Birtaniya ta soki jinkirin shigar da tallafi zuwa Gaza

Asalin hoton, EPA
Gwamnatin Birtaniya ta yi suka kan jinkirin shigar da tallafin jin kai zuwa Gaza, bayan sama da tantuna 1,100 da ta tura sun ɗauki fiye da shekara guda kafin su isa.
Sakatariyar harkokin waje, Yvette Cooper, ta ce duk da tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra’ila, har yanzu ana samun cikas wajen kai tallafin da Birtaniya ta biya, lamarin da ya ƙara taɓarɓarewar rayuwa a Gaza inda MDD ta ce mutane miliyan 1.5 na buƙatar mafaka cikin gaggawa kafin lokacin sanyi.
Tantunan wanda kowanne zai iya daukar iyali guda sun isa Gaza a ranar Litinin, kuma ana sa ran ƙarin wasu su isa a wannan makon.
Gwamnatin Birtaniya ta ce za su taimaka wa kimanin mutum 12,000 su samu mafaka a lokacin sanyi.
Cooper ta ce "jinkirin kai tallafi ba kamata ya ci gaba da ɗorewa ba, inda ta buƙaci buɗe dukkan hanyoyin shiga Gaza domin ingantaccen tallafi ya riƙa isa ba tare da tangarɗa ba."
Fiye da mutane miliyan 1.9 kimanin kashi 90 na al'ummar Gaza kenan sun rasa muhallansu tun bayan ɓarkewar rikicin Isra’ila da Hamas a 2023, in ji MDD.
Cooper ta ce "shigowar tantunan wani muhimmin mataki ne, amma akwai bukatar karin tallafi da kuma gaggawar sake gina Gaza.

