Hakimi ya murmure daga jinya zai buga wa Morocco Afcon
Wanda ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallon kafa na bana na Afirka, Achraf Hakimi ya warke daga jinya, zai kuma buga wa Morocco gasar cin kofin nahiyar Afirka da za ta gudanar, kamar yadda ya sanar ga manema labarin wasanni ranar Asabar.
Tun farko an yi tantamar da ƙyar ne idan ƙyaftin din zai yi wa Morocco wasannin, bayan raunin da ya ji a karawa da Paris St Germain ta yi rashin nasara a hannun Bayern Munich a Champions League a Faransa a watan jiya.
Tun daga lokacin ake cewa ba zai warke da wuri ba, amma kuma mai shekara 27 ya sanar da bakinsa cewar ya warke a kuma lokacin da za a yi bikin fara wasannin ranar Lahadi 21 ga watan Disamba.
Morocco mai masaukin baƙi za ta fara wasa a rukunin farko da Comoros a Rabar ranar Lahadi, amma ba a fayyace ko za a fara wasan da Hakimi ba.
An bayyana mai tsaron bayan a matakin gwarzon ɗan ƙwallon kafar Afirka na bana a watan jiya a Rabat, ya kuma karɓi ƙyautar tare da sandunan dogarawa, sakamkon aiki da aka yi masa a kafarsa.
Sai dai kuma tawagar Morocco ta bayyana shi cikin ƴan ƙwallon da za su buga mata babbar gasar tamaula ta Afirka.