Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo maku rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/07/2023
Taƙaitattu
NAFDAC ta ƙwace haramtaccen maganin feshi na naira miliyan 20 a Sokoto
NCAA za ta hukunta kamfanonin jirgin sama da ba su mutumta ƙa'idar lokaci
Shugaba Biden ya ƙaddamar da taron NATO karo na 75
Shugaban Brazil ya yi kiran gudanar da zaɓe mai inganci a Venezuela
An gano ƙarin gawawwaki bayan harin Rasha a Ukraine
Za a ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza
NERC za ta hukunta kamfanonin rarraba lantarki kan karancin wuta a Najeriya
Rahoto kai-tsaye
Daga Badamasi Abdulkadir Mukhtar da Umar Mikail da Aisha Babangida
An ɗaure mutumin da aka samu da laifin cin mutunci ga shugaban Uganda
Wata kotun Uganda ta zartar wa wani mutum hukuncin ɗaurin shekara shida bayan kama shi da laifin cin mutunci ga Shugaban kasar Yoweri Museveni.
An sami Edward Awebwa da laifi ne bayan wallafa wasu bidiyo a kafar sada zumunta kuma daga cikin tuhumar da ake masa har da amfani da kalamai da aka alaƙanta da zargi ga uwar gidan shugaban da kuma ɗansa wanda shi ne kwamandan rundunar soji.
Kotun ta ce hukuncin zai iya zama darasi gare shi.
Ba shi ne na farko da da ke amfani da TikTok da aka zartar wa irin wannan hukuncin ba, inda ko a shekaru biyu da suka gabata an taba kama wani marubuci kan yin ɓatanci ga iyalan shugaban
An zartar wa ƴan fafutikar siyasa 40 ɗaurin rai da rai a Daular Larabawa
Asalin hoton, UAE MINISTRY OF JUSTICE
Wata kotu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yanke wa fiye da ƴan gwagwarmayar siyasa 40 hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samun su da hannu a laifukan ta'addanci.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce kotun ɗaukaka ƙara ta Abdu Dhabi ta samu mutanen da laifi saboda kafa wata ƙungiyar ta'addanci.
Ƙwararru daga Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun soki shari'ar da rahotanni suka ce ake yi wa mutane tamanin da huɗu.
Ɗaya cikinsu ya ce babu adalci a shari'ar saboda an hana waɗanda ake zargi tuntuɓar lauyoyinsu.
Tarayyar Turai ta ce ƙyamar Yahudawa ta ƙaru
Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Tarayyar Turai ta ce Yahudawa a yankin na ci gaba da fuskantar ƙyama da kyara musamma ma a intanet.
Hukumar ta faɗi haka ne bayan sabbin alƙalumman da ta fitar kan Yahudawa a ƙasashen Tarayyar Turai 13 da suka ƙunshi Jamus da Faransa da Austria da kuma Hungary.
An tattara alƙalumman ne kafin harin Hamas a Isra'ila na 7 ga watan Oktoban 2023, amma kuma rahoton ya ƙunshi bayanai daga hukumomin Yahudawa 12 a 2024.
An gudanar da binciken ne daga Janairu zuwa Yunin bara, kuma kashi 96 na waɗanda aka zanta da su sun ce sun fuskanci ƙyama a rayuwarsu.
Rahoton ya ce Yahudawa da dama sun ce suna rayuwa cikin ɗarɗar bayan harin Hamas.
Hukumar ta ce Yahudawan sun fi fuskantar cin zarafi da tsoratarwa kuma adadin ya ƙaru a dukkanin ƙasashen da aka gudanar da bincike.
An kama wani ƙunshe da macizai 100 a wandonsa a China
Hukumomin hana fasa kwabri a China sun kama wani mutum da ke ƙoƙarin fataucin macizai sama da 100 a cikin wandonsa.
An kama shi ne a lokacin da yake ƙoƙarin tsallakawa zuwa Hong Kong.
A lokacin da suke binciken aljihunsa ne suka fahimci cewa akwai micizai 104 cikin jikunan leda a rufe.
Galibinsu ƙanana ne, kuma wani bidiyon da jami'an kwastom na China suka fitar ya nuna yawan macizan.
A bara ma an taɓa kama wata mata tana ƙoƙarin fataucin macizai a rigar mama.
China dai na ɗaya daga cikin ƙasashen da aka fi fataucin dabbobi.
