KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 01 ga watan Yulin 2026

Skip Bidiyo and continue reading
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Muslim Muhammad Yusuf da Haruna Kakangi

  1. Farashin ɗanyen mai ya ƙara sauka bayan tattaunawar Iran da Amurka

    Farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya na ci gaba da faɗuwa a ranar Laraba bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka a ƙasar Qatar na tafiya yadda ya kamata.

    Farashin ɗanyen mai na Brent ya sauka zuwa dala 71.35 kan kowace ganga, yayin da na West Texas Intermediate (WTI) ya ragu zuwa dala 68.28 kan kowace ganga.

    Ana kallon tattaunawar da ake yi a Qatar na taka rawa wajen samun wannan ci gaban, lamarin da ya rage fargabar da ake yi kan yiwuwar samun tangarɗa ga samar da ɗanyen mai.

    Trump ya ce dangantaka tsakanin Amurka da Iran na tafiya yadda ya kamata, inda ya ce ana ganin ci gaba a tattaunawar da ke gudanar a Qatar.

  2. DSS ta kama tsohon ministan fasahan Najeriya kan zargin takardun bogi

    Uche Nnaji

    Asalin hoton, Uche Nnaji/X

    Jami'an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) sun kama tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, a safiyar ranar Laraba a filin jirgin saman Akanu Ibiam da ke Enugu.

    Rahotanni sun ce an kama Nnaji ne yayin da yake shirin hawa jirgi zuwa Abuja.

    Wasu majiyoyin tsaro sun ce jami'an DSS sun kama shi ne bisa buƙatar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, wadda ake zargin tana bincikensa kan zargin amfani da takardun bogi

    Daga bisani an miƙa shi ga hukumar ICPC, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Majiyoyin sun kuma ce ICPC ta taɓa gayyatar tsohon ministan sau da dama bayan samun koke-koke kan yadda ya gudanar da ma'aikatar da yake jagoranta, lamarin da ya sa ta nemi taimakon DSS domin cafke shi.

    Uche Nnaji ya yi murabus daga muƙaminsa a ranar 7 ga Oktoban 2025, bayan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan takardun karatunsa daga Jami'ar Najeriya (UNN) da kuma takardar kammala bautar ƙasa ta NYSC.

    A lokacin, ya ce murabus ɗin ba yana nufin amincewa da laifin da ake zarginsa da shi ba ne, illa dai mataki ne na mutunta tsarin shari'a, inda ya ce zarge-zargen suna da alaƙa da siyasa.

    A watan Nuwamban 2025, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya domin tilasta wa Jami'ar da shugaban jami'ar su ba shi kwafin cikakken bayanan karatunsa.

    Lamarin ya sake ɗaukar sabon salo ne bayan jam'iyyar PDP ta zaɓi Uche Nnaji a matsayin ɗan takararta na gwamnan jihar Enugu a zaɓen 2027.

  3. Girgizar ƙasa a Venezuela na iya ƙara barazanar fataucin ƙananan yara - MDD

    Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargaɗi cewa girgizar ƙasar da ta afku a Venezuela a makon da ya gabata na iya ƙara buɗe kafar safarar ƙananan yara idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba kan yaran da lamarin ya shafa.

    UNICEF ta ce ana ƙiyasin aƙalla ƙananan yara 680,000 ne ke buƙatar agajin gaggawa a yankunan da girgizar ƙasar ta shafa, inda yawancin iyalai suka rasa matsuguni ko suka rabu da ƴaƴansu.

    Masu aikin jin ƙai a ƙasar sun kuma ce an samu rahoton ɓacewar wasu yara bayan an ceto su daga wuraren da girgizar ta shafa.

    Haka kuma an gano wani tallan intanet da ake zargin yana ƙoƙarin tara yaran da sayar da su, abin da ya ƙara tayar da hankalin hukumomi.

    Ƙungiyoyin fararen hula a Venezuela na ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin duniya da su ƙara ƙaimi wajen kare haƙƙin ƙananan yara tare da toshe duk wata kafa da masu safarar mutane za su iya amfani da ita a wannan yanayi.

