyar.

    Duk da cewar ya barar da fenareti a wasansu da Denmark bai damu ba. A cikin nitsuwa ya zura fenareti cikin raga a karshen wasan.

    Amma masoya kwallon kafa da yawa Croatia suna korafi game da irin rawar da dan wasan na Real Madrid ke takawa.

  14. 'Abin da ya sa Croatia ta cancanci wasan karshe'

    Croatia

    Asalin hoton, BBC Sport

    Tsohon dan wasan Ingila, Rio Ferdinand, ya ce 'yan wasan da suka hada kai a matsayin tawaga guda kuma suka fahimci abinda mai horaswarsu ke so sun taka rawar gani a wannan gasar.

    (Croatia) Sun taba yin irin haka a muhimman gasa. Shi ya sa suka samu shiga wannan wasan karshen, in ji Ferdinand.

  15. Kylian Mappe zai kafa tarihi

    Zai zam dan wasan Faransa mafi karanci shekaru da ya taba buga wasan karshe na gasar kofin duniya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Salon bai canza ba...

    Wannan shi ne wasan karshe na goma na kofin duniya (a jere) da za a samu akalla dan wasa daya daga Bayern Munich da Inter Milan a cikin masu taka leda.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Masu 'wakiltar' Madrid a wasan karshe

    Wadannan ne 'yan wasan Madrid da za su buga wa kasashe biyun da ke karawa a wasan karshe na gasar kofin duniya ta shekarar 2018.

  18. Kasashen ba su sauya 'yan wasa ba

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Kasashen biyu dai ba su sauya 'yan wasansu ba. 'Yan wasan da suka buga musu wasan da suka buga na baya bayan nan ne za su fara musu wasa.

  19. Barka da shigowa

    Jama'a, barkanku da shigowa wannan shafin inda za mu kawo muku labarai da sharhi game da wasan karshe na gasar cin kofin duniya tsakanin Faransa da Croatia.