Waɗanda suka mutu a makarantar Indonesia sun kai 54

Asalin hoton, EPA
Adadin waɗanda suka mutu a ginin makarantar da ta rushe a ƙasar Indonesia, sun ƙaru zuwa 54, a cewar hukumomi.
Yayin da ake ci gaba da neman wasu gwammai.
Ɗaruruwan dalibai ne, mafiya yawansu maza 'yan shekara goma sha ne, suka taru domin sallar jam'i, a makarantar kwana da ake koyar da ilimin addinin musulunci, Al Khoziny da ke gabashin Java, a lokacin da ginin ya rushe a ranar Litinin da ta gabata.
Lamarin ya faru ne yayin da ake ci gaba da ginin makarantar.
Hukumar kare bala'oi ta ƙasar ta ce, lamarin shi ne mafi muni da aka samu a wannan shekarar.
Ana sa ran masu ceto za su zaƙulo wasu mutum 13 da baraguzan ginin ya binne.
Masu bincike na neman gano musabbabin rushewar ginin. Yayin da wasu ke cewa ginin mai hawa biyu ya rufta ne saboda ba a yi mishi tushe mai ƙwari ba.



