Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran muhimman labarai a sassan duniya na 16/04/2026.

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Ƙungiyar ɗaliban FGC Kano sun koka kan ƙoƙarin mamaye filayen makaranta

    Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban kwalejin tarayya da ke Kano ta yi kakkausar suka kan abin da ta kira haramtaccen cin iyakar fili mallakar kwalejin tarayya da ke Kano.

    Al'amarin dai ya janyo damuwa a tsakanin tsaffin ɗaliban game da tsaron kadarorin ilimi na ƙasa.

    Kungiyar ta bayyana cewa ta ɗauki matakai cikin gaggawa domin shawo kan lamarin, ciki har da matakan shari’a, amma a cewarsu ana ci gaba da aikin yanka filayen da gine-gine.

  2. Ukraine ta ce harin Rasha ya kashe mata mutum 12

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Ukraine sun ce wasu hare-haren makamai masu linzami da Rasha ta kai cikin dare a yankun da dama na ƙasar sun kashe aƙalla mutum 12.

    Mutum shida sun mutu a yankin tashar jirgin ruwa ta Odesa da ke kudanci kamar yadda hukumomin soji na birnin suka ce.

    Mutum huɗu sun rasu a hare-haren makamai masu linzami a babban birnin ƙasar Kyiv, ciki har da yaro mai shekara 12. An kuma kashe uku a Dnipro da ke tsakiyar Ukraine ɗin.

    Su ma dai dakarun Ukraine na kai hari Rasha, inda Gwamnan yankin Krasnodar da ke kudancin Rasha ya ce hare-haren jiragen sama marassa matuka na Ukraine sun kashe yara biyu, 'yan shekara 5 da kuma 14, da lalata harkokin kasuwanci a kusa da tashar jirgin ruwa ta Tuapse da ke Bahar Aswad.

  3. Gagarumar gobara ta tashi a matatar mai a Australia

    Masu aikin agajin gaggawa a Australia sun ce an yi nasarar kashe wata gagarumar gobara da ta tashi a daya daga cikin matutun man ƙasar biyu.

    Gobarar ta tashi ne a matatar Geelong da ke jihar Victoria, inda fashewa ta rika cilla wuta sama har tsawon sama da kafa 190.

    Yanzu abin da ake ƙoƙarin sani shi ne irin illar da gobarar ta yi da kuma yadda tasirinta zai kasance wajen samar da mai a Australia.

    Tuni dai farashin ya yi tashin gwauron zabi saboda yaƙin Gabas ta Tsakiya.

    Matatar man ƙasar na samar da wajen kashi 10 cikin dari na man da ƙasar ta Australia ke buƙata, duk da cewa an kashe wutar, lamarin zai iya shafar yawan fetur ɗin da ake samarwa.

    Har yanzu matatar na ƙwarya-ƙwaryar aiki, inda za a ci gaba da samar da man gas da dizil da man jirgin sama - cikin takatsantsan. An samu dukkanin ma'aikatan matatar.

  4. Yaƙin Iran zai shafi yara 40,000 - Save The Children

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon bincike da ƙungiyar agaji ta duniya ta Save the Children ta fitar, ya nuna cewa a duk ƙarin dala biyar a kan kowace gangar ɗanyen mai, na iya raba kusan yara 40,000 da samun tallafin abinci da magunguna don kare rayukansu.

    Rahoton ya fito ne a dai-dai lokacin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara haddasa tashin farashin man fetur a duniya.

    Wannan matsi na zuwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin Amurka da Iran.

    Hakan dai na nuna yadda rayuwar ƙananan yara ta dogara kacokan kan yanayin farashin makamashi na Duniya.

  5. An yanke wa Malema hukuncin zaman gidan kaso na shekaru biyar

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An yanke wa fitaccen ɗan siyasar nan na ƙasar Afirka ta Kudu, Julius Malema mai shekaru 45 ɗaurin shekara biyar a gidan yari.

    Twanet Olivier wadda ta yanke hukuncin a wata kotun Majistare ta samu Malema da laifin mallakar harsasai da harba bindiga ba bisa ƙa'ida ba a wurin taruwar jama'a da jefa rayuwar mutane haɗari.

    Malema wanda ya saka baƙaƙen kaya da jan lakatai sannan yana tsaye yana kallo a lokacin da alƙaliyar ta yanke masa hukunci.

