Yadda zaben kasar Ghana ya gudana

Wannan shafin ya kawo muku bayanai da rahotani da hotuna kan yadda aka yi zaben shugaban kasa da 'yan majalisa a kasar Ghana.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An takaita zirga-zirga a baburan hawa

      • Marubuci, Yusuf Ibrahim Yakasai
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Kumasi, Ghana

    Mutane suna da damar ci gaba da harkokin su a Ghana a lokacin da ake ci gaba da zaben. To sai dai an hana yawo da babura a yau har zuwa gobe da safe

    Ghana Election

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Wasu sun sanya alama a kan layin zabe

    Tun kafin a fara zabe wasu mutanen suka saka alamar suna kan layi, domin da zarar an fara kada kuri'a su samu damar jefa ta su da wuri.

    Ghana Election
  3. , Wasu Tun a daren Talata suka fara bin layi

      • Marubuci, Yusuf Ibrahim Yakasai
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Kumasi, Ghana

    Tun tsakar daren Talata wasu mutane suka fara hawa kan layi domin su samu kada kuri'un su da wuri 

    A mafi yawan wurare dai an fara zaben a kan kari. Sai dai an samu jinkiri a wasu wurare a birnin Accra. Sai dai duk da haka an fara zaben kafin 7:30 na safe.

    Ghana Election
  4. Tun da sanyin safiya aka fara kada kuri'a

      • Marubuci, Yusuf Ibrahim Yakasai
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Kumasi, Ghana

    Tun da karfe 7:30 na safe agogon Ghana aka fara kada kuri'u a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a Ghana. 

    Za a kada kuri'n ne a mazabu dubu ashirin da takwas da dari tara da casa'in da biyu. 

    Haka kuma mutum miliyan goma sha biyar da dubu dari bakwai da uku, da dari tara da casain ne za su kada kuria a zaben na yau.

    Ghana Election
  5. An fara gudanar da zagen kasar Ghana

    An bude rumfunan zabe a Ghana, bayan da 'yan takarar shugaban kasar su bakwai suka yi kira da a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. 

    Jami'an tsaro sun tabbatar da mutuwar mutum daya dan adawa, bayan da rikici ya barke a lokacin da ake yin kamfen a ranar Talata. 

    Manyan 'yan takarar shugaban kasa sun hada da shugaba John Mahama da tsohon Firai minista Nana Akufo-Ado. 

    Ghana Election

    Asalin hoton, ap

    Bayanan hoto, Tun da karfe 7:00 na safe agogon GMT aka fara kada kuri'a a wasu wuraren
  6. Barkanmu da saduwa kan yadda za mu kawo muku zaben kasar Ghana kai tsaye