KAI TSAYE, Ko Moroko za ta iya taka wa Faransa birki?

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Zagayen kwata-fainal
France versus Morocco kick off 21:00
Faransa
21:00
plays
Moroko

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Haruna Ibrahim Kakangi

  1. Saibari ba zai buga wa Moroko wasa ba saboda rauni

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Morocco za ta rasa babban ɗan wasa Ismael Saibari yayin da take neman ɗaukar fansa kan Faransa sakamakon doke ta da ta yi a wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta 2022.

    Saibari ya zura kwallo a kowanne wasan rukuni, inda ya zura kwallaye a wasan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Brazil, da nasara 1-0 kan Scotland da kuma nasara 4-2 dkan Haiti.

    Ɗan wasan mai shekaru 25, wanda ya tashi daga PSV Eindhoven zuwa Bayern Munich a wannan bazarar, shi ya zura ƙwallon da ta ba shi nasara a kan Netherlands a wasansu na ƙarshe na ƴan 32.

    Duk da haka, Saibari ya fuskanci matsala bayan mintuna 22 sakamakon raunin da ya samu a cinyarsa a lokacin da Morocco ta doke Canada da ci 3-0 a wasan ƙarshe na ƴan 16. "Yana fama da rauni amma ina fatan ba ƙarshen gasarsa ba ke nan," in ji kocin Morocco Mohamed Ouahbi.

  2. Moroko za ta nemi ɗaukar fansa kan faransa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasa tsakanin Faransa da Morocco ba wasan kwata-fainal na gasar cin kofin duniya ba ne kaɗai.

    Ga magoya bayan Morocco da dama, ba tu ne na neman ɗaukar fansa. Shekara huɗu da suka gabata, Faransa ta kawo ƙarshen gasar cin kofin duniya ta ban mamaki da Moroko ta yi a Qatar, inda ta doke ƙasar Afirka da Larabawa ta farko da ta kai wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya.

    A yau Alhamis a Boston za su sake haɗuwa, amma a wannan karon Moroko za ta zo ne a matsayin ƙasar da ta cancanci samun gurbi a wasan ƙarshe na gasar.

    Tun bayan gasar Qatar, tawagar ƴan ƙasa da shekara 20 ta Morocco ta lashe gasar cin kofin duniya na wannan rukuni, yayin da babbar tawagar ƙasar ta haura zuwa matsayi na shida a jerin ƙasashen duniya na FIFA. Alamun da ke nuna cewa ƙokarin da hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ke yi na bunƙasa ɓangaren wasan matasa na haifar da sakamakon da ake buƙata.

    Don haka tambayar da ake yi ba wai kawai ko Moroko za ta iya doke Faransa ba ne.

    Tambayar ita ce ko tawagar da ta girgiza duniya a Qatar za ta iya tabbatar da cewa ƙoƙarin da ta yi ba shine kololuwa ba, amma tushe ne da za a ɗaura a kai.

    A Qatar, Maroko ta kafa tarihi. A Boston, tana da damar da za ta tabbatar da cewa yanzu ma aka fara.

  3. Ko Moroko za ta iya maimaita irin rawar da ta taka a Qatar?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da nasarar da Moroko ta samu na kaiwa zagayen kusa da na ƙarshe a Qatar abin mamaki ne, wannan tawagar da ke fafatawa a Amurka ta fi ƙarfin a yi mata kallon ta ƴan wasa marasa ƙarfi.

    A ranar Asabar da ta gabata, zakarun gasar ƙasashen Afirka (wanda Senegal ke jiran ɗaukaka ƙara bayan wasan ƙarshe mai cike da ce-ce-ku-ce a watan Janairu), sun sanya ƴan wasa huɗu ne kacal daga cikin waɗanda suka sha kashi a wasan kusa da na ƙarshe da suka kara da Faransa shekaru huɗu da suka gabata.

    Suna wasa da kuzari da kuma ƙarfin hali, kuma za su zama ƙalubale mafi tsanani da Faransa ta fuskanta zuwa yanzu a gasar bana.

    A ɓangaren ƙasar da ta zo ta biyu a gasar 2022, uku ne kawai daga cikin ƴan wasan da suka buga wasan kusa da na ƙarshe suka fara wasan da Faransar ta yi nasara kan Paraguay a ranar Asabar. Fitowar William Saliba, ɗan wasan tsakiya kuma gwarzon ɗan wasa Michael Olise, suna daga cikin sabbin abubuwan da Didier Deschamps ya yi tun daga lokacin.

    Kylian Mbappe har yanzu shi ne gwarzon ɗan wasa kuma zai ci gaba da ƙoƙarinsa na doke Lionel Messi na Argentina wajen samun kyautar takalmin zinare da kuma lambar gwarzon ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a tarihin gasar cin kofin duniya.

    Abin la'akari a nan shi ne rabin adadin rashin nasarar da Faransa ta yi a gasar cin kofin duniya a cikin wannan ƙarnin sun zo ne a hannun ƙasashen Afrika (Uku daga cikin shida).

    Moroko ba ta yi rashin nasara ba cikin wasanni 34 a jere da ta fafata a baya ba, amma ba ta taɓa nasara kan Faransa ba wadda ta lashe wasannin bakwai a jere, yayin da ta yi nasara a wasanni 11 cikin 12 da ta buga.