Asalin hoton, CUSTOMS CHINA
Ƴansanda sun kama wani da sassan jikin mutum a Abuja
Rundunar ƴansandan Abuja ta ce jami'anta sun kama wani ɗauke da sassan jikin mutum a yankin unguwar Lugbe.
Sanarwar da mai magana da yawun rundunar ta aika wa BBC ta ce an kama mutumin ne ranar Talata bayan samun bayanan sirri.
Hotunan da rundunar ta aika wa BBC sun nuna ƙwarangwal da ƙasusuwan jikin mutum.
"Da yana amsa tambayoyi mutumin ya ce ya tsinci sassan jikin ne a daji lokacin da yake farauta a Kuje, tare da cewa yana shirin sayar wa kan N600,000," a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, kwamishinan ƴansandan Abuja ya bayar da umarnin ƙaddamar da bincike domin gano sassan jikin mamacin da kuma wanda ke shirin saye.
Sannan binciken zai tantance ko wanda ake zargi "ya kashe wani ne domin fataucin sassan jikinsa, a matsayin wata hanyar kasuwanci."
Asalin hoton, Abuja Police
'Ƴan Boko Haram da dama sun miƙa wuya'
Asalin hoton, Other
Rundunar haɗin kai a Tafkin Chadi ta ce gwamman ƴan kungiyar Boko Haram ne daga kasar Nijar da Kamaru suka mika wuya ga rundunar tsaro ta hadaka da ke yankin tabkin Chadi.
"Mun samu adadin ƴan Boko Haram 69 da iyalansu da suka miƙa wuya daga farkon Juli zuwa shida shida ga watan na wannan shekarar," kamar yadda kakakin rundunar Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya shaida wa BBC.
Ya ce wasunsu da dama sun miƙa wuya ne da makamansu, kuma sun samu yawan masu miƙa wuyar ne sakamakon wani farmaki da suka ƙaddamar na fatattakar ƴan Boko Haram a yankin na Tafkin Chadi.
"Kuma suna miƙa wuya ne sakamakon toshe duk wata hanya da suke samun kayayyakin masarufi," a cewar kakakin rundunar.
Boko Haram dai ta daɗe tana addabar yankin Tafkin Chadi wanda ya haɗa ƙasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.
An fara aiwatar da tsagaita wuta a jamhuriyar Congo
Asalin hoton, AFP
Rahotanni daga gabashin jamhuriyar dimokuradiyyar Congo sun ce an fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta domin shigar da kayan buƙata da aka ƙulla tsakanin mayaƙan M23 da dakarun gwamnati, kwana biyar bayan ƙulla ta.
Amurka ce ta shige gaba wajen
Ana zargin ƙasashen Rwanda da Uganda masu maƙwabtaka da Congo da ɗaukar nauyin ƴan tawayen.
Amurka na fatan yarjejeniyar ta kai ga tsagaita wuta ta dindindin, amma rahotanni na cewa mayaƙan M23 za su iya ci gaba da ƙwace iko da wurare bayan wa'adin yarjejeniyar ya ƙare.
Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da shirin ta na janye jami'an ta masu aikin kwantar da tarzoma daga ƙasar.
Yadda Musulman Bosnia ke tunawa da kisan kiyashin da aka yi musu a 1995
Garin Srebrenica na Bosniya na fuskantar makoma mara tabbas yayin da yawancin matasa ke barin garin.
A karon farko a wannan shekara, za a gudanar da ranar 11 ga watan Yuli a matsayin ranar tunawa ta duniya don karrama maza da yara maza 8,000 da aka kashe a shekarar 1995, ta'asa mafi muni a Turai tun bayan yaƙin duniya na biyu.
Kisan kiyashin na Srebrenica, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi a matsayin kisan ƙare-dangi, ya kasance kololuwar yaƙin Bosnia, rikicin da ya barke bayan ballewar Yugoslavia a farkon shekarun 1990.
Abin da kuke son sani kan wasan Netherlands da Ingila
AU na jagorantar tattaunawa kan kawo ƙarshen yaƙin Sudan
Asalin hoton, reu
Tawagar Tarayyar Afirka za ta koma teburin tattaunawa a birnin Addis Ababa na Ethiopia da nufin nemo hanyar kawo ƙarshen yaƙin Sudan.
