Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 29/06/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Nan za mu rufe wannan shafi na rahotonni kai-tsaye.

    Za mu kawo wasu rahotonnin gobe da safe.

  2. Yaƙi da Iran ya samar mana da damarmaki - Netanyahu

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Isra'ila ya ce yakin kasarsa da Iran ya samar da damarmaki da dama da suka haɗa da sakin ragowar 'yan kasarsa da Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.

    Amma kuma Benjamin Netanyahu ya kafe cewa har yanzu akwai bukatar samo hanyar magance rikicin na Gaza, da kuma murkushe Hamas gaba ɗaya.

    Netanyahu ya yi kalaman ne a yau Lahadi, ranar da hukumar tsaro da kai dauki a Gaza ta ce akalla mutum 23 Isra'ila ta kashe a hare-haren da take kai wa sassan zirin, kuma uku daga cikinsu kananan yara ne.

    Wakilin BBC ya ce bayan wata 21 na yaki bangarorin biyu na kira da a kawo karshen yakin.

    Rundunar sojin Isra'ila ta bayar da umarnin tashi ga mazauna unguwannin arewacin Gaza da kuma birnin na Gaza kansa, tana mai gargadin Falasdinawa cewa za ta dauki mataki na ba makawa.

  3. Gwamnan Kano ya sauya sunan kwalejin wasanni da na 'yanwasa 22 da suka mutu

    Abba Kabir

    Asalin hoton, KNSG

    Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sauya sunan kwalejin horar da harkokin wasanni ta jihar zuwa sunayen tawagar 'yanwasan Kano 22 da suka rasu a kan hanyar komawa gida daga gasar ƙasa a watan Mayun da ya wuce.

    Yayin wani biki a gidan gwamnatin jihar, Gwamna Abba ya sanar cewa daga yanzu za a dinga kiran kwalejin Kano State Sports Institute da sunan Kano State 22 Athletes Sports Institute domin tunawa da su.

    Kazalika, ita ma hukumar harkokin wasanni ta sauya suna zuwa Kano State 22 Athletes Sports Commission.

    "Waɗannan 'yanwasa sun saka Kano alfahari, ya kamata a dinga tunawa da su har abada. Ba za mu manta da sadaukarwar da suka yi wa jihar nan ba," a cewar gwamnan.

    Gwamnan ya bayar da sanarwar ne lokacin da wata tawagar wakilai ta uwargidan shugaban ƙasa Remi Tinubu ta kai ziyarar jaje, inda ta bayar da gudummawar naira miliyan 110, kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito.

  4. 'Dalilin da ya sa rabin farashin wake ya faɗi a Najeriya'

    Wake

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar manoman wake a Najeriya ta bayyana amfani mai yawa da suka samu a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da suka jawo raguwar farashinsa a kasuwanni a baya-bayan.

    Shugaan ƙungiyar ta Cowpea and Beans Farmers, Processors and Marketers Association of Nigeria (C&BFPMAN), Kabir Shuaibu ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na NAN cewa suna farin ciki da saukar farashin.

    Rahoton na NAN ya ce daga wata ukun ƙarshe na 2024, farashin babban buhun wake mai nauyin 100kg ya kai har N210,000 zuwa N240,000, a madadin N90,000 da aka dinga sayar da shi a 2023.

    Sai dai kuma, daga wata ukun farko na 2025 zuwa yanzu farashin ya sauka sosai zuwa N80,000 ko N120,000 - ya danganta da nau'insa.

    "Muna farin ciki da saukar farashin waken. Mun samu ninki 10 na abin da muka saba samu a shekarun baya," kamar yadda Kabiru ya shaida wa NAN.

  5. Gwamnatin Nijar ta kafa majalisar tuntuɓa

    Nijar

    Asalin hoton, ORTN

    Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta kafa majalisar tuntuɓa ta wucin-gadi, wadda aka fi sani da majalisar tuntuɓa ta Consultative Council of the Re-foundation ko kuma CCR a taƙaice.

    Kafar yaɗa labarai da ActuNiger mai zaman kanta ta ruwaito cewa hukumomin ƙasar ne suka zaɓa tare da naɗa ƴanmajalisar, kuma an kafa ta ne bisa shawarar taron tuntuɓa da aka yi a ƙasar a watan Fabrairu.