  4. Za mu rufe gidajen mai idan gwamnati ta tilasta mana ƙayyade farashi - Dillalai

    Gidan mai a Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar dillan mai a Najeriya ta IPMAN ta yi barazanar rufe gidajen mai a faɗin ƙasar idan gwamnatin tarayya ta tilasta musu sayar da man fetur a farashin da ta ƙayyade.

    Barazanar ta biyo bayan kalaman ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da kuma hukumar albarkatun mai ta NMDPRA, waɗanda suka gargaɗi dillalan mai kan ci gaba da sayar da man fetur a farashin da bai yi daidai da saukar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ba.

    Jaridar Daily Trust ta ambato sakataren yaɗa labarai na IPMAN, Chinedu Ukadike, na cewa idan gwamnati ta yi yunƙurin ƙaƙaba farashin man fetur zai sa ƙungiyar ta dakatar da ayyukan gidajen mai a faɗin Najeriya.

    "Idan gwamnati ta yi ƙoƙarin tilasta mana ƙayyade farashi, za mu rufe dukkan gidajen manmu a faɗin ƙasar."

    NMDPRA dai ta yi gargaɗin cewa za ta hukunta gidajen man da ke sayar da man fetur a farashin da bai yi daidai da farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ba.

    A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, George Ene-Ita, ya fitar a ranar Laraba, ya ce hukumar na sane da raguwar farashin ɗanyen mai a duniya, inda ya ce dole ne farashin man fetur ya zo daidai da yadda farashin yake, kamar yadda dokar albarkatun mai ta 2021 a ƙasar ta tanada.

    Ya ce hukumar ta riga ta gargaɗi kamfanonin kasuwancin mai da su guji ƙara farashi domin cin ribar da ta wuce ƙa'ida.

    NMDPRA ta ce ana sa ido kan gidajen mai, kuma za a ɗauki matakin a kan duk wanda aka samu da laifi.

    Lokpobiri ya ce bayan dakatar da yaƙi tsakanin Iran da Amurka, ƴan Najeriya na sa ran ganin an rage farashin man fetur a ƙasar.

  5. Ƴanbindiga sun kashe mutum 10 a Benue

    Benue Govt

    Asalin hoton, Benue Govt

    Aƙalla mutum 10 aka kashe da sanyin safiyar Laraba bayan wasu mahara ɗauke da makamai sun kai hari ƙauyen Saai da ke gundumar Mbajir a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

    Mazauna yankin sun ce maharan sun kutsa cikin ƙauyen da tsakar dare, inda suka riƙa harbe-harbe ba tare da ƙaƙƙautawa ba.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani mazaunin yankin na cewa wasu daga cikin mutanen sun jikkata sakamakon harbin bindiga, yayin da aka kashe wasu ciki har da Mchiaga Akaa Agbondo, wanda ya ce "an sassara shi da adda har ba a gane fuskarsa".

    Ya ƙara da cewa ana ci gaba da kula da wasu da suka jikkata a asibiti.

    Shugaban ƙaramar hukumar Katsina-Ala, Justine Shaku, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma ya je yankin domin duba halin da ake ciki.

    Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi Allah wadai da harin, inda ya yi zargin cewa maharan ƴan ta'adda ne da ke fakewa da sunan makiyaya, domi kawo cikas ga ayyukan noma da samar da abinci a jihar.

    Gwamnan ya umarci jami'an tsaro su tura ƙarin dakaru zuwa yankin Saai da sauran ƙauyukan da ke makwabtaka da yankin domin farautar waɗanda suka kai harin, tare da ƙara tsaurara matakan tsaro ga manoma.

    Rundunar ƴansanda ba ta fitar da wata saarwa game da harin ba.

  6. ADC ta shigar da sunan Atiku da Amaechi a matsayin ƴan takararta a shafin INEC

    Atiku da Amaechi

    Asalin hoton, ATIKU/X

    Jam’iyyar adawa ta ADC a Najeriya ta ce ta shigar da sunayen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa na zaɓen 2027 a shafin tantance ƴan takara na hukumar zaɓe INEC.

    Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

    Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, Bolaji ya ce shigar da sunayen da bayanan ƴan takarar wani babban ci gaba ne a shirye-shiryen da jam’iyyar ke yi don tunkarar babban zaɓen ƙasar.

