Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 03/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya kai tsaye - Lahadi - 03/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Sabbin hare-hare Isra'ila sun kashe mutum 30 a Gaza

    Jami'an Lafiyar Falasɗinawa a Gaza sun ce aƙalla mutum 30 aka kashe a wasu sabbin hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai, yayin da aka kashe rabin wannan adadi a arewacin yankin da aka yi wa ƙawanya.

    Jami'an sun ce kimanin mutum 13 aka kashe a Beit Lahiya da Jabalia - Harin shi ne mafi muni da Isra'ila ta kai tun bayan zafafa hare-haren da ta fara a farkon watan Oktoba.

    Tun da farko, wani hari da aka kai yankin Khan Younis ya kashe mutum takwas ciki har da ƙananan yara huɗu.

    Hare-haren na baya-bayan nan na zuwa ne, yayin Unicef ke alla wadai da kisan ƙananan yara 50 a cikin kwana biyu a Jabalia.

    Isra'ila ta ce tana kai hare-hare yankin arewacin Gaza ne domin hana ƙungiyar Hamas sake farfaɗowa.

  3. Chadi ta yi barazanar fita daga ƙawancen sojin mai yaƙi da Boko Haram a Tafkin Chadi

    Muhammat Deby

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno ya ya yi barazanar janye dakarun ƙasarsa daga cikin ƙawancen soji na MNJTF mai yaƙi da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi bayan harin Boko Haram na baya-bayan nan kan sojojin ƙasarsa.

    Cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin ƙasar ta fitar - wadda Jaridar PRNigeria ta samu kwafinsa - shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ganin yadda dakarun ƙasarsa ke aiki a kan iyakar ƙasar.

    Hakan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan wani mummunan hari da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai wa sansanin sojojin ƙasar da ke Barkaram ranar 27 ga watan Oktoba.

    Harin ya yi sanadin mutuwar sojojin ƙasar da dama, lamarin da ya janyo hankali shugaban ƙasar, har yake maida irin wannan martani.

    Sanarwar fadar gwamnatin - mai ɗauke da sa hannun, daraktan sadarwa na ofishin shugaban ƙasar, Hassan Abdelkerim Bouyëbri - ta ambato shugaban ƙasar na cewa zai janye dakarun ƙaar daga ƙawancen MNJTF, saboda abin da ya kira ''rashin haɗin kai tsakanin dakarun ƙawancen wajen yaƙi da Boko Haram''.

  4. 'Yansandan Najeriya sun kama 'yan ƙasar waje 113 bisa zargin laifukan intanet.

    masu laifi

    Asalin hoton, EFCC

    Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce ta kama wasu mutum 130 bisa zargin laifukan da suka shafi laifukan intanet.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce daga cikin mutanen da ta kama, mutum 113 'yan ƙasashen China da Malaysia ne.

    Sanarwar ta ƙara da cewa an kama mutanen - ciki har da 'yan Najeriya 17 - a wani gini da ke unguwar Jahi a Abuja, babban birnin ƙasar.

    ''Mutanen na amfani da kwamfutoci da wasu na'urori wajen aikata laifukan'', in ji sanarwar.

    'Yansanda sun kuma ce suna gudanar da bincike game da mutanen, tare da yi zuzzurfan nazari kan abubuwan da aka ƙwato a wajensu, kafin a gabatar da su a gaban kotu.

  5. Ɓaraka ta kunno kai a Kwankwasiyya

    ..

    Babbar ɓaraka ta kunno kai a tafiyar siyasar Kwankwasiyya ta jam'iyyar NNPP, yayin da 'yan majalisar tarayya biyu a jihar suka sanar da ficewa daga tafiyar.

    Mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya, Ali Sani Madakin Gini ya tabbatarwa da BBC cewa ya fita daga tsagin Kwankwasiyya a cikin jam'iyyarsa ta NNPP.

    Ɗan majalisar mai wakiltar Dala a tsakiyar birnin Kano ya tabbatar da haka ne bayan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta wanda a ciki aka ji yana cewa "Daga yau, na daina harkar Kwankwasiyya".

    A cikin bidiyon Ali Madakin Gini ya bayyana cewa "Kwankwasiyya ƙarya ce, Kwankwasiyya yaudara ce".

    Ya ƙara tabbatarwa da BBC cewa: "Na fahimci cewa an gina tafiyar Kwankwasiyya ce kawai domin ci gaban Kwankwaso".

    Haka shi ma takwaransa da ke wakiltar ƙananan hukumomin Kibiya da Rano da kuma Bunkure, Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya sanar da raba gari da tafiyar ta kwankwasiyya.