    A taron ne dai aka amince da tsawaita mulkin sojin da shekara biyar zuwa 10.

    "A majalisar akwai wakilai 194 da suke wakiltar ƙungiyoyi da dama, da matasa, da sarakuna, da mata, da jami'o'i, da mazauna ƙasashen waje, da sauransu," kamar yadda rahoton ya bayyana.

    "Manufar majalisar ita ce ba wa gwamnatin shawara kan harkokin gwamnati da ciyar da ƙasar gaba, a gefe guda kuma suna tsare-tsaren tabbatar da dimokuraɗiyya."

    Nijar da maƙwabtanta - Mali da Burkina Faso - duk suna ƙarƙashin mulkin soji ne, kuma alamu na nuna akwia sauran lokacin kafin komawarsu mulkin dimuraɗiyya.

  6. Sojojin Mali sun kashe 'jagoran mayaƙa' da ya shiga ƙasar

    Mali

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin ƙasan Mali ta sanar da samun nasarar kashe wani wanda ta kira 'jagoran mayaƙa' da ta ce ɗan ƙungiyar IS da ya shiga ƙasarta domin jan hankalin mutane ta hanyar amfani da farfaganda.

    Rundunar ta ce ta kashe shi ne tare da wasu mayaƙa guda biyar a wani samame da ta kai a arewacin Menaka, kamar yadda kafar gwamnatin ƙasar, ORTM ta ruwaito.

    ORTM ta ce sojojin ƙasar sun samu bayanan sirri ne kan shigar mutumin ta yankin Chamane, gari mai nisan tafiyar kilomita 38 daga garin Menaka, inda ya fara tattara mazauna yankunan yana yaɗa bayanan farfaganda domin jan hankalinsu game da harkokinsu.

    "Mutumin ya fara jan hankalin mazauna yankin domin taimaka masa wajen yaɗa farfaganda," in ji rahoton ORTM.

    A nasu bayaninsu, rundunar sojin haya ta Rasha ta ce sunan mutumin Abu Dahbab, kuma masanin dasa nakiyoyi ne da farfaganda, sannan ta yaba wa dakarunta bisa ƙoƙarin da suka tare da sojojin ƙasar wajen daƙile yunƙurin 'baƙon hauren."

  7. Ba mu da hannu a harin ƙunar baƙin waken Pakistan - Indiya

    Indiya cikin fushi ta yi watsi da sanarwar da runduanr sojin Pakistan ta yi cewa harin ƙunar baƙin waken da ya kashe sojojin Pakistan aƙalla goma sha uku jiya Asabar, mayaƙa da ke samun goyon bayan Delhi ne suka ƙaddamar da shi.

    Jami'ai sun ce ɗan ƙunar bakin waken ya tuƙa wata mota maƙare da abubuwan fashewa inda ya yi kan jerin gwanon motocin sojoji a yankin arewacin Waziristan kusa da iyakar ƙasar da Afghanistan.

    Ɗaya ne daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai a kan iyaka a watannin baya-bayan nan.

    A bana, hare-haren ƴanbindiga sun ƙaru inda ƙwararru a fannin tsaro ke cewa ƙungiyoyi masu da'awar Jihadi na ƙara ƙarfi a ƙarƙashin mulkin Taliban a Afghanistan.

  8. Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 38 a Tanzania

    Tanzania

    Asalin hoton, Mwananchi

    Aƙalla mutum 38 ne suka rasu, sannan wasu 28 suka jikkata bayan wani hatsarin mota, inda motoci biyu suka ƙone bayan sun yi taho mu gama a arewacin Kilimanjaro a Tanzania.

    Kwamishinan yankin Kilimanjaro, Nurdin Babu ya ce hatsarin ya auku ne da yammacin ranar Asabar a lardin Same bayan tayar ɗaya daga cikin motocin ya fashe, suka haɗe, sannan wuta ta tashi.

    Mutum 22 daga cikin 28 da suka jikkata sun samu sauƙi har an sallame su daga asibiti, amma akwai guda shida da suke cigaba da jinya.