    INEC ce ke bayar da damar shigar da sunayen ƴan takara ga jam'iyyun siyasa a ƙasar, inda ta yi zama da wakilan jam'iyyun domin nuna musu yadda tsarin yake.

  7. Mutum uku sun mutu yayin murnar nasarar Mexico a gasar kofin duniya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum uku ciki har da wata budurwa mai shekara 19 ne suka mutu sakamakon turmutsutsu yayin murnar nasarar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Mexico ta samu kan Ecuador da cin 2-0 a birnin Mexico.

    Jami'an lafiya sun ce sauran mutanen da suka mutu sun haɗa da wata mata mai shekara 48 da wani namiji mai shekara 44, waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu bayan an kai su asibiti.

    Sama da mutum miliyan ɗaya ne suka taru a kusa da dandalin Angel of Independence domin murnar nasarar, wadda ita ce ta farko da Mexico ta samu tun shekarar 1986.

    Magajin garin Mexico City, Clara Brugada, ta miƙa ta'aziyya ga iyalan mamatan tare da kira ga jama'a da su yi bukukuwa cikin hankali da kulawa.

    Nasarar ta sa Mexico ta kai zagayen 'yan wasa 16 na arshe, inda za ta iya karawa da Ingila idan ta doke Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

  8. Iran ta sha alwashin ɗaukar fansar kisan Ayatollah Ali Khamenei

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta bayyana cewa za ta ɗauki fansar kisan jagoran addininta, Ayatollah Ali Khamenei da ya mutu a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai mata..

    Majalisar tsaron ƙasar ce ta sanar da hakan a shafinta na X inda ta ce za su ɗauki fansa daga duk waɗanda ta zarga da hannu wajen shiryawa da kuma aiwatar da kashe shi.

    An kashe Khamenei a ranar 29 ga watan Maris, ranar farko ta harin da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran.

    Harin ya kuma yi sanadin mutuwar wasu manyan jami'an ƙasar da kuma wasu daga cikin iyalansa.

    Majalisar tsaron ƙasar ta ce ba za ta ƙyale waɗanda suka aikata kisan ba kuma sai ta hukunta su.

    Iran ta jaddada aniyarta ta ɗaukar matakin ramuwar gayya kan waɗanda take ɗora wa alhakin mutuwar jagoran.

    A halin yanzu, an shirya gudanar da jana'izar Khamenei da kuma binne shi daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli a biranen Tehran da Qom da Mashhad.

    Haka kuma, za a gudanar da bukukuwan tunawa da shi a biranen Bagadaza, Kazmain, Karbala da Najaf na ƙasar Iraki.

  9. An kama mutum 900 bayan zanga-zangar ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami’an tsaro a Afirka ta Kudu sun ce sun kama mutum 900 bayan zanga-zangar ƙyamar baƙi da aka gudanar a faɗin ƙasar ranar Talata.

    Mafi yawan waɗanda aka kama ana zarginsu da laifukan shige da fice ba bisa ƙa’ida ba da kuma satar dukiyoyi.

    Hukumomi sun ce an gudanar da zanga-zanga 120, inda mafi yawansu suka gudana cikin lumana, sai dai guda 12 da suka rikiɗe zuwa tashin hankali.

    Lardin Western Cape ne ya fi yawan waɗanda aka kama, da mutum 215.

    An tura sojoji zuwa tsakiyar Johannesburg domin taimaka wa ’yansanda bayan rahotannin fashi da wawason shaguna, ciki har da a yankin Claremont da ke Durban.

    Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce mafi yawan zanga-zangar ta gudana cikin lumana. Masu zanga-zangar dai na zargin baƙi da ƙara rashin aikin yi da aikata laifuka, kuma sun yi alƙawarin ci gaba da gudanar da gangamin duk mako har sai an biya buƙatunsu.

  10. Iran ta ce za ta mayar da martani mai ƙarfi ga duk wata barazana

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce duk wata barazana da aka yi wa al'ummar Iran ko shugabanninta za ta fuskanci "martani cikin gaggawa kuma da ƙarfi."

