Saibari ba zai buga wa Moroko wasa ba saboda rauni
Morocco za ta rasa babban ɗan wasa Ismael Saibari yayin da take neman ɗaukar fansa kan Faransa sakamakon doke ta da ta yi a wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta 2022.
Saibari ya zura kwallo a kowanne wasan rukuni, inda ya zura kwallaye a wasan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Brazil, da nasara 1-0 kan Scotland da kuma nasara 4-2 dkan Haiti.
Ɗan wasan mai shekaru 25, wanda ya tashi daga PSV Eindhoven zuwa Bayern Munich a wannan bazarar, shi ya zura ƙwallon da ta ba shi nasara a kan Netherlands a wasansu na ƙarshe na ƴan 32.
Duk da haka, Saibari ya fuskanci matsala bayan mintuna 22 sakamakon raunin da ya samu a cinyarsa a lokacin da Morocco ta doke Canada da ci 3-0 a wasan ƙarshe na ƴan 16. "Yana fama da rauni amma ina fatan ba ƙarshen gasarsa ba ke nan," in ji kocin Morocco Mohamed Ouahbi.