    Shugaban ƙasar Samia Suluhu ta nuna rashin jin daɗinta kan yawaitar hatsari a ƙasar, inda ta ce alƙaluman hatsarin suna ɗaga hankali.

    Daga watan Janairu zuwa watan Afrilu, an yi hatsari 1,322 a ƙasar, inda mutum 1,275 suka mutu, wanda ƙari ne a kan irin wa'adin nan a bara da kashi tara.

    A ranar 8 ga watan Yuni, mutum 28 suka rasu a babbar hanyar Tanzania-Zambia da ke kudancin yankin Mbeya lokacin da wata babbar motar ɗaukar kaya ta ƙwace, ta buga da ƙananan motoci biyu.

  9. Gobe Litinin za a yi jana'izar Ɗantata a Madina

    Dantata

    Asalin hoton, Sanusi Dantata

    Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid ya ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana'iza tare da binne gawar marigayin a garin Madina.

    Mustapha ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta cewa, "Alhamdulillah an samu amincewar (hukumomi), za a ɗauki Aminu Alhassan Ɗantata daga Abu Dhabi zuwa Madina. Za a yi jana'iza gobe da safe in sha Allah."

    A safiyar jiya Asabar ne da attajirin ɗankasuwar ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, amma iyalansa suka jinkirta binne shi domin a cewarsu, suna su ne su cika masa burinsa na kasancewar a binne a garin na Madina.

    An dai gudanar masa da sallar da gawa ba ta kusa a jihar Kano, wanda Sheikh Ibrahim Khalil ya jagoranta.

  10. Babu wanda zai shafe gudunmuwar da Wike ya ba ni - Fubara

    Rivers

    Asalin hoton, Rivers State Government Press

    Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ce babu wata sadaukarwa da ba zai yi ba, matuƙar za ta zama sanadiyar samar da zaman lafiya da ci gaba jihar.

    Fubara, ya bayyana haka ne a Fatakwal a ranar Asabar lokacin da yake yi wa magoya bayansa jawabi, inda ya nanata musu cewa lallai sun sasanta da Ministan Abuja Nyesom Wike.

    Ya ce ya san akwai wasu masoyansa da ba za su ji daɗin sasancin ba, sai ya ce su yi haƙuri domin, "wasu lokutan dole a ɗauki matakan da ba za a ji daɗinsu ba domin gyara," in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    "Kowa ya san mun iya bakin ƙoƙarinmu, mun duk abin da ya kamata. Amma yanzu maganar gaskiya babu abin da muke buƙata sai zaman lafiya."

    "Babu wanda zai shafe irin gudunmuwar da Ministan Abuja Nyesom Wike ya ba ni. Lallai mun samu saɓani a kan wasu abubuwa, amma babu wanda zai ce bai irin rawar da mutumin nan ya taka ba, da irin ƙalubalen da ya fuskanta. Don haka duk wanda yake ƙaunata da gaskiya ya ajiye karinsa, yanzu lokaci ne na neman zaman lafiya."

  11. Shugaban Serbia ya zargi masu zanga-zanga da yunƙurin kifar da gwamnati

    Serbia

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban masu zanga-zanga ne suka hallara a Belgrade, babban birnin Serbia jiya Asabar inda suke neman a matso da lokacin zaɓe gaba tare da kawo ƙarshen gwamnatin Shugaba Aleksandar Vucic.

    A ɗaya daga cikin manyan gangamin da aka yi na tsawon watanni ana zanga-zangar ƙarƙashin jagorancin ɗalibai, dandazon al'umma sun cika wani dandali da tituna maƙil.

    Wasu sun yi arangama da ƴansandar kwantar da tarzoma a lokacin da suke tsaka da gudanar da zanga-zangar, wadda suka ce ta lumana ce.

    Shi dai Shugaba Vucic ya zarge su da ƙoƙarin kifar da gwamnati.

    Magoya bayan shugaban ƙasar suma sun taru domin gudanar da tasu zanga-zangar a kusa da majalisar dokokin ƙasar.

    Ɗaliban dai sun zargi shugaban ƙasar Serbia da makusantansa da tafka rashawa da kuma tauye ƴancin kafafen yaɗa labarai.