    Ya bayyana hakan ne a martaninsa ga kalaman ministan tsaron Isra'ila, Yisrael Katz, wanda ya ce Isra'ila za ta kai hari da ƙarfi kan Iran idan ta sake harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila, tare da cewa sojojin Isra'ila na shirin gudanar da wani farmaki kan Iran.

    Araghchi ya ce yarjejeniyar da aka cimma a Islamabad a sarari take kuma kowa na iya duba abubuwan da ta ƙunsa.

    Ya kuma ce shugaban Amurka ya ɗauki alhakin tabbatar da cewa Isra'ila ta bi ƙa'idojin yarjejeniyar, yana mai ƙara da cewa idan Isra'ila ta kauce daga wannan tsarin, Iran za ta mayar da martani.

  11. Ba ma wasa da tsaron ƙasarmu da makamanmu - Iran

    ....

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Muƙaddashin ministan tsaron Iran ya ce ƙasar ba ta wasa da tsaronta da kuma makamanta, yana mai jaddada cewa Iran ba za ta taɓa tattaunawa ko yin sulhu kan ƙarfin tsaronta ba, musamman makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa.

    Majid Ibn al-Reza ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin X, bayan ganawa da mambobin Kwamitin Tattalin Arziki na Majalisar Dokokin Iran.

    Ya ce a yayin taron an jaddada cewa ƙarfin tsaron Iran, da shirinta na makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa, wani muhimmin ɓangare ne na tsaron ƙasar wanda ba sa wasa da su.

    Har ila yau, ya ce Iran za ta ci gaba da haɓaka waɗannan makamai ta hanyar amfani da ƙwarewa da albarkatun cikin gida.

    Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Iran da Amurka ke gudanar da tattaunawa ta kaikaice a ƙasar Qatar.

    Tattaunawar na mayar da hankali ne kan mashigar Hormuz da kuma batun sakin kadarorin Iran da aka ƙwace a ƙasashen waje.

  12. An zargi gwamnatin Habasha da sake tura sojoji zuwa gabashin Tigray

    Ƙungiyar TPLF ta zargi gwamnatin Habasha da sake tura sojoji daga yammacin Tigray zuwa gabashin yankin, matakin da ta ce zai iya ƙara tsananta rikici a yankin.

    A wani taron manema labarai da aka yi ranar 30 ga Yuni, shugabar ofishin TPLF, Fetlework Gebrezighiabher, ta ce duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Pretoria, gwamnatin na ci gaba da takurawa al’ummar Tigray, har ma ta zarge ta da kashe fararen hula.

    Tun da farko, TPLF ta ce gwamnati na kokarin mamaye yankin Tigray da sojoji tare da shirye-shiryen sake fara yaƙi, yayin da gwamnatin Habasha ta maida martani da cewa TPLF ce ke shirin tayar da rikici.

    A ɓangaren ƙasa da kasa, Tarayyar Turai da Amurka sun nuna damuwa kan ƙarin fargabar rikici, suna kira da a aiwatar da yarjejeniyar Pretoria gaba daya, sai dai TPLF ta yi watsi da wannan kira.

  13. Ɗalibai 35 da aka sace lokacin rubuta jarabawa na hannun ƴanbidiga - Ƴansanda

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴansandan Najeriya sun tabbatar da cewa aƙalla ɗalibai 36 tare da wani ma’aikacin makaranta guda ɗaya ne har yanzu ke hannun ƴan bindiga bayan da suka sace su a harin da suka kai ranar Litinin.

    Ƴanbindigar sun kai musu harin ne a yayin da suke rubuta jarabawar kammala makarantar sakandare ta NECO a wata da ke jihar Borno.

    Ƴansandan sun ce sun riga sun tantance adadin mutanen da aka sace, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin ceto su.

    Tuni dai aka kuɓutar da mutane 10, ciki har da mataimakin shugaban makarantar.

    An kai harin ne a garin Lassa da ke ƙaramar hukumar Askira Uba, inda ɗaliban ke tsaka da rubuta jarabawa.

    Harin na zuwa ne bayan wasu makamantan hare-haren a yankin, inda ake ci gaba da bincike a dazukan da ke maƙwaftaka domin gano inda waɗanda aka sace suke da kuma ceto su.

  14. Najeriya za ta nemi diyya daga Afrika ta Kudu

    ...

