Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu
A madadin sauran abokan aiki, muke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni dangane da muhimman batutuwa da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/05/2025.
Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello Diginza
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu
A madadin sauran abokan aiki, muke cewa mu kwana lafiya.
Jam'iyyar PAP mai mulki a Singapore ta lashe babban zaɓen ƙasar karo na 14 a jere, inda ta lashe duka kujerun majalisar dokokin ƙasar, in ban da guda 10.
Sakamakon zaɓen ya zai wa firaministan ƙasar, Lawrence Wong damar kafa sabuwar gwamnati mai rinjayen gaske.
Jam'iyyar PAP ta kasance tana jagorantar ƙasar tun bayan samun ƴancin kan ƙasar daga Birtaniya a 1965.
Yayin da ake yaba mata kan nasara a fannin tattalin arziki, ana sukar gwamnatin kan zargin taƙe haƙƙin bil'adama da ƴancin albarkacin baki.
Ɗaruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zangar goyon bayan dimokraɗiyya a Mali, da ke ƙarƙashin mulkin soji.
Jam'iyyun siyasar ƙasar ne suka kira zanga-zangar saboda da fargabar rushe su.
A ranar Laraba ne hukumomin Mali suka bayyana aniyar janye dokar da ke kula da jam'iyyun siyasa a ƙasar.
A shekarar da ta gabata ne shugaban mulkin sojin ƙasar, Kanal Assimi Goita ya alƙawarta mayar da ƙasar kan tafarkin dimokraɗiyya, to amma daga baya ya jingine aniyar tasa.
Tun bayan juyin mulkin ƙasar a 2020 da 2021 an yi ta haramta shirye-shiryen siyasa a ƙasar
Ko a shekarar da ta gabata ma sai da aka tuhumi shugabannin jam'iyyun siyasa 11 da yunƙurin yi wa ƙasar bi-ta-da ƙulli.
Firaministan Yemen da duniya ta amince da gwamnatinsa ya ajiye muƙaminsa, saboda abin da ya kira kasa wanzar da ikonsa.
Gwamntin Ahmed bin Mubarak ta koma birnin Aden mai tashar jiragen ruwa fiye da shekara 10 da suka gabata, lokacin da mayaƙan Houthi suka ƙwace iko da babban birnin ƙasar, Sanaa, da wasu biranen ƙasar masu yawan jama'a.
Yaƙin basasar da aka ɗauki lokaci mai tsawo ana tafkawa ya kasa murƙushe mayaƙan Houthi.
Mista Mubarak ya ce ya sauka daga muƙaminsa ne bayan fuskantar ''matsaloli masu yawa''.
A baya-bayan na Amurka ta ƙara azama a hare-haren da take kai wa ƴantawayen Houthi a Yemen, a wani yunƙuri na dakatar da su daga kai hare-haren kan jiragen ruwa a Tekun Maliya.
An kwantar da shugaban Serbia, Aleksander Vucic, a asibiti, kwanaki kafin bulaguron da ake sa ran zai yi zuwa Rasha don halartar bikin shekara-shekara da ake yi don tunawa da kakkaɓe ƴan Nazi
Shugabannin Turai sun yi ta matsa lamba kan Mista Vicic ya soke bulaguron, to amma a baya ya dage cewa sai ya je.
Bayanai na cewa Firaministan Slavakia, Rober Fico na fama da rashin lafiya, lamarin da ya sa ake ake raɗe-raɗin shi ma ba zai halarci bikin da ya tsara zuwa birnin Moscow.
Tun da farko, Shugaban Ukraine, Volodymar Zelensky ya yi gargaɗin cewa ba zai tabbatar da tsaron shugabannin da za su ziyarci babban birnin na Rasha ba.
Ƙungiyar Hamas ta fitar wani bidiyo na biyu da ke nuna wani mutum da ake tunanin ɗan Isra'ila ne da take garkuwa da shi.
