Ƙungiyar dillan mai a Najeriya ta IPMAN ta yi barazanar rufe gidajen mai a faɗin ƙasar idan gwamnatin tarayya ta tilasta musu sayar da man fetur a farashin da ta ƙayyade.
Barazanar ta biyo bayan kalaman ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da kuma hukumar albarkatun mai ta NMDPRA, waɗanda suka gargaɗi dillalan mai kan ci gaba da sayar da man fetur a farashin da bai yi daidai da saukar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ba.
Jaridar Daily Trust ta ambato sakataren yaɗa labarai na IPMAN, Chinedu Ukadike, na cewa idan gwamnati ta yi yunƙurin ƙaƙaba farashin man fetur zai sa ƙungiyar ta dakatar da ayyukan gidajen mai a faɗin Najeriya.
"Idan gwamnati ta yi ƙoƙarin tilasta mana ƙayyade farashi, za mu rufe dukkan gidajen manmu a faɗin ƙasar."
NMDPRA dai ta yi gargaɗin cewa za ta hukunta gidajen man da ke sayar da man fetur a farashin da bai yi daidai da farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ba.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, George Ene-Ita, ya fitar a ranar Laraba, ya ce hukumar na sane da raguwar farashin ɗanyen mai a duniya, inda ya ce dole ne farashin man fetur ya zo daidai da yadda farashin yake, kamar yadda dokar albarkatun mai ta 2021 a ƙasar ta tanada.
Ya ce hukumar ta riga ta gargaɗi kamfanonin kasuwancin mai da su guji ƙara farashi domin cin ribar da ta wuce ƙa'ida.
NMDPRA ta ce ana sa ido kan gidajen mai, kuma za a ɗauki matakin a kan duk wanda aka samu da laifi.
Lokpobiri ya ce bayan dakatar da yaƙi tsakanin Iran da Amurka, ƴan Najeriya na sa ran ganin an rage farashin man fetur a ƙasar.