  12. Dokokin taƙaita shan sigari na Faransa sun fara aiki

    Faransa

    Asalin hoton, EPA

    A yau ne sabbin dokokin hana shan taba a bakin teku da wuraren shaƙatawa da kusa da tashoshin bas da makarantu za su fara aiki a Faransa.

    Masu goyon bayan matakin sun ce hakan zai kare ƙananan yara daga illolin da ke tattare da shaƙar hayaƙin taba sigari.

    Sai dai har yanzu akwai izinin mutum ya zuƙi taba a wuraren cin abinci da kuma mashaya.

    Masu fafutukar yaƙi da shan taba sun ce ba su ji daɗin yadda matakin bai haɗa da tabar laturoni ba.

  13. Akume bai ajiye muƙamin sakataren gwamnati ba - Fadar shugaban Najeriya

    George Akume

    Asalin hoton, Senator George Akume

    Fadar shugaban Najeriy ta ƙaryata labarin da ake yaɗawa cewa tsohon gwamnan jihar Benue, George Akume ya ajiye muƙaminsa na sakataren gwamnatin tarayya.

    Jim bayan da aka tabbatar da ajiye muƙamin shugaban jam'iyyar APC mai mulki a ƙasar da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi ne aka fara yaɗa raɗe-raɗin cewa Akume ma ya ajiye muƙaminsa, inda wasu suka fara yaɗa jita-jitar shi ne zai zama shugaban jam'iyyar.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce labari ne na ƙanzon kurege, domin "babu abin da ya canja.

    "Shugaba Tinubu yanzu haka yana Saint Lucia, kuma babu wani naɗi sabo da ya yi. Labarin da ake yaɗawa na canja Akume ba gaskiya ba ne."

  14. Trump ya miƙa ƙudurin haraji da rage kashe kuɗaɗe mai shafi 900 ga majalisar ƙasar

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dokokin Amurka ta kaɗa ƙuri'ar tafka muhawara kan ƙudirin shugaba Trump kan haraji da kuma kashe kuɗaɗen gwamnati.

    An dai shafe tsawon sa'a uku ana kaɗa ƙuri'a kan batun, saboda daftarin ƙudirin da shugaba Trump ɗin ya gabatar wa majalisar, ya kai fiye da shafuka 900.

    A cewar wakiliyar BBC, ƙudirin na neman a rage yawan kuɗaɗe kan wasu shirye-shiryen muhalli da na kula da lafiyar al'umma.

    Ƙudirin ya ƙunshi sa takunkumi kan ɗaya daga cikin manyan hanyoyin kashe kuɗaɗe na tarayya wato Medicaid wanda shirin kiwon lafiya ne da miliyoyin Amurkawa suka dogara da shi.

    Ƙudirin zai kuma ƙara yawan kuɗaɗen da ake kashewa don tabbatar da tsaro a iyakoki da biliyoyin dala tare da tsawaita matakin rage haraji da ƴan demokrats suka ce ya fi fifita masu arziki.

  15. Iran za ta iya gyara cibiyoyin nukiliyarta cikin watanni - IAEA

    Nukiliya

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban hukumar kula da nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce Iran tana da ikon ta sake fara inganta sinadarin uranium cikin ƴan watanni.

    Da yake magana da kafar yaɗa labarai ta CBS, Rafael Grossi ya ce harin da Amurka ta kai Iran a ƙarshen makon da ya gabata ya yi gagarumar ɓarna amma bai lalata gaba ɗaya tashohin nukiliyar ba.

    Grossi ya ƙara da cewa Iran ƙasa ce mai matuƙar ƙwarewa da tarin ƙwararru idan aka zo ga batun fasahar nukiliya, lamarin da ya ce a bayyane yake.

    Kalamansa sun yi hannun riga da iƙirarin Fadar White House cewa shirin nukiliyar Iran ya fuskanci koma-baya.

    Iran dai ta yi watsi da buƙatar hukumar na ta duba wuraren da aka kai wa harin.

  16. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu cigaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zamunta irin su Facebook da X da Instagram da ma zaurenmu na Whattsapp domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.