Ƙungiyar ISIS ta ɗauki alhakin harin da ya hallaka mutum aƙalla 30 a jihar Adamawa

Wasu ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutane ashirin da tara a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun shiga wani filin wasan ƙwallon ƙafa ne inda jama’a ke taruwa, kana suka buɗe wuta kan mai uwa-da-wabi.
Ofishin gwamnan jihar ya ce maharan sun shafe sa’o’i da dama suna harbin jama'a da ƙona gidaje, da babura da wuraren ibada.
A shekarun baya-bayan nan, yankin ya sha fama da hare-hare daga kungiyoyin ‘yan daba na cikin gida da kuma masu alaka da ISIS.
Wata sanarwa da kungiyar ta ISIS ta wallafa a shafinta, ta dauki alhakin kai harin.
Rahotanni na cewa an tura jami’an soji da ƴan sanda zuwa yankin domin daƙile yiwuwar sake kai wani harin.


