Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/01/2025.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Isiyaku Muhammed, Ahmad Bawage, Usmna Minjibir, da Umar Mikail

  1. Za mu karɓe mulki a hannun APC a 2027 – PDP

    PDP

    Asalin hoton, PDP

    Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya ta PDP ta ce za su samu ƙarin gwamnoni a zaɓen 2027, ƙari a kan guda 12 da take da su a yanzu, sannan ta karɓe mulkin ƙasar.

    Jagororin jam'iyyar ne suka bayyaka haka a lokacin da suka kai ziyara ga Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Ma'ajin jam'iyyar, Alhaji Ahmed Yayare ne bayyana hakan a madadin jam'iyyar, inda ya ce yanayin yadda ƙasar ke fama da taɓarɓarewar tattalin arziki ne ya sa PDP za ta samu sauƙin samun nasara a 2027.

    Ya ƙara da cewa, "babu abin da zai hana PDP karɓe mulkin ƙasar. Yanzu APC ba ta abin da za ta yi kamfe da shi saboda yunwa da talauci ya yi a ƙasar. Idan suka fita kamfe sai an jefe su."

  2. Kama shugaban ƙasar Koriya ta Kudu da aka tsige ya ci tura

    Koriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu bincike a Koriya ta Kudu sun ce alhakin aiwatar da sammacin kama Shugaban Ƙasar Yoon Seok-yeol a halin yanzu ya rataya ne a wuyan ƴansanda bayan masu binciken sun gaza kama shi a cikin kwanaki ukun da suka gabata.

    Shugaban wanda aka tsige na ci gaba da kasancewa a cikin gidansa, inda jami'an tsaron fadar shugaban ƙasa da gungun magoya bayansa ke ba shi kariya.

    A wata sanarwa da ya fitar shugaban hukumar tsaron ƙasar Park Jong-joon, ya ce ba shi da niyyar barin masu bincike su cafke shugaban.

    Ya ce Ko da yake majalisa ta tsige Shugaba Yoon, shugaban ƙasa ne wanda jama'a suka zaɓa, kuma yana da ƴancin samun tsaro kamar yadda doka ta tanada.

  3. Matar da aka sauya wa hanta ta warke garau

    Burtaniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata ƴar Birtaniya, wadda ta kasance ta farko da aka yi wa tiyatar sauya hanta bayan fama da cutar kansa ta warke garau.

    Matar ƴar shekara 32 mai suna Bianca Perea ta sha fama da cutar kansa na kusan shekara huɗu, wadda har ta shafi hantarta, har ta kai zai yi wahala a iya yi mata tiyata.

    Sai dai daga bisani an yi aikin na sauya hantar a watan Fabarairun bara, sannan yanzu likitoci sun tabbatar da cewa ta warke garau.

  4. Yarjejeniyar barin dabbobi su shiga gonaki a Nijar ta fara aiki

    A jihar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar an sanar da amincewa da buɗe gonaki ga makiyaya domin su shiga da dabbobinsu don cin karmami da sauran tarkacen gona a wannan makon.

    Dama dai akwai wata yarjejeniya tsakanin manoma da makiyaya ta bai wa makiyaya damar shiga gonaki bayan girbi don yin kiwo na wani lokaci kafin a sake yin shuka.

    A baya dai lamarin ya sha haifar da rashin fahimtar juna tsakanin ɓangarorin biyu, har sai da ta kai ga mahukunta shiga tsakani tare da amincewa da wannan yarjejeniya.

    Shugaban hukumar kula da tsarin filayen karkara da dokokin da ke kare su a jihar ta Maraɗi Malam Galo Badaje ya bayyana wa BBC cewa ana gudanar da tsarin ne tare da sahhalewar manyan ɓangarori biyu da abin ya shafa, wato manoma da makiyaya, inda gwamnati ke ƙoƙarin bunƙasa lamarin domin haɓɓaka tattalin arziƙin al'umma.

  5. An wanke mata ƴan Najeriya uku daga zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Saudiyya

    Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun wanke wasu ƴan Najeriya mata guda uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

    Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ce ta fitar da sanarwar hakan, a jiya Lahadi, inda ta ce an kama su ne a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 2024 a birnin Madina.

    Sanarwar ta ce kotu ta wanke su ne bayan wata goma ana shari'a ana tafka shari'a.

    An kama matan ne bayan an kama wasu mutum biyu ƴan Najeriya da miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da hodar ibilis, inda aka zargi matan da taimakon su wajen shigar da ƙwayoyin zuwa ƙasar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa an miƙa matan ga ofishin jakadancin Najeriya da ke Saudiyya, kuma tuni aka fara shirye-shiryen mayar da su ƙasarsu Najeriya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. 'Ƙungiyar su Shekarau za ta koma jam'iyyar siyasa'

    Shekarau

    Asalin hoton, Shekarau Facebook

    Ƙungiyar League of Northern Democrats (LND) wadda wasu ƴan siyasa daga arewacin Najeriya suka kafa ƙarƙashin shugabancin tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ta fara yunƙurin zama jam'iyyar siyasa domin fuskantar zaɓen shekarar 2027.

    Ƙungiyar ta zargi jam'iyya mai mulki ta APC da babbar jam'iyyar adawa ta PDP da gazawa wajen ciyar da Naeriya gaba, sannan ta buƙaci ƙungiyoyin kudancin ƙasar da su shigo su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ceton ƙasar.

    A wata sanarwa da jaridar Daily Trust ta ruwaito daga ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar, Dr Umar Arɗo, ya ce ƙungiyar ta LND za ta kawo sauyi tare da sake dawo da martabar ƙasar.

    Ya ce rashin ingancin gwamnati ne ya jefa ƙasar cikin ƙangin talauci da rashin tsaro da rashin tabbas.

    Sai dai tuni jam'iyyar APC ta mayar da martani, inda daraktan watsa labaranta, Alhaji Bala Ibrahim ya ce su dai ko gezau, domin a cewarsa, rikiɗewar ƙungiyar zuwa jam'iyyar siyasa ba barazana ba ce ga jam'iyyar APC a zaɓen 2027.

  7. Dattawan Arewa sun koka da kwamitin da aka kafa domin duba ƙudurin haraji

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu Facebook

    Ƙungiyar dattawan Arewacin Najeriya ta koka kan rashin shigar da ƙwararu a kwamitin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci ofishin ministan shari’a da na majalisar ƙasar su kafa domin sake duba ƙudurorin cikin tsanaki.

    Ƙungiyar ta ce bai kamata gwamanti ta nemi a kawo sauye-sauye cikin gaggawa kan batun dokar harajin ba, inda ta ce aiwatar da dokar ba tare da tuntuɓa yadda ya kamata ba zai yi wa jihohin yankin illa.

    Farfesa Abubakar Jika Jiddere ɗaya ne daga cikin shugabanin ƙungiyar ya ce kawo yanzu sun kamala yi wa dokar harajin duba na tsanaki kuma sun haɗa rahotonsu, wanda haka yasa suke ganin dole a sake nazari kan ƙudurin.

  8. Assalamu alaikum

    Jama'a masu bibiyar wannan shafin na labaran kai-tsaye, muna muku barka da sake saduwa a wannan safiya ta Litinin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su X da Facebook da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.