    Tawagar lauyoyin Malema sun fara shirin neman ɗaukaka ƙara.

  6. Ana fargabar ƴan'ta'adda na shirin kai hare-hare a Abuja - AFP

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an tsaron Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon bayanan sirri da ke nuna cewa ƙungiyoyin ƴan'adda na shirin kaihare-hare kan gine-gine gwamnati a Abuja, babban birnin Najeriya da jihar Neja mai maƙwabtaka.

    Wata wasikar sirri ta cikin gida a hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya da kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu, ta nuna cewa ƴan bindigar na shirin kai wa filin jirgin sama na Abuja da gidan yari da cibiyar tsare mutane ta sojoji duka a Abuja.

    Bayanin na sirri ya yi kama da harin da ƴan bindiga suka kai wa sansanin sojin sama a birnin Niamey na jamhuriyar Nijar abin da ya janyo fargabar yiwuwar hare-haren bai ɗaya a yankin.

  7. Hezbollah ta ce ta harba rokoki zuwa garuruwan Isra'ila

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Ƙungiyar Hezbollah ta ce ta harba jerin rokoki ga Isra'ila da safiyar ranar Alhamis.

    A wani saƙo da ƙungiyar ta wallafa a Telegram, ta ce ta kai hare-hare kan Kiryat Shmona da Kfar Giladi da Misgav Am da kuma Margaliot da ke arewacin Isra'el da ke kusa da kan iyakarta da Lebanon.

    "Wannan martanin zai ci gaba har zuwa lokacin da zaluncin Amurka da Isra'ila a kan ƙsarmu da mutanenmu," in ji saƙon na Hezbollah.

    Kawo yanzu dai Isra'ila ba ta uffan ba.

    Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta ƙoƙarin zaman tattaunawa tsakanin Isra'ila da Lebanon wanda bayanai ke nuna Donald Trump ke matsa lambar yin hakan.

  8. Shugaban Faransa na shirin haramta wa ƴan ƙsa da 15 amfani da soshiyal midiya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Faransa na shirin gudanar da wani taro ta hanyar bidiyo, da shugabannin tarayyar Turai, domin ci gaba da matsa lamba don haramta wa duk wani da yake ƙasa da shekara 15 amfani da shafukan sada zumunta.

    Wakilin BBC ya ce Emmanuel macron zai shafe ranar a cibiyar harshen Faransanci ta ƙasa da ƙasa da ke arewacin Paris inda zai ƙaddamar da ranar, kashe intanet -ta ƙasar domin ƙarfafa wa yara gwiwa su riƙa karatu

    Yanzu haka wata doka da za ta buƙaci shedar yawan shekarun mutum kafin ya yi amfani da shafukan na majalisar dokokin Faransa inda ake shirin tabbatar da ita.

    Haka kuma taron zai tattauna wasu hanyoyin na tantance yawan shekarun mutum.

    Ba da daɗewa tarayyar Turai ta ƙaddamar da manhajarta ta tantance shekaru, wadda matasa 'yan shekaru goma sha za su iya amfani da ita domin shiga shafukan sada zumunta.

    Haka kuma manhajar za ta iya dakatar da duk wanda yake ƙasa da shekara 18 daga shiga shafukan batsa da na caca.

  9. Trump ya ce Isra'ila da Lebanon za su yi magana da juna

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Trump ya nuna cewa shugabannin Isra'ila da Lebanon za su yi magana da juna, a ranar Alhamis- zaman karon farko a sama da shekara 30.

    A wani sako da ya sanya a shafinsa na sada zumunta Trump ya ce yana kokarin ganin ya samar da 'yar sa'ida a tsakanin kasashen biyu.

    Iran dai ta kafe cewa dole ne a shigar da batun rikicin Isra'ila da Hezbollah a duk wata yarjejeniya da za a yi ta kawo karshen babban yakin Gabas ta Tsakiya.

    A ranar Laraba Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce dakarun kasarsa na ci gaba da matsawa da kai hari kan Hezbollah.

  10. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barkan ku da warhaka a shirin shafin kai tsaye na BBC Hausa inda muke kawo muku labarai da rahotanni kan muhimman abubuwan da ke faruwa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da ƙasar Iran da abubuwan da ke faruwa a sauran ƙsashen duniya.

    Yau ma kamar kullum mun dawo da shafin namu kuma da fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu. Mun gode