Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/09/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Tsohon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu zai bayyana a gaban kotu yau

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A yau ne tsohon mataimakin Sudan ta Kudu na farko Riek Machar, zai bayyana gaban kotu inda zai fuskanci shari'ar da ake masa kan zargin aikata kisa da cin amanar ƙasa da kuma laifukan da suka shafi take haƙƙin bil adama.

    Tuhume-tuhumen na da alaƙa da harin da mayaka masu ɗauke da makamai waɗanda ake zargi na bashi goyon baya suka kai wanda ya yi sanadin rasa rayukan sojojin Sudan ta Kudun 250.

    An cire Mista Machar daga kan muƙaminsa a lokacin mulkin gwamnatin haɗin kai ƙarkashin shugaba Salva Kiir inda aka yi masa ɗaurin talala bayan harin da aka kai a watan Maris.

    Magoya bayansa sun bayyana shari'ar a matsayin bita da ƙullin siyasa sannan sun zargi Mista Kiir da neman rufe bakin abokin hamayyarsa.

    Wannan Shari'ar ta sanya fargabar yiwuwar sake dawowar yaƙin basasar ƙasar da kuma rikicin ƙabilanci wanda aka kawo ƙarshensa a 2018 bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

  2. Amincewa da ƙasar Falasɗinu taimakon ta'addanci ne - Netanyahu

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Firaiministan Isra'ila ya zargi shugabannin kasashen yamma wadanda suka amince da kafa Falasɗinu da mara wa ta'addanci baya.

    Benjamin Netanyahu, ya ce Falasdinawa ba za su taba samun kasarsu ba sannan kuma Isra'ila zata mayar da martani ga sanarwar da Birtaniya da Canada da Australia da kuma Portugal suka yi.

    Wakilin BBC ya ce a yau ma Faransa da sauran kasashen Turai za su sanarwa irin wannan a wajen babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya da za a yi.

    Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, ya ce amincewa da Falastine a matsayin kasa mataki ne tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin. Amurka ma dai kira matakin kassshen yamma a matsayin neman suna.

    A bangare guda kuma rahotanni sun ce an kashe karin wasu Falasdinawa 71 a Gaza a jiya Lahadi.

  3. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya Lahadi wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su Facebook da X da Instagram domin karanta wasu labaran.

    Ku kasance tare da mu.