Isra'ila ta tabbatar da kai hari a Syria
Sojojin Isra'ila sun tabbatar da kai hari yankin sojin Syria, bayan ƙungiyar da ke sa ido a yaƙin ƙasar ta ce sun kai sama da hare-hare ta sama 20 a sassan ƙasar.
Wakilin BBC ya ce kafar yaɗa labaran Syria ta ce ababen fashewa sun tashi a arewaci birnin Damascus da wajen kusa da birnin Hama.
An kuma ba da rahotannin wasu hare-haren a Latakia da arewa maso yammacin yankin Idlib.
Wannan na zuwa ne bayan hari ta sama da Isra'ilar ta kai kusa da fadar shugaban ƙasa a birnin Damacus a jiya Juma'a.