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta nemi a biya diyya kan dukiya da wuraren kasuwancin ‘yan ƙasarta da suka bari a Afirka ta Kudu yayin da ake mayar da su gida sakamakon hare-haren nuna ƙyamar baƙi.

    Muƙaddashin babban jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Alexander Ajayi ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da ya yi da kafar watsa labarai ta Channels da ke Najeriya, inda ya ce gwamnati ta fara tattara bayanai kan dukiyar da ƴan ƙasar suka bari, domin tuntubar gwamnatin Afirka ta Kudu kan yadda za a biya diyya.

    Ya ce an buƙaci ƴan Najeriyan da ke dawowa su rubuta cikakken bayanin kadarorinsu da suka hada da kantuna da motoci da sauran dukiya, yana mai cewa shirin ba zai tsaya ga mayar da su gida kawai ba, gwamnati na kuma da ƙudurin kare jarin ƴan kasarta.

    A gefe guda kuma, wasu karin ƴan Najeriya 271 sun isa filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas, bayan kwaso su daga Afirka ta Kudu, inda suka gargaɗi sauran ƴan kasa da su guji zuwa can.

    A jiya ne dai wasu ƴan Afirka ta Kudu suka gudanar da zanga-zangar ƙyamar baƙi bayan cikar wa’adin da aka ba ƴan ƙasashen waje da ba su da takaddar zama a ƙasar su fice, lamarin da ya ƙara tayar da hankula a ƙasar.

  15. Ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliya a sassan jihar Legas

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ruwan sama mai ƙarfi da aka shafe sa’o’i ana yi a ranar Talata ya haddasa ambaliya a sassan birnin Legas da ke kudancin Najeriya, lamarin da ya janyo tsaiko ga zirga-zirgar jama’a tare da jefa mazauna da dama cikin matsala.

    Gwamnatin Jihar ta bukaci mazauna su kwantar da hankulansu, tana mai cewa tana sa ido kan halin da ake ciki da kuma kokarin shawo kan matsalar ambaliyar da ta sake kunno kai a makonnin baya-bayan nan.

    Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na jihar, Tokunbo Wahab, ya bayyana cewa ruwan saman ya zo da tsananin yawa cikin kankanin lokaci, wanda ya haddasa cunkoso a magudanan ruwa tare da janyo ambaliya a yankuna kamar Victoria Island, Lekki, Ikeja, Gbagada, Mushin da Mafoluku.

    Ya kuma ce ba Legas kaɗai irin wannan ruwan sama mai ƙarfi ya shafa ba, domin an samu makamancin haka a wasu sassan Afirka da ma Arewacin Amurka.

    Gwamnatin ta kuma gargaɗi jama’a da su guji zubar da shara a magudanan ruwa da kuma yin gine-gine a wuraren da ke hana ruwa gudana domin rage illar ambaliya a nan gaba.

  16. Za a rufe Tehran ranar Talata saboda jana’izar Ayatollah Khamenei

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Iran ta sanar da cewa za a rufe babban birnin kasar, Tehran, a ranar Talata 6 ga watan Yuli, domin sauƙaƙa gudanar da jana’izar Ayatollah Ali Khamenei da kuma bai wa masu makoki damar fita daga birnin cikin sauki bayan halartar tarukan da za a gudanar.

    Mai magana da yawun gwamnatin, Fatemeh Mohajerani, ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin taimakawa wajen sauƙaka zirga-zirgar dubban mutanen da suka halarci jana’izar jagoran addinin ƙasar.

    Ta kuma bayyana cewa an ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar zaman makoki a faɗin Iran baki ɗaya.

    Ana sa ran binne Ayatollah Ali Khamenei a birnin Mashhad ranar Alhamis 8 ga watan Yuli.

    An tsara gudanar da tarukan jana’iza da alhini a biranen Tehran, Qom da Mashhad daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli.

    Haka kuma, za a gudanar da wasu tarukan tunawa da shi a biranen Bagadaza, Kazmin, Karbala da Najaf a ƙasar Iraq.

    Ayatollah Ali Khamenei ya rasu ne sakamakon hare-haren saman da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, inda suka kai harin a gidansa sai dai har yanzu ba a binne shi ba.

  17. Assalamu alaikum!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.