    A zantawarsa da BBC, Hon. Rurum ya ce ya fice daga tafiyar ne sakamakon ''rashin adalci'' daga ɓangaren uban tafiyar, Rabi'u Kwankwaso.

    Zuwa yanzu dai ba a ji wani martani daga ɓangaren Sanata Kwankwaso ba a kan wannan ikirari.

    Duka 'yan majalisar biyu sun bayyana cewa har yanzu sunan nan a jam'iyyarsu ta NNPP, amma ba tsagin jagorancin Sanata Rabi'u Kwankwaso ba.

    Matakin na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano, wanda jam'iyyar NNPP ta lashe dukkan kujerun.

    'Yan majalisun biyu - Ali Madakin Gini, da Kabiru Alhassan Rurum - sun yaba wa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da cewa shi mutumin kirki don haka suka shawarce shi da ya yi duk yadda zai yi, ya ''tsaya da ƙafarsa''.

    A kwanan baya ne dai wata ƙungiya ta ɓullo a fagen siyasar Kano mai taken 'Abba Tsaya da Ƙafarka' mai rajin gwamnan na Kano ya daina biyayya ga jagoran Kwankwasiyya, ya ci gashin kansa, lamarin da ya janyo jam'iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Kano da wani kwamishina, bisa zarginsu da alaƙa da ƙungiyar.

  6. RSF sun kashe mutum 13 a wani sabon hari kan fararen hula a Sudan

    Aƙalla mutum 13 ne suka mutu a wani hari da da ake zargin dakarun RSF ne suka kai a kudancin birnin Khartoum na ƙasar Sudan.

    An yi zargin cewa mayaƙan ƙungiyar sun buɗe wuta kan fararen hula a garin Al Hilaliya da ke jihar Al Jazeera, da ke kudancin Khartoum.

    An samu rahotonnin sace kayyaki da cinna wa gidaje wuta. An dai ɗauki fiye da shekara guda ana gwambza yaƙi tsakanin RSF da sojojin ƙasar.

    Yaƙin ya jefa ƙasar cikin mawuyacin halin buƙatar jin ƙai, yayin da fiye da mutum miliyan 11 suka rasa muhallansu.

  7. MDD ta yi gargaɗin samun matsananciyar yunwa a Najeriya a 2025

    Abinci

    Asalin hoton, WFP

    Ofishin Majalisar Dinkin Duniya, mai lura da al'amuran jin ƙai ya yi hasashen samun matsananciyar yunwa a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka.

    Cikin wani saƙo da ofishin ya wallafa a shafinsa na X, ya yi gargaɗin samun tsanantar matsalar a Najeriya tsakanin watan Nuwamban 2024 zuwa watan Mayun 2025.

    ''Ya kamata a ɗauki matakai domin yaƙi da yunwa da ceto rayukan mutane a yanzu da kuma tsawon lokaci a nan gaba'', kamar yadda ofishin ya wallafa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Bayanan da ofishin ya fitar sun nuna cewa a NAjeriya, mutum miliyan 38 ne za su fuskanci matsalar, yayin da ƙasar Sudan ta Kudu ke biye mata da mutum miliyan 21, sai ƙasar Ethiopia mai mutum miliyan 15.

    A farkon wannan shekarar ne dai gwamnatin Najeriya ta sanar da wasu matakai uku na kawo sauƙi ga matsalar ƙarancin abinci a ƙasar.

    Ɗaya daga cikin matakan shi ne, gwamnatin ta fito da tan 42,000 na abinci daga rumbunan ma'aikatar harkokin noma da nufin kawo sauƙi ga al'ummar ƙasar.

    Haka kuma gwamnatin ta ce idan har matsalar ta faskara za ta iya ɗaukar matakin shigar da abinci daga ƙasashen waje domin magance tsadar abinci a faɗin ƙasar.

  8. Jam'iyyar Labour mai mulkin Abia ta kasa cin ko ƙaramar hukuma ɗaya a jihar

    Gwamna Alex Otti da tambarin jam'iyyarsa ta Labour

    Asalin hoton, Alex Otti/Labour Party

    Jam'iyyar Labour da ke mulkin jihar Abia ta kasa cin ko da ɗaya daga ƙananan hukumomin jihar 17 a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a jiya Asabar.

    A maimakon haka jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP), ce ta cinye yawancin ƙananan hukumomin inda ta samu 15 daga cikin 17.

    Jam'iyyar Young Progressives Party (YPP) ce ta ci ragowar ƙananan hukumomin biyu - ƙaramar hukumar Ugwunagbo da kuma Osisioma Ngwa.