An nuna mutumin mai suna Maxim Herkin cikin wata hanyar ƙarƙashin ƙasa an ɗaura masa bandeji mai yawa a raunukan da ƙungiyar ta ce ya ji su ne sakamakon harin Isra'ila.
Mista Herkin na da shekara 35 a lokacin da Hamas ta yi garkuwa da shi a harin da aka kai wurin bikin kaɗe-kaɗe na Nova a watan Oktoban 2023.
Hamas na yawan fitar bidiyoyin Isra'ilawan da take garkuwa da su a wani mataki na ƙara matsin lambar da gwamnatin Isra'ila ke fuskanta a cikin gida, wani abu da gwamnatin ke bayyanawa a matsayin farfaganda.
Har yanzu akwai ragowar aƙalla Isra'ilawa 50 da ke hannun Hamas, yayin da aka yi imanin cewa 24 daga cikin na nan da ransu.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin ƙwato duka wurare da dazukan ƙasar da ƴanbindiga ke ɓuya, ta hanyar girke sabbin dabaru na zamani domin yaƙi da ta'addaci da ƴan fashin daji.
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga jagororin jihar Katsina a lokacin liyafar cin abincin dare da aka shirya masa a gidan gwamnatin jihar ranar Juma'a.
''Dangane da matsalar tsaro, matsala ce da ta addabi ƙasarmu', kuma na yi magana da sojoji, na tabbatar musu cewa za mu yi duk mai yiwuwa don kawo ƙarshen matsalar ƴanbindiga'', in Tinubu.
"Za mu samar da kayan aiki na zamani domin ƙwace duka dazukan ƙasarmu daga hannun miyagu, matsalar tsaro ta shafi duka Najeriya ne ba wani yanki ba, kuma mun sani cewa indai muna so ƙasarmu ta ci gaba to dole mu kawar da matsalar tsaro a Najeriya,'' in ji shugaban ƙasar.
Haka kuma Shugaba Tinubu ya tabbatar da tallafa wa rayuwar waɗanda ayyukan ta'addanci ya shafa
Ƙungiyar Likitoci ta Duniya ''Medecins Sans Frontieres'' ta ce an kai harin bom kan ɗaya daga cikin asibitocinta a Suda ta Kudu.
MSF ta ce an samu rahoton rasa rayukada raunuka a lokacin harin.
Ƙungiyar ta kuma ce harin ya lalata wani ɓangare na gidnin asibitin Old Fangak da ke jihar Jongei.
An kai harin ne kwana guda bayan shugaban sojojin ƙasar, Paul Majok Nang ya ɗora alhakin hare-hare da ake kai wa jiragen ruwa kan masu taar da ƙayar bayan da ke alaƙa da mataimakin shugaban ƙasar, Riek Machar.
Masu aiko da rahotonni sun ce akwai fargabar dawowar yaƙin basasa a ƙasar sakamakon rashin jituwa tsakanin shugaban ƙasar Salva Kiir da Msita Mr Machar.
Ƙungiyoyin kare hakƙin bl'adama na kira ga sojojin ƙasar su dakatar da hare-haren bom kan yankunan fararen hula.
An rantsar da shugaban ƙasar Togo, Faure Gnassingbé, a matsayin shugaban majalisar ministocin ƙasar - wani sabon muƙami mafi girma a ɓangaren zartarwa.
Hakan na zuwa bayan sauyi a kundin tsarin mulkin ƙasar, da ya kawo ƙarshen tsarin shugaban ƙasar, domin fara amfani da tsarin firaminista a ƙasar.
Ƴan'adawa na cewa an yi sauyin ne domin bai wa Mista Gnassingbe damar ci gaba sa kasancewa a kan mulki har abada.
A shekarar 2005 ne ya zama shugaban ƙasar, bayan ya gaji mahaifinsa, Gnassingbe Eyadema - da ya mulki ƙasar na kusan shekara 40.
Ƙungiyar Opec da ƙawayenta sun amince da ƙara yawan man fetur da suke fitarwa zuwa kasuwar duniya a watan Yuni, duk kuwa da karyewar farashin man a kasuwar duniya sakamakon raguwar buƙatarsa.
Farashin man fetur ya yi faɗuwar da ba a taɓa gani ba cikin watan Afrilu, inda aka sayar da gangar mai kan dala 60, bayan da Opec da ƙawayenta suka ayyana ƙara yawan man da suke haƙowa a watan Mayu.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato majiyar OPEC na bayyana cewa Saudiyya na buƙatar a ladabtar da mambobin ƙungiyar iraƙi da Kazakhstan saboda saɓa ƙa'idar yawan da da ƙungiyar ta amince su fitar.
A baya-bayan nan ne Dnald Trump ya yi kira ga ƙungiyar OPEC ta ƙara yawan man da take fitarwa.
A cikin wannan wata na Mayu ake sa ran Shugaba Trump zai ziyarci Saudiyya.
Wata kotu a Tunisia ta tura tsohon firaministan ƙasar, Ali Laarayedh zaman gidan kaso na shekara 34 bisa laifin ta'addanci.
Tsohon firaministan ya shiga sahun fitattun mutanen da aka ɗaure a ƙasar, a wani yanayi da masu suka ke kira da "ɗaurin wulaƙanci."
Ali mai shekara 69 a rayuwa yana cikin masu adawa da shugaba Kais Saied na ƙasar, kuma jagoran jam'iyyar Ennadha - wadda ta fi ƙarfi a majalisar ƙasar kuma take fafutikar yaɗa addinin Musulunci.
An tuhumi Laarayedh da wasu mutum shida ne da kafa wani sansanin ta'addanci tare da taimakon matasan ƙasar suna tafiya ƙasashen waje domin shiga ƙungiyoyin mayaƙa masu ikirarin jihadi a Iraqi da Syria.
"Ni ba mai laifi ba ne," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya kalato daga wasiƙar da ya rubuta zuwa ga babban mai shari'a.
A ranar Juma'a ne aka yanke masa hukunci, amma ya ce ɗaurin da aka yi masa ba ya rasa nasaba da siyasa.
Mubarak Mahmud matashin da da ya ƙirƙiri tsarin auna tsawon bishiya ta hanyar ɗaukar hoto da wayar salula da sauran bayanan da kake buƙatar sani game da bishiyar.
Matashin ya ce wannan zai sauƙaƙa wajen samun bayanai ga masu bincike.
A ƙarshe ya ba matasa shawarar cewa kowannensu na da wata baiwa da zai iya amfani da ita wajen inganta rayuwar al'ummar ƙasarsa.
"Ba mu damu da sayar da kayayyaki ga Amurka ba," in ji Hu Tianqiang a daidai lokacin da wani jirginsa na roba ke shawagi a saman kanmu.
Kantin Hu, mai suna Zhongxiang Toys, yana cikin babban kantin bayar da sarin kayayyaki a birnin Yiwu na ƙasar China.
A kasuwar akwai shaguna sama 75,000, kuma za a iya cewa akwai duk wani abu da ƴankasuwa suke buƙata. Za ka iya wuni ɗaya ba ka karaɗe ɓangare ɗaya na kasuwar ba.
Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya tafi ƙasar Gabon domin halartar bikin rantsar da zaɓaɓɓan shugaban ƙasar, Brice Clotaire Oligui Nguema.
Shettima zai wakilci shugaban Najeriya Bola Tinubu ne a taron bikin, wanda a yanzu haka yake ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar Katsina da ke arewacin ƙasar.
Nguema ya lashe zaɓen ƙasar ne da aka yi a watan Afrilun da ya gabata, bayan ya yi watanni yana mulkin riƙon-ƙwarya.
A wata sanarwar da mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce, "Mataimakin shugaban ƙasar koma Najeriya bayan bikin rantsuwar."
Mutuwar ɗaya ne daga cikin manyan matsalolin da ke ci wa yankin arewacin Najeriya tuwo a ƙwarya.
Matsalar ta zama gagaruma da ke shafar mutane da dama, kama daga matan da ake saki, zuwa iyayen matan da ma ƙananan yaran da iyayensu ke rabuwa, sakamakon halin da yaran kan faɗa a wasu lokuta, sakamakon rashin rayuwa da duka iyayensu
Matsalar na ci gaba da ɗaukar hankulan jama'ar yankin, lamarin da ya sa malamai da masana ke ta kiraye-kiraye magance matsalar.
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance, ya zargi hukumomin Jamus da sake gina katangar Berlin, bayan kiran jam'iyyar AFD da ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayi.
Mr Vance ya ce AFD ce jam'iyya mai yawan wakilci a yammacin ƙasar, amma wasu na neman rushe ta.
Kalaman na zuwa ne bayan sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce a ƙara wa hukumar leƙen asirin ƙasar ƙarfin sa ido kan ƴan adawa cin amanar ƙasa ne a fakaice.
Wakilin BBC ya ce hukumar leƙen asirin ƙasar ta ce jam'iyyar AFD na son hana mutane ƴancinsu na dimukradiyya, kuma hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar.
Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, ƴan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mata 25 a garin Kurmi na ƙaramar hukumar Maru
An ce dai an yi garkuwa da matan ne suna kan hanyar zuwa gidan bikin.
Haka ma wasu ƴan bindigar sun yi garkuwa da aƙalla mutum 19 yayin da suka raunata ƙarin wasu da dama, a garin Galadi da ke ƙaramar hukumar Tsafe, duk dai a jihar ta Zamfara.
Isra'ila ta sanar da sabon shirin rusau a yamma da gaɓar kogin Jordan da ta mamaye, a ci gaba da matakin da ta ce ta na ɗauka kan ƙungiyoyin Faladinawa masu ɗauke da makamai.
Wakilin BBBC ya ce taswirar baya-bayan nan da hukumomin Isra'ila suka fitar, ta nuna za a rushe sama da gine-gine 100 a sansanonin ƴan gudun hijira na Tulkarm da Nurul Shams.
Sanarwar Isra'ilar ta ce za a bai wa mazauna sansanonin wata uku don samun damar kwashe kayayyakinsu.
Tun daga watan Junairu kawo yanzu, sama da Falasɗinawa dubu 40 aka tilastawa ficewa daga gidajensu a sansano uku da sojin Isra'ila suka toshe a yamma da gaɓar kogin Jordan.
Gwamnan Neja Mohammed Umaru Bago ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa akwai saɓani mai girma tsakaninsa da mataimakinsa, Yakubu Garba, inda ya ce babu abin da ke tsakaninsu sai dai fahimtar juna da girmama juna.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya karɓi karramawar gwarzon ma'aikata a bikin Ranar Ma'aikata da aka yi a Minna.
"Wannan duk raɗe-raɗi ne kawai ake yaɗawa. Muna da fahimtar juna sosai da mataimakina, kuma babu abin da zai iya shiga tsakaninmu. Burinmu shi ne samun nasara, kuma za mu same ta," in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Bago ya samu rakiyar Sanata Mohammed Sani Musa ne, wanda yake wakiltar Neja ta Gabas a majalisar dattawa.
Sai dai ya ce wasu ayyukan masu muhimmanci ne suka sa mataimakinsa bai samu damar halartar bikin ba.
A Najeriya, hukumar kwastam ta ƙasar ta musanta zancen da ake yi cewa, wai za ta dawo da nau'in harajin nan na kashi huɗu cikin ɗari da ake cirewa na shigar da kaya cikin ƙasar, wanda ake kira ''FOB'', wanda aka ɗage aiki da shi a ƴan watannin baya.
Al'amarin da hukumar ta ce, ko da za a ci gaba da aiki da wannan haraji, sai an zauna da dukkan masu ruwa da tsaki, a tattauna da su.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar AbdulLahi Aliyu Maiwada ne ya yi BBC wannan ƙarin bayani, inda ya ƙara da ba zai yiwu a dawo da karɓar harajin ba ta bayan fage ba tare da an zauna an daddale tare da fahimtar juna ba.