An ba Chelsea damar sayen Martinez, za a duba lafiyar Quansah a Leverkusen

Asalin hoton, Getty Images
An bai wa Chelsea damar ta ɗauko ɗanwasan Aston Villa Emiliano Martinez kan fam miliyan 45 duk da cewa ana tunanin golan na Argentina ɗan shekara 32 zai fi karkata ga komawa Manchester United. (Mirror)
Manchester United ta shirya fara tattaunawa kan yarjejeniyar sayen Martinez idan suka cefanar da golan Kamaru Andre Onana mai shekara 29. (Football Insider)
Za a duba lafiyar ɗanwasan Liverpool mai shekara 22 Jarell Quansah a Bayer Leverkusen ranar Litinin kafin sayen shi kan fam miliyan 35. (Fabrizio Romano)
Liverpool ta kusa daidaitawa kan sayen ɗanwasan Crystal Palace mai shekara 24 Marc Guehi. (Mirror)
Darwin Nunez ta shirya komawa Napoli a bazara sai dai kulob ɗin na Italiya ba su shirya da farashin fam miliyan 70 da Liverpool ta yi wa ɗanwasan na ƙasar Uruguay mai shekara 26 ba. (Mirror)
Wataƙila sai Manchester United ta biya ƴanwasanta su bar ƙungiyar a wannan bazara saboda tsadar kwantiraginsu mai tsawo, yayin da ɗanwasa Marcus Rashford mai shekara 27 da takwaransa Alejandro Garnacho mai shekara 20 ke cikin ƴan wasan da kulob ɗin ke son cefanarwa. (Telegraph - subscription required)
Sunderland ta amince ta biya Strasbourg fam miliyan 30 kan ɗanwasan Habib Diarra mai shekara 21 wanda ɗan asalin Senegal ne. (Guardian)
Nottingham Forest ta yi tayin fam miliyan 5 kan ɗanwasan Real Mallorca Pablo Maffeo mai shekara 27. (El Chiringuito - in Spanish)
Newcastle da Burnley sun kasa daidaitawa kan farashin James Traffordyayin da aka yi fatali da tayin da Magpies ta yi tun asali na fam miliyan 25 kan ɗanwasan Ingilan mai shekara 22. (Sky Sports)
Crystal Palace ta shirya gogayya da Newcastle da Liverpool da Tottenham a zawarcin ɗanwasan Southampton mai shekara 19 Tyler Dibling a wannan bazarar. (Football Insider)
Nico Williams ya shaida wa Barcelona cewa yana son ya koma ƙungiyar daga Athletic Bilbao sai dai ɗanwasan na Sifaniya mai shekara 22 ya nemi a yi masa rajistar buga wasa wanda hakan na iya nufin sai Barca ta fara cefanar da ƴan wasanta don ta iya biyan buƙatun La Liga. (Marca - in Spanish)
Tuni Al-Nassr ta ƙulla yarjejeniyar tura ɗanwasanta Jhon Duran mai shekara 21 zaman aro a Fenerbahce. (Foot Mercato - in French)