    Shugaban hukumar zaɓen jihar, (ABSIEC), George Chima, shi ne ya bayyana sakamakon a ofishin hukumar da ke babban birnin jihar, Umuahia, a jiya Asabar.

    Mista Chima, ya bayyana gamsuwarsa da yadda zaɓen da ya ce sama da jam'iyyu 12 suka shiga, ya gudana.

    Sakamakon rigimar da ake yi ta shugabancin jam'iyyar Labour a tarayya, 'yantakarar da ake gani suna da goyon bayan gwamnan jihar Alex Otti, sun tsaya takara ne a jam'iyyar Zenith Labour Party, wadda ta ci kujeru 15 ɗin.

    Shugabancin jam'iyyar Labour na ƙasa na fama da rikici inda ake da ɓangare biyu, na tsohuwar ministar kuɗi Sanata Nenadi Usman, da Gwamna Otti ke bi, da kuma ɓangaren Julius Abure.

  9. Jihohin da Harris da Trump ke buƙata kafin su ci zaɓe

    Harris da Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Akwai jihohi 50 a Amurka kuma yawancinsu akwai inda suke karkata wajen zaɓe a al'ada - ko dai su zaɓi jam'iyyar Democrat ko kuma Republican a duk zaɓe.

    Wannan ya rage 'yan jihohi kaɗan ke nan da ɗan takara zai iya ci - kuma a wannan zaɓen akwai jihohi bakwai da suke hakan.

    Waɗannan jihohi su ne ake kira waɗanda ba-a-san-maci-tuwo-ba... jihohin sun kasu kashi biyu - Nevada, da Arizona, da North Carolina, da Georgia. Sai kuma ɗaya rukunin da ya ƙunshi ; Wisconsin, da Michigan, da kuma Pennsylvania.

    A faɗin Amurka gaba ɗaya akwai jimillar irin waɗannan kuri'u na wakilan masu zaɓe (electoral college)' 538 da ɗantakara zai ci, kuma ɗantakarar da ya samu 270 ko sama da haka shi ne zai ci zaɓen shugaban ƙasar.

    A dukkanin jihohin in bayan jihohi biyu, ɗantakarar shugaban ƙasar da ya samu ƙuri'un jama'a mafiya yawa zai ci dukkanin ƙuri'un wakilan masu zaɓe na jihar.

    Kowanne daga cikin ƴantakarar na buƙatar ya ci aƙalla jihohi uku na ba-a-san-maci-tuwo-ba ya yi nasara.

  10. Hare-haren sama da Rasha ta kai Kyiv sun yi ɓarna a birnin - Ukraine

    Hari a Kyiv

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Ukraine ta ce wani harin sama da Rasha ta kai da daddare kan babban birnin ƙasar, Kyiv, ya lalata gine-gine da tituna da layukan lantarki.

    Sojojin sun kuma ce wasu rahotanni da aka bayar tun da farko na wata wuta da ta tashi ba su illata kowa ba.

    Ana ta ankarar da jama'a a yawancin sassan gabashin ƙasar ta Ukraine saboda hare-haren da Rasha ke kaiwa tun daren Asabar.

    Shugaba Zelensky ya faɗa a shafukan sada zumunta da muhawara cewa sannu a hankali yanzu Rasha na amfani da jirage marassa matuƙa ƙirar Iran, samfurin Shahed da kuma makamai masu linzami.

    Ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce garkuwarta ta sama ta yi nasarar tare hare-haren jirage marassa matuƙa har goma sha tara a cikin dare, waɗanda ta hari kudu maso yammacin ƙasar.

  11. Zaɓen Amurka: Wuraren da 'yan takara za su ƙarƙare yaƙin neman zaɓen a yau Lahadi

    Yayin da ake dab da ƙarƙare yaƙin neman zaɓen Amurka a yau Lahadi, duka jam'iyyun biyu za su ƙarƙare yaƙin neman zaɓe a jihohi marasa tabbas. Ga abin da muke sa ran gani a yau.

