Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 17/11/2025

Wannan shafi ne da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 17/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Aliyu Ja'afar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Ma'aikatan lantarki sun yi barazanar katse wuta a faɗin Najeriya

    Ma'aikacin wutar lantarki ya na aikin gyara wuta

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ma'aikatan lantarki ta Najeriya (NUEE) ta yi barazanar katse wuta a faɗin ƙasar, sakamakon zargin da take yi na cewa an kai wa ma'aikatan kamfanin rarraba lantarki na ƙasar hari.

    Cikin wata sanarwa da muƙaddashin babban sakataren ƙungiyar, Dominic Igwebike ya fitar, ya ce hakan ya zama wajibi ne bayan zargin wasu ƴansanda da ke aiki bisa umurnin gwamnatin jiha, sun yi wa ma'aikatan da ke aiki a cibiyar lantarki ta Egbu da ke Jihar Imo duka, da yi musu barazana da bindiga da kuma garkuwa da wasu.

    A cewar sa ƴan sandan sun shiga cibiyar ne da ƙarfin tsiya, tare da lalata kayayyakin aiki da dakatar da ayyukan da ake gudanarwa, kamar yadda kafar talibijin ta channels ta ruwaito.

    A cewar sanarwar, ƙungiyar ta riga ta bai wa mambobinta umurnin katse samar da lantarki a jihar Imo har sai wani lokaci.

    Ta kuma yi barazanar katse aiki a faɗin Najeriya har sai hukumomi sun ɗauki matakan gaggawa na tabbatar da tsaron ma'aikatan lantarki a faɗin ƙasar.

  2. SERAP ta buƙaci CBN ya dawo da Naira triliyan 3 da ake zargin sun yi ɓatan dabo

    Ƙungiyar Kare Haƙƙin Jama’a da Kula da Al’amuran Tattalin Arziki (SERAP), ta bai wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, kwanaki bakwai da ya fitar da bayanai kan Naira Tiriliyan 3 na kuɗaɗen al’umma da ake zargin sun yi batan dabo.

    Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan lamari na zuwa ne bayan wani rahoton Babban Ma’ajin Kasa na shekara ta 2022, wanda ya buƙaci CBN ya bayyana inda kuɗaɗen suka shiga.

    Rahoton ya nuna akwai matsalar ɓacewar rarar kudi da basukan da ba a biya ba da kuma kwangiloli masu cike da ayoyin tambaya.

    SERAP ta ce CBN ya gaza tura sama da naira triliyan 1 da biliyan 440 na rarar kudi na gwamnatin tarayya zuwa asusun kuɗaɗen shiga na bai ɗaya.

    A sanarwar da ta fitar, SERAP ta lura cewa CBN bai karɓo sama da naira biliyan 700 ba na basussukan da kuɗaden kai dauki da aka bayar tsakanin 2018 zuwa Mayun 2022 ba.

    Haka kuma CBN ya bayar da kwangiloli 43, na sama da Naira biliyan 189, sai dai ƴan kwangilar sun yi jinkiri da gangan inda daga baya suka buƙaci a sauya farashin kwangilar wanda ya kai ga biyan kuɗi fiye da Naira biliyan 9 ba bisa ƙa'ida ba.

    Tana kuma fargabar za a iya karkatar da waɗannan kudaɗen don haka ne ta nemi a gaggauta dawo da su baitul malin gwamnati, ko ta ɗauki matakin shari'ah.

  3. Da gaske ne an yi yunƙurin kashe Lt. Yerima a Abuja?

    AM Yerima

    Asalin hoton, Lere Olayinka - Aresa 1

    Da yammacin ranar Lahadi ne rahotonin yunƙurin kashe Laftanar Ahmed Yerima - matashin sojan da ya yi sa-in-sa da ministan Abuja, Nyesom Wike a makon da ya gabata - suka cika shafukan sada zumunta.

    Rahotonnin sun yi iƙirarin cewa wasu matasa ne da ba a san ko su wane ne ba suka yi yunƙurin halaka sojan ruwan a Abuja, babban birnin ƙasar.

    Laftanar AM Yerima ya ɗauki hankalin ƴan Najeriya a makon da ya gabata bayan da ya jagoranci tawagar wasu sojoji da suka hana ministan Abuja, shiga wani fili da ya yi zargin ana gina shi ba bisa ƙa'ida ba.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ƴansandan Najeriya, reshen birnin na Abuja ta fitar ta hannun kakakinta, SP Josephine Adeh, ta ce babu inda aka samu irin wannan iƙirari.

    Karanta cikakken labarin a nan:

  4. Babban taron PDP ya saɓa wa doka - Anyanwu

    Sakataren ɗayan ɓarin jam'iyyar PDP, mai alaƙa da ministan Abuja Nyesom Wike, Samuel Anyanwu, ya bayyana babban taron jam'iyyar da aka gudanar cikin ƙarshen mako a garin Ibadan da ke jihar Oyo a matsayin abin da ya saɓa doka.

    Anyanwu ya faɗi hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar talibijin ta Channels.

    A cewar sa, a yayin da jihohi da dama suka ƙaurace wa taron, ba za a iya bayyana shi ba a matsayin wanda aka yi da yawun kowa ba.

    A taronta na 2025 da aka yi a ƙarshen mako, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta kori Ministan Abuja Nyesom Wike, da tshohon gwamnan Ekiti Ayo Fayose, da sakataren ta na ƙasa Samuel Anyanwu, da wasu ƴan jam'iyyar saboda zargin yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.

    Hakazalika jam'iyyar ta rusa shugabancin jamiyyar a jihohin Imo da Abia da Enugu da Akwa Ibom da kuma Rivers.

    A gefe guda kuma tsagin Wike na jam'iyyar ya kira taron gaggawa na shugabanci da kuma kwamitin amintattun jam'iyyar na ɓarinsa.

  5. Hasina: Kotu ta yanke wa tsohuwar Firaiministar Bangladesh hukuncin kisa

    Sheikh Hasina, tsohuwar Fira ministar Bangladesh

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Dhaka, babban birnin ƙasar Bangladesh ta yanke wa tsohuwar Firaiministar ƙasar Sheikh Hasina hukuncin kisa bayan ta same ta da laifin cin zarafin bil'adama, da kuma bai wa jam'ian tsaro umurnin kashe masu zanga-zanga.

    An yi mata shari'ar ne yayin da take gudun hijira a Indiya, inda ta tsere tun bayan hamɓarar da gwamnatin ta.

    Sai dai Sheikh Hasina ta ƙi amincewa da hurumin kotun na yi mata shari'a.

    An jibge jami'an tsaro a wajen kotun da ma faɗin babban birnin ƙasar.

  6. Ana yanke wa Sheikh Hasina hukunci kan zargin cin zarafin bil'adama

    Hambararriyar fira ministan Bangladesh Hasina

    Asalin hoton, Getty Images

    An tsaurara matakan tsaro a duk faɗin ƙasar Bangladesh a yayin da ake yanke hukunci a shari'ar da ake yi wa hambararriyar Firaminista, Sheikh Hasina.

    Ana zargin ta da aikata laifukan cin zarafin bil'adama, kuma ana mata shari'ah ne ba tare da tana nan ba saboda ta tsere daga ƙasar zuwa Indiya bayan an hambarar da gwamnatinta.

    'Yan sanda ɗauke da makamai na tsaye a wajen kotun da ke Dhaka.

    An bai wa jami’ai izinin buɗe wuta idan aka lalata dukiyoyin jama’a ko kuma idan aka jefa bama-baman fetur kan jami’an tsaro.

    Ana shari'ar Ms Hasina ne, dangane da umarnin da ake zargin ta bayar na murƙushe zanga-zangar da ɗalibai suka yi a bara, inda aka kashe ɗaruruwan mutane.

    Ms Hasina ta musanta zargin, sai dai masu shigar da ƙara na neman a yanke mata hukuncin kisa.

  7. Ina son a fitar da bayanan gwamnati kan Epstein -Trump

    Shugaba Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Donald Trump ya ce ya na goyon bayan ƙoƙarin da ƴan majalisa ke yi na fitar da bayanan gwamnati da suka shafi mutumin da aka samu da laifin lalata wato Jeffrey Epstein.

    A wani lamari da ake yi wa kallon gagarumin sauyin ra'ayi, Mista Trump ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa ba su da wani abin da za su boye, inda ya ƙara da cewa lokaci ya yi da za a rufe babin wannan batu da ya bayyana a matsayin wata yaudara ta 'yan jam'iyyar Democrat.

    Ya ce suna amfani da Jeffery Epstein a matsayin abin da zai kawar da hankali daga manya-manyan nasarorin da jam'iyyar su ke samu.

    Shugaban na Amurka dai yana fuskantar matsin lamba daga ‘yan jam’iyyar Democrat da wasu ‘yan Republican kan matakin da gwamnatinsa ta dauka na ƙin sakin bayanai kan shari'ar Epstein.

    A ranar Talata ne ake sa ran majalisar za ta kada kuri’a kan batun.

  8. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin.

    Aisha Aliyu Ja'afar ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a fadin duniya.

    Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.