Bayan watanni na shirye-shiryen gudanar da gasar cin kofin ƙasashen Afirka (AFCON) tuni aka yi bikin fara wasannin ranar Lahadi a birnin Rabat, inda Morocco mai masukin baƙi ta doke Comoros 2-0 a rukunin farko.
Ƙungiyoyi 24 za su kece raini a gasar da za a yi birane guda shida a filayen wasa tara a ƙasar da ke da tsananin sha’awar ƙwallon ƙafa.
Za a yi mako huɗu aka tata ɓurza a wasannin, kuma za ta yi ta yi gwaji a wasannin kafin gasar cin kofin duniya ta 2030, inda Maroko ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da za su karɓi baƙunci.
Hakan ya sa masarautar kasar ta fara shirye-shiryen gina manyan kayayyakin more rayuwa mafi girma a tarihin wasannin motsa jiki na Afirka domin shiri da take yi kafin gasar kofin duniya da za ta yi hadaka da Sifaniya da kuma Portugal.
Mai rike da kofin, Ivory Coast, tana fatan kare kofin da ta lashe a 2023, yayin da Najeriya za ta yi fatan wuce matakin da ta kai bayan rashin nasara a wasan karshe a hannun Ivory Coast.
Senegal ta Sadio Mané tana cikin wasannin bayan lashe gasar shekarar 2021, yayin da Masar ke fatan rade-radin makomar Mohamed Salah ba zai ɗauke hankalin tawagar ba daga neman lashe kofi na takwas jimilla a nahiyar, wanda zai zama sabon tarihi.
Ga jerin rukunin kasashen da za su buga Afcon a Morocco:
Rukunin farko: Morocco, Mali, Zambia, Comoros
Rukuni na biyu: Egypt, South Africa, Angola, Zimbabwe
Rukuni na uku: Nigeria, Tunisia, Uganda, Tanzania
Rukuni na huɗu: Senegal, DR Congo, Benin, Botswana
Rukuni na biyar: Algeria, Burkina Faso, Equatorial Guinea, Sudan
Rukuni na shida: Kamaru, Gabon, Ivory Coast da kuma Mozambique
An fara gasar cin kofin Afirka a Morocco ranar 21 ga watan Disambar 2025 za kuma a karkare ranar 18 ga watan Janairun 2026.