    • Ɗan takarar jam'iyyar Republican,Donald Trump zai halarci gangami a jihohin Pennsylvania da North Carolina da kuma Georgia.
    • Ita kuwa takwararsa ta jam'iyyar Democratic, Kamala Harris za ta gudanar da nata gangamin a jihar Michigan, da kuma yaƙin neman zaɓe a jihar Pennsylvania.
    • Haka kuma, mai ɗakin shugaban ƙasar, Jill Biden za ta fito yaƙin neman zaɓe a jihar Pennsylvania, yayin da ake sa ran tsohon shugaban ƙasar, Bill Clinton ya bayyana a gangamin jihar Georgia.
    • Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Republican, JD Vance zai gabatar da nasa gangamin a jihohin Florida da Pennsylvania da kuma New Hampshire.
  12. Birnin Bangkok ya ɓullo da tara da ɗauri ga masu kyanwa da karnukan da ke damun jama'a

    Karnuka a titi

    Hukumomin babban birnin Thailand, Bangkok sun ɓullo da sababbin dokoki domin taƙaita mallakar karnuka da kyanwa.

    Daga yanzu ba za a bar mutum ya mallaki kare ko kyanwa ba sai a duba girman gidansa ya isa ya yi hakan, sannan kuma za a maƙala wa dabbobin 'yar mitsitsiyar na'ura a jikinsu ta sadarwa domin sanin duk wani abu dangane da su.

    Duk karen da aka samu ya ciji wani mutum ko yana haushin da yake damun jama'a, to za a ci tarar mai shi abin da ya kai har dala 300 da kuma zaman gidan yari na wata ɗaya.

    An yi ƙiyasin akwai karnuka wajen dubu hamsin a Birnin na Bangkok, da kuma wasu dubu tara da suke gararamba a titi babu masu su.

    Sashen kula da dabbobi na tafi-da-gidanka zai riƙa dandaƙe, ko fiɗiye duk dabbar da aka samu babu mai ita.

  13. Tsawa ta hallaka yara 14 da jikkata 34 a Uganda

    Hoton walkiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Yara aƙalla goma sha hudu ne suka mutu a arewacin ƙasar Uganda bayan da tsawa ta faɗa musu.

    Ƴansanda sun ce akwai kuma wasu yaran talatin da huɗu da ta ji wa rauni, inda bakwai daga cikinsu suke cikin mawuyacin hali a asibiti.

    Lamarin ya faru ne a jiya Asabar da yamma a lokacin ibada a sansanin 'yan gudun hijira na Palabek a gundumar Lamwo.

    Sansanin na ɗauke da 'yan gudun hijira na Sudan ta Kudu kusan dubu talatin da shida.

    A kwanan nan an riƙa yin mamakon ruwan sama da tsawa da walkiya sosai a yankin.

  14. Ƙungiyar Afenifere ta soki Tinubu kan fifita Yarabawa a muƙamai

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, BOLA AHMED TINUBU/FACEBOOK

    Ƙungiyar kishin ƙabilar Yarabawa zalla ta Afenifere ta gargaɗi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan abin da ta kira sonkai da fifita 'yan ƙabilar Yarabawa wajen bayar da muƙaman tarayya.

    Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Ayo Adebanjo, da kuma sakatarenta na yaɗa labarai Justice Faleye suka fitar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

    Ƙngiyar ta yi gargaɗin cewa lamarin zai iya zama barazana ga alaƙar ƙabilu da kuma zaman tare na lumana a tsakanin ƙabilun ƙasar.

    Afeniferen ta kuma jaddada buƙatar gann shugaban ya gyara kuskuren da ta tace ya yi a kan bayar da muƙaman.

    A sanarwar ƙungiyar ta ce ba za ta taɓa lamunta da tsabar sonkai da nuna bambanci da Tinubu yake yi ba inda ya naɗa Yarabawa shugabannin dukkanin hukumomin yaƙi da miyagun laifuka da kuma tattalin arziƙi ba.

    Afeniferen ta ce ba ta yadda za ta yi shekara da shekaru tana yaƙar abin da ta kira kaka-gida na mulkin Fulani, sannan kuma yanzu ta goyi bayan kaka-gida na Yarabawa ko wata ƙabila ba.

  15. Magoya bayan tsohon shugaban Bolivia Morales sun yi garkuwa da sojoji in ji gwamnati

    Rikici a Bolivia

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar harkokin wajen Bolivia ta ce magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Evo Morales na riƙe da aƙalla sojoji 200.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ta ce an kai wa wasu sansanonin rundunar sojin ƙasar uku hari a lardin Chapare da ke tsakiyar ƙasar shekaran jiya Juma'a.

    Gwamnati ta ce maharan sun kuma kwasi makamai da alburusai.

    Yankin dai na da ɗimbin magoya bayan Mista Morales, wanda ya taɓa zama abokin shugaba mai ci yanzu, Luis Arce, amma yanzu ya koma abokin hamayya.

