Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Nabeela Mukhtar

  1. An gudanar da jana'izar babban kwamandan Iran a Tehran

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Dandazon mutane ne suka taru a Tehran, babban birnin Iran domin halartar jana'izar Abbas Nilforoushan, wani babban kwamandan dakarun juyin-juya hali na Iran.

    An yi imanin cewa an kashe Nilforoushan ne tare da tsohon shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah a wani hari da Isra'ila ta kai Lebanon ranar 27 ga watan Satumba.

    An kuma yi wasu jana'iza guda biyu a Iraqi a jiya Litinin kafin mayar da gawar zuwa ƙasarsa ta haihuwa.

    Kwamandan dakarun juyin-juya hali, Esmail Qaani, shi ma ya halarci jana'izar kamar yadda gidan talabijin na Iran ya nuna, abin da ya kawo karshen raɗe-raɗen wajen da yake.

    A ranar Juma'a, dakarun juyin-juya halin suka sanar da gano gawar Nilforoushan, inda aka yi jana'izar binne shi a garinsa ta haihuwa na Isfahan a Iran, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

  2. Libya na ci gaba da atisayen buga wasa da Najeriya

    Libya

    Asalin hoton, Libyan FF/X

    Tawagar kwallon kafa ta ƙasar Libya na ci gaba da atisayen buga wasa da Najeriya a wasan neman shiga gasar cin kofin Afirka ta 2025.

    Tawagar ta gudanar da atisayen ne a yammacin ranar Litiin a filin wasa na Benina International Stadium.

    Sai dai haka na zuwa ne a daidai lokacin da tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yanke shawarar cewa ba za ta buga wasa da Libya ba bayan sun tsinci kansu cikin wani yanayi da suka shafe kusan awa 15 a filin jirgin sama na Abraq da ke Libya.

    Tuni dai Super Eagles ta koma gida Najeriya yayin da ita kuma hukumar kwallon ƙafa ta Afrika CAF ta sanar da cewa ta fara bincike kan rikita-rikatar.

    Libya

    Asalin hoton, Libyan FF/X

    Libya

    Asalin hoton, Libyan FF/X

    Libya

    Asalin hoton, Libyan FF/X

  3. Dalilin da ya sa yan Najeriya suka kwana cikin duhu ranar Litinin

    Layin wuta na ƙasa

    Asalin hoton, TCN

    Najeriya ta sake fuskantar katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewar babban layin lantarki na ƙasar a ranar Litinin.

    Layin ya lalace ne da misalin ƙarfe 7 na yamma, kamar yadda sanarwa daga kamfanin rarraba lantarki ta ƙasa (TCN) ya bayyana.

    Lamarin ya jefa miliyoyin 'yan ƙasar da kuma sana'o'insu cikin duhu.

    Wannan dai shi ne karo na biyar da layin ke lalacewa a shekarar 2024.

    Shi ma kamfanin rarraba hasken wutar lantarki reshen jihar Kano (KEDCO) ya nemi afuwar kwastomominsa kan abin da ya faru a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

    "Muna bakin cikin sanar da ku cewa an samu ɗaukewar wuta ne sakamakon matsalar da aka samu a layin wuta na ƙasa," kamar yadda shugaban sashen sadarwa na kamfanin Sani Bala ya bayyana.

    Ya ce hakan ne ya janyo rashin rarraba wutar zuwa ga kwastomomi.

    "Muna rokon al'umma da su yi hakuri yayin da muke ci gaba da aiki tukuru don shawo kan matsalar ta faru da kuma mayar da wutar lantarki yadda muka saba," in ji shi.

    Ya buƙaci mutane da su kula sosai wajen kare kai daga masu sata ko lalata wayoyin wutar lantarki.

  4. 'Mutum 55 aka kashe cikin sa'o'i 24 a Gaza'

    Ma'aikatar lafiya karkashin ikon Hamas a Gaza ta ce aƙalla mutum 55 aka kashe a Gaza cikin sa'o'i 24 da suka wuce, sannan an jikkata wasu 329.

    A wani sabon bayani da ma'aikatar ta fitar, ta ce aƙall Falasɗinawa 42, 344 ne aka kashe sakamakon samamen da Isra'ila ta fara kai wa Gaza tun bayan harin da Hamas ta kai cikin Isra'ilar ranar 7 ga Oktoba, inda aka jikkata 99,013.

  5. Ƴan bindiga sun kai hari tare da kashe DPO a Delta

    Ƴan bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun kai hari tare da kashe wani DPO na ƴansanda a karamar hukumar Ughelli ta Arewa da ke jihar Delta.

    Mai magana da yawun ƴansandan jihar, Bright Edafe, shi ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya ce ƴan bindigar sun kuma raunata wani DPO na shiyyar Ororoekpe inda aka garzaya da shi asibiti domin ba shi kulawa.

    Edafe ya ce jami'an ƴansandan biyu sun fita samame ne da wasu jami'ai lokacin da ƴan bindigar suka yi musu kwantan-ɓauna, inda ya ce ana ci gaba da bin tsawunsu da nufin kama su.

    Kakakin ƴansandan ya kuma ruwaito karya doka da oda a wata karamar hukumar Aniocha ta Arewa na jihar inda matasa suka far wa kayayyaki tare da cinna musu wuta.

    A cewarsa, tarzomar ta ɓarke ne bayan lakaɗawa wani mutum duka har ta kai ga mutuwarsa da wani yayi wanda suke zargi da kwace filayen al'umma a yankin.

    Wasu jagororin al'umma sun nuna adawa da matakin abin da ya janyo tarzomar da ta yi sanadiyyar ran mutumin.

    Edafe ya bayyana cewa an kama mutum uku da ake zargi da aikata laifin kuma ana ci gaba da bincike.

  6. Isra'ila na duba yiwuwar mayar da martani kan harin da Iran ta kai mata

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Ofishin Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce matakin mayar da martani kan harin da Iran ta kai makonni biyu da suka gabata zai dogara ne kan buƙatun tsaron Isra'ila.

    Sanarwar da aka fitar a daren jiya ta kasance martani ne ga wani rahoto da jaridar Washington Post ta wallafa wanda ya ce Mr Netanyahu ya shaida wa shugaba Biden cewa ba zai kai hari kan tashoshin Nukiliyar Iran ba.

    Rahoton ya ce Isra'ila za ta takaita martanin na ta domin kaucewa yin tasiri kan zaɓen Amurka da za a yi a watan mai zuwa.

  7. 'Dole Najeriya ta ci gaba da gyaran tattalin arziki da take yi tsawon shekara 15'

    Shugaba Tinubu

    Asalin hoton, STATE HOUSE

    Bankin Duniya ya ce dole ne Najeriya ta ci gaba da yin tsare-tsaren da take kai a yanzu na tsawon aƙalla shekara 15, muddin tana son ɗorewar tattalin arzikinta.

    Mataimaikin shugaban bankin, Mr Indermit Gill ne ya bayyana haka a wani taron tattalin arziki karo na 30 da aka yi a Abuja ranar Litinin.

    Ya ce ya kamata gwamnati ta jajirce wajen ci gaba da tsare-tsarenta na yanzu domin shawo kan matsaloli da ƙasar ke fuskanta wanda kuma suka janyo rashin cigaba tsawon lokaci.

    "Babu wani wayo da za a yi a batun gyaran tattalin arziki. Ya kamata Najeriya ta tsaya kan tsare-tsarenta na tsawon shekara 15. Tsare-tsaren da aka ɗauka yanzu ba za su yi daɗi ba ko kuma kawo sakamako mai kyau nan take, amma za su ɗora ƙasar kan turbar cigaba mai ɗorewa," in ji shi.

    Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin ƴan Najeriya ke ci gaba da nuna fushinsu kan cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi da kuma tashin farashin dala.

    Duk da cewa waɗannan tsare-tsare sun janyo tsadar rayuwa da kuma wahalhalu daban-daban ga ƴan ƙasar, jami'in na Bankin Duniya ya ce komawa baya ba zai haifar da ɗa mai ido ga tattalin arzikin ƙasar ba.

  8. Harris da Trump sun fafata a jihar Pennsylvania

    Harris and Trump

    Yayin da ya rage makwanni uku a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Amurka, Kamala Harris da Donald Trump sun gudanar da yaƙin neman zaɓensu a jihar Pennsylvania.

    Ms Harris ta sanar da wani shiri na bai wa maza baƙaƙen fata ƙarin damammakin bunƙasa tattalin arziki tare da bayyana wasu dabi'un abokin karawarta a matsayin na mara hankali.

    Shi kuma Trump ya yi magana ne a wani taron zauren inda ya yi alkawarin bunƙasa harkar hako mai domin rage farashin makamashi.

  9. Dakarun mu ba za su fice daga Lebanon ba - MDD

    MDD

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dakarunta na wanzar da zaman lafiya da ke a kudancin Lebanon ba za su je ko ina ba, inda ta sake yin fatali da kiran da Isra'ila ta yi na janye su.

    Dakarun MDD da dama ne suka jikkata a harin da sojojin Isra'ila suka kai wa Hezbollah.

    Mataimakin babban sakataren MDD, Jean-Pierre Lacroix, ya jaddada cewa dole ne a tabbatar da tsaron dakarun.

    Ya ce babban kiran da su ke yi ga dukkan ɓangarorin shi ne su mutunta hakkin da ya rataya a wuyansu na kare lafiya da tsaron dakarun wanzar da zaman lafiyar.

  10. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da hantsin Talata.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da kuma sauran sassan duniya.