AU tana neman gudanar da tattaunawa da ta ƙumshi dukkan ɓangarori, amma a baya wata gamayyar fararen hula mai suna Tagadum ta ƙi yarda ta shiga tattaunawar.
Amma wani jami'in AU ya ce yana da yaƙinin cewa gamayyar za ta shiga tattaunawar a wannan karon.
Mohammed Ibn Chambas ya ce jam'ar Sudan rayuwa cikin matsanancin hali saboda yaƙin, wanda ya raba mutane fiye da miliyan takwas da muhallin su.
Ya ce akwai buƙatar mutane su jingine banbancin da ke tsakanin su domin neman ɓangarorin sun amince da tsagaita wuta.
Rundunar soji Isra'ila ta rarraba wasu takardun sanarwa da ke umartar Falasɗinawa su fice daga birnin Gaza.
Wannan ne karo na biyu da ake umartar mutane su fice daga birnin Gazar, tun bayan fara yaƙin.
Takardun sanarwar sun yi gargaɗin cewa birnin ya kusa zama cibiyar gwabza yaƙi, sun kuma bayar da bayanan wajen da Falasɗinawan za su iya komawa domin tsira.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tattaunawar tsagaita wuta wadda Amurka da Qatar da kuma Masar ke jagoranta.
Akwai kyakkyawar fatan cewa za a cimma tsagaita wuta, da kuma ceto mutanen da Hamas ke tsare da su.
Washington ta kuma yi gargaɗin cewa har yanzu akwai giɓi a tattaunawar.
NAFDAC ta ƙwace haramtaccen maganin feshi na naira miliyan 20 a Sokoto
Asalin hoton, Nafdac
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya ta ƙwato magungunan feshi da basu da inganci da na bogi da kuma waɗanda aka haramta shiga da su ƙasar da kuɗin su ya kai naira miliyan 20 a kasuwannin jihar Sokoto.
Sanarwar da NAFDAC ta fitar ta ce ta kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a safarar kayan.
Hukumar ta ce ta yi nasarar kamen ne bayan bincike da kuma aikin haɗin gwiwa a tsakanin jami'anta da sauran jami'an hukumomin hana safarar ƙwayoyi.
NAFDAC ta kuma ƙona katon-katon na wani maganin feshi mai suna Endocoton Super, wanda ke ɗauke da sinadarin da ke da illa ga lafiyar jama'a da kuma muhalli.
Kasuwannin da hukumar ta ce jami'anta sun kai samamen sun haɗa da tsohuwar kasuwa da kasuwar Kara da kuma babbar kasuwar Sokoto.
NCAA za ta hukunta kamfanonin jirgin sama da ba su mutumta ƙa'idar lokaci
Asalin hoton, INSTAGRAM/FLYAIRPEACE
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya, NCAA ta yi gargaɗin cewa za ta hukunta kamfanonin sufurin da ke yaudarar matafiya a kan lokacin tafiyar jirage.
Muƙaddashin daraktan hukumar, Chris Najomo, ya ce hukumar ba za ta lamunci rashin cika alƙawari da kuma kiyaye ƙa'idojin sufurin jirgin sama ba.
Ya yi gargaɗin cewa kamfanonin da suke saɓa ƙa'idojin za su fuskanci hukunci mai tsanani, kamar yadda doka ta yi tanadi.
Hukumar ta ce ta yi tanadi mai inganci domin sauƙaƙe yadda ake mallakar lasisin gudanar da kamfanonin jiragen sama a Najeriya, da kuma kaucewa kura-kuran baya.
“NCAA ta na fatan ganin hakan zai sa kamfanonin jiragen su tashi tsaye domin gudanar da ayyukan su yadda ya dace'' inji Chris Najomo.
NCAA ta jaddada cewa babu wani dalili da zai hana kamfanonin jiragen sama gudanar da ayyukan cikin tsari kamar yadda ake yi a sauran ƙasashen duniya.
Rasha ta yi alƙawarin sakin 'yan Indiya da ke aiki a cikin sojojinta
Asalin hoton, Getty Images
Rasha ta yi alƙawarin sakin dukkan 'yan ƙasar Indiya da ke aiki a cikin sojojinta, a cewar ma'aikatar harkokin wajen Indiya.
Wannan alƙawarin ya zo ne a ƙarshen ziyarar da firaministan Indiya Narendra Modi ya kai birnin Moscow, inda ya tattauna batun da shugaba Vladimir Putin.
Delhi dai na neman a sako 'yan Indiyawa, wadanda suka ce an yaudare su ne zuwa ƙasar Rasha bisa alkawarin ayyukan da ba na yaƙi ba a cikin sojoji, amma daga baya aka tilasta musu yin fada a Ukraine.
Aƙalla Indiyawa hudu aka kashe a yaƙin da ake yi.
A ranar Talata, sakataren harkokin wajen Indiya, Vinay Kwatra ya ce akwai 'yan Indiya kusan 35 zuwa 50 a cikin sojojin Rasha, wadanda 10 daga cikinsu tuni aka dawo da su gida.
Ya ƙara da cewa a yanzu ƙasashen biyu za su yi ƙoƙarin dawo da sauran mutanen.
Indiyawan da suka maƙale a Rasha sun ce wasu wakilai ne suka yaudare su da neman kudi da fasfo na Rasha.
Yawancin waɗannan mutanen sun fito ne daga iyalai matalauta waɗanda aka yi musu alƙawarin aiki, wani lokaci a matsayin "masu taimako" a cikin sojojin Rasha.
A farkon wannan shekarar, ma'aikatar ta bukaci "dukkan 'yan Indiya da su yi taka tsantsan tare da nisantar irin wannan rikicin".
Sanarwar haɗin gwiwa da Indiya da Rasha suka fitar bayan tattaunawar tasu ta ce ɓangarorin biyu sun tanadi wasu muhimman abubuwa guda 9 na hadin gwiwa da suka haɗa da makamashin nukiliya da magunguna.
Shugabannin sun kuma ce za su yi niyyar haɓaka kasuwancin ƙasashen biyu zuwa dala biliyan 100 nan da shekarar 2030.
NERC za ta hukunta kamfanonin rarraba lantarki kan karancin wuta a Najeriya
Asalin hoton, TCN
Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya NERC, ta gargadi kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da cewa za su fuskanci hukunci idan ba su yi amfani da aƙalla kashi 95 cikin 100 na makamashin da aka ware musu domin samar da wutar lantarki ga jama'a a kowanne wata ba.
Wannan wani ɓangare ne na sabon umarnin hukumar NERC kan tsarin sa ido kan ayyuka rarraba wutar lantarkin.
Hukumar ta ce duk kamfanin rarraba wutar lantarki da ya kasa cika wannan ƙofa na samar da wuta zai ga raguwar kashi 5 cikin 100 a cikin kuɗin gudanarwa da ayyukan su na kwata na gaba.
NERC ta gabatar da ma'auni bakwai masu mahimmanci (KPIs) don tantance ayyukan kamfanonin.
NERC ta jaddada cewa hukunta kamfanonin ya zama dole don kiyaye tsarin kasuwa da ɗorewar kudi.
Hukumar ta kuma ce rashin mayar da hankali da kuma martani a kan ƙorafe-ƙorafen mabuƙaci zai haifar da cin tara a kullum daga ₦1,000 zuwa 10,000.
NERC ta ƙarar da cewa rashin bin ka'ida na kuma iya haifar da korar jami'an da ke da alhaki.
Shugaban NERC, Sanusi Garba, ya sanya hannu kan wannan umarni ne a ranar 5 ga Yulin 2024, inda ya jaddada ƙudirin hukumar na tabbatar da tsauraran matakan tsaro.
A yau ake sa ran za a ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza da kasar Qatar ke shiga tsakani, da sako karin Isra'ilawan da Hamas ta yi garkuwa da su tun watan Oktoban bara.
Wakilan Amirka da na Isra'ila za su gana da manyan jami'an gwamnatin Qatar da Masar.
Fadar White House ta ce ana tattaunawar ne a cikin sirri da ake fatan ta kai ga cimma yarjejeniya mai inganci.
Alamu sun nuna Hamas ta rage wasu daga cikin bukatunta ga Isra'ila kafin ta amince da yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.
Sai dai ta ce ci gaba da kai hare-hare da sojin Isra'ila ke yi a zirin Gaza babbar barazana ce ga tattaunawar.
A kalla Falasdinawa 29 ne rahotanni suka tabbatar da mutuwarsu a jiya Talata, bayan hari da sama da Isra'ila ta kai wata makaranta da iyalai Falasdinawa ke fakewa.