    Magoya bayan na Morales na neman lallai lallai a kawo ƙarshen binciken da ake masa kan zargin cin zarafin wata yarinya ‘yar shekara goma sha shida, da kuma safarar mutane, zarge-zargen da ya musanta.

  16. Ana tura ƙarin sojoji da 'yan sanda yankin Valencia da ambaliya ta shafa a Sifaniya

    Sojoji sun ceto wata mata

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙarin sojoji da 'yan sanda na ci gaba da isa yankin Valencia da ambaliyar ruwa ta shafa a Sifaniya.

    Jami'an wani ɓangare ne daga cikin dubu 10, da Firaministan ƙasar Pedro Sanchez ya yi alƙawarin aikawa don taimakawa.

    Wannan ne aikin soji mafi girma a lokacin zaman lafiya a tarihin Sifaniya kuma hakan ta faru ne sakamakon yadda wasu shugabannin al'umma ke sukar mahukunta kan jinkirin da ake samu a aikin ceto.

    Ambaliyar wadda ita ce mafi muni da aka yi a ƙasar cikin shekaru da dama ta bar yankunan gaba daya cikin laka tare da cika da motoci da tarkace.

    Ta kuma janyo mutuwar sama da mutane 200.

    Masu aikin ceto na ci gaba da kurɗawa wuraren ajiye motoci na ƙarƙashin ƙasa da ma gidaje don ceto waɗanda suka tsira da kuma kwaso gawarwaki.

  17. Ana zaɓen shugaban ƙasa a Moldova tsakanin ra'ayin Turai da na Rasha

    Shugaba Maia Sandu na kaɗa ƙuri'a

    Asalin hoton, DANIEL MIHAILESCU/AFP

    Jama'a a Moldova na shirin fita rumfunan zaɓe don kaɗa ƙuri'a a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar, yayin da makomarta ke cikin halin ƙila-wa-ƙala.

    Shugaba Maia Sandu wadda ke son kusanci da Turai tana takara da Aleksandr Stoia-noglo, wanda ke samun goyon bayan jam'iyyar gurguzu ta Rasha.

    Ƙuri'ar raba gardama makwanni biyu da suka gabata ta goyi bayan yin sauyi ga kundin tsarin mulkin ƙasar wanda ya haɗa da fatan shiga ƙungiyar Tarayyar Turai.

    Sakamakon ya bayar da mamaki saboda yadda aka yi kan-kan-kan, lamarin da ya haifar da zargin cewa Rasha ta yi kutse a zaɓen.

  18. An kai hari asibitin da ake rigakafin shan-inna a Gaza

    Ana yi wa yaro ɗigon polio

    Asalin hoton, EPA

    An kai hari kan wani asibitin allurar rigakafin cutar shan inna ta Polio a arewacin Gaza a ranar da aka sake fara aikin rigakafin a can.

    Mutane 6 ne suka jikkata, hudu daga cikinsu yara ne.

    Jami'an Falasdinawa sun yi zargin cewa jirgin saman Isra'ila maras matuki ne ya kai harin, amma Isra'ila ta musanta hakan.

    Hukumar kula da ƙananan yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ta bukaci Isra'ila da ta gudanar da bincike na gaggawa kan wani hari na daban da aka kai kan wata mota da ke ɗauke da ɗaya daga cikin ma'aikatanta da ke aikin rigakafin a jiya Asabar.

  19. Zaɓen Amurka: Trump da Harris na kammala yaƙin neman zaɓe

    Harris da Trump

    Kamala Harris ta ƙarƙare yaƙin neman zaɓenta, inda ta bayyana a wani shirin barkwanci na talabijin da ake kira Saturday Night Live wato SNL a takaice.

    Tare da mai kwaikwayonta Maya Rudolph, mataimakiyar shugaban Amurkar ta yi ta bada dariya sa'ad da take bada labarin wasu abubuwa da suka faru a rayuwarta.

    Musamman ta yi kafa da kada zuwa birnin New York don shiga shirin, yayin da abokin hamayyarta Donald Trump wanda ya taba bayyana a shirin tun takararsa ta farko a 2016, ke yaƙin neman zaɓe a jihar North Carolina da Virginia.

    Trump ya bayyana wa magoya bayansa cewa ranar Talatar nan da za a yi zaɓe, za ta kasance ranar ƙwatar yanci, inda ya ce shi ne zai lashe zaɓen.

  20. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Lahadi 03/10/2024.

    Ni, Muhammad Annur Muhammad da Abdullahi Bello za mu kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba.

    A yi jimirin kasancewa da mu.

    Mu fara da wannan karin maganar - Babban goro sai magogin ƙarfe