Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Za a yi karