Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/10/20224

Wannan shafi ne da kawo maku rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/10/20224

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Nabeela Mukhtar da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Najeriya ta yi asarar abincin da zai ciyar da mutum miliyan takwas a 2024 - FAO

    Hukumar abinci da bunƙasa aikin noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Najeriya ta tafka asarar tan 55,629 na abinci saboda ambaliyar ruwa a 2024.

    Ƙididdigar da hukumar ta fitar ta nuna cewa asarar kayan abinci da aka tafka a Najeriya a bana ta isa a ciyar da mutum miyan takwas da rabi har tsawo wata shida.

    Mataimakin shugaban hukumar a Najeriya, Salisu Mohammed, ya ce ɗumamar yanayi da hauhawar farashi da matsalar tsaro da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki, na daga cikin abubuwan da suka addabi ɓangaren noma a Najeriya cikin shekarar nan.

    Wannan ƙididdiga na zuwa ne albarkacin bikin Ranar Abinci ta Duniya, wanda ya mayar da hankali ga kira ga gwamnati ta haɗa hannu da ƙwararru wajen magance ƙalubalen ƙarancin abinci mai gina jiki a tsakanin al'umma.

    Hukumar ta bayyana gamsuwa da matakan da gwamnati ke ɗauka wajen wadata ƙasa da abinci, amma ta yi gargaɗin cewa dole sai ta ƙara ƙaimi domin cim ma hakan.

  2. Majalisar wakilai ta buƙaci Tinubu ya gaggauta gabatar da kasafin 2025

    Majalisar wakilai ta ja hankalin shugaban Najeriya Bola Tinubu kan yiyuwar karya tanadin dokar kashe kuɗin ƙasa idan har ya yi jinkirin gabatar da kasafin kuɗn 2025 ga majalisa.

    Wannan na zuwa ne yayin da ya rage watanni biyu wa'adin kasafin 2024 ya ƙare.

    Ɗan majalisar da ya gabatar da ƙudirin, Clement Jimbo, ya ja hankali cewa ya kamata a ce kawo yanzu an gabatar da kasafin kuɗin 2025 kasancewar watanni biyu kacal suka rage kafin wa'adin kasafin kuɗin bana ya ƙare.

    Majalisar wakilan ta bayyana damuwa a kan ƙurewar lokacin da ya kamata a samu domin nazari kan kasafin na baɗi kafin amincewa da shi a majalisar dokokin tarayya.

    Majalisar ta yi nuni da cewa doka ta buƙaci a gabatar wa majalisa ƙiyasin kasafin kuɗi aƙalla watanni huɗu kafin shiga sabuwar shekara domin samun damar tantancewa shi da kuma amincewa.

    A yanzu dai majalisar ta miƙa wannan batu ga kwamitinta a kan tsare-tsaren ƙasa.

    A ranar biyu ga watan Oktoba shugaba Tinubu ya bar Najeriya zuwa Birtaniya domin yin hutun makonni biyu.

  3. Sojojin Nijar sun buɗe ƙofar cin hanci - Transparency International

    Kungiyar Transparency International mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta ce matakan da shugabannin mulkin sojin Nijar sun buɗe ƙofar cin hanci da rashawa, saboda cire kwangilar ayyukan ma'aikatar tsaro da ayyukan gidajen zaman manyan jami'ai daga bin ƙa'idojin da doka ta yi tanadi.

    Wata takardar da Janar Abdourahamane Tiani, ya sanya wa hannu ta ce ba za a bi ƙa'idar bayar da kwangila ba a duk wani aiki da za a gudanar a cikin fadar shugaban ƙasar.

    Ƙungiyar mai yaƙi da cin hancin ta ce hakan wata hanya ce da jami'ai za su yi amfani da ita wajen tafka rashawa.

    Transparency International ta kuma zargin sojojin da suka ƙwace mulki a ƙasar da tafiyar da harkokin mulki ba bisa tanadin doka ba.

    A watan Yuli ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da dama sun yi gargadi kan ƙaruwar cin zarafin mutane a Nijar.

  4. Amurka ta ce ta kai hari wuraren ajiyar makaman ƴan tawayen Houthi a Yemen

    Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce ta kai wasu jerin hare hare kan wuraren ajiyar makamai guda biyar a sassan kasar Yemen da ke karkashin ikon ƴan tawayen Houthi.

    Sakataren tsaron Amurka, Lloyd Austin, ya ce sojojin Amurka sun kai hari a wuraren na ƙarƙashin ƙasa da ke ɗauke da makaman da ake amfani da su wajen kai hari kan jiragen ruwa na fararen hula da na soji a yankin.

    Ya ce hare-haren wata yar manuniya ce da ke nuna ko ba dade ko ba jima, Amurkar za ta samu bankaɗo wuraren da Hutawan ke amfani da su wajen hana zirga zirgar jiragen ruwa a yankin.

  5. Tauraron mawaƙan One Direction Liam Payne ya mutu

    Liam Payne, ɗaya daga cikin mawaƙa a tawagar One Direction, ya mutu a Argentina bayan ya faɗo daga hawa na uku na gidan bene a Buenos Aires, kamar yadda 'yansanda suka bayyana.

    Wata sanarwa ta ce 'yansanda sun ga gawar Payne bayan da masu aiki ceto suka garzaya unguwar Palermo a ranar Laraba, bayan da suka samu rahoton faruwar wani abin tayar da hankali.

    Payne mai shekaru 31, ya samu shahara ne sakamakon haɗa tawagarsu a shirin X Factor a shekara ta 2010 tare da Harry Styles, Louis Tomlinson, Niall Horan da Zayn Malik.

    Tun da farko a wannan watan, Payne ya halarci kallon kuwa a Argentina tare da daya daga cikin 'yan One Direction, Niall Horan.

    Sa'o'i kafin mutuwarsa, Payne ya wallafa a shafinsa na Snapchat cewa: "Yau rana ce me daɗi a Argentina."

  6. Sanatocin Kenya za su kaɗa ƙuri'ar tsige mataimakin shugaban ƙasar

    Majalisar dattawan Kenya za ta kaɗa ƙuri'ar tsige mataimakin shugaban ƙasar, Rigathi Gachagua yayin da aka shiga rana ta biyu ta zaman tsige shi a majalisar.

    Mataimakin shugaban ƙasar zai bayyana domin kare kansa a majalisar, inda doka ta yi tanadi za a iya tsige shi idan har aka samu amincewar kashi biyu cikin uku na jimillar su.

    Ya na fuskantar zargin aikata laifuka 11 da suka haɗa da rashawa da tunzura rikicin ƙabilanci da kuma yi wa gwamnati zagon ƙasa.

    Da aka fara zaman a ranar Laraba, mataimakin shugaban ƙasar ya musanta dukkan zargin da ake masa.

    A makon jiya ne aka samu ƴan majalisar ƙasar da dama masu goyon bayan tsige shi, lamarin da ya share fagen ƙaddamar da bincike a majalisar dattawan.

    Ɗan majalisar da ya gabatar da ƙudirin neman tsige shi, Mwengi Mutuse, ya bayyana a zauren majalisar a ranar Laraba inda ya haƙiƙance cewa Mista Gachagua ya saɓa tanadin kundin mulkin ƙasar.

    Tuni dai kafafen yaɗa labaran Kenya suka fara hasashen wanda zai maye gurbin Gachagua, inda suka gabatar da sunayen wasu gwamnoni da kuma ministoci.

  7. Kamala Harris ta yi alkawarin sauya salon mulkin Amurka idan ta lashe zaɓe

    Ƴar takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Democrat, Kamala Harris, ta yi alƙawarin sauya salo daga irin kamun ludayin shugaba Joe Biden, idan har ta samu nasara a zaben da za a yi a wata mai zuwa.

    A cikin hirarta ta farko da tashar Fox News mai ra'ayin mazan jiya, wacce aka tsara don tattaunawa da yan jam'iyyar Republican da ke da tantama kan abokin hamayyarta Donald Trump, Madam Harris ta ce tana wakiltar rukunin matasa shugabbannin gobe ne.

    Ta ce ''kamar kowanne sabon shugaban ƙasa, nima zan shigo da tawa kwarewar da na samu a tsawon rayuwata.''

    Ta yi ta zazzafar muhawara da jagoran tattaunawar Bret Baier na tashar Fox, a lokuta da dama musamman kan batun shige da fice.

  8. Amurka na nazari kan salon Isra'ila na hana shigar da abinci Gaza

    Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta ce Washington na sa ido don ganin Isra'ila ba ta aiwatar da abin da ta kira "manufar hukunta mutane da yunwa" a arewacin Gaza ba.

    Linda Thomas-Greenfield ta shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa aiwatar da wannan manufa na iya haifar da mummunan sakamako bisa dokokin kasa da kasa.

    An yi ta yada rahotannin cewa da gangan sojojin Isra'ila ke hana kai kayan agajin abinci zuwa zirin, a wani mataki na tilasta wa Falasdinawa barin arewacin yankin.

    Kimanin motoci 50 ne suka shiga zirin jiya Laraba, bayan wata wasikar barazana da Amurka ta aikawa Isra;ilar game da abun da take yi na hana shigar da kayan agaji.

    Sai dai Isra'ila ta musanta hana shigar da kayan jin kan, tana cewa Hamas ce ke handame su.

  9. Buɗewa

    Masu bibiyar BBC Hausa barkan mu da safiyar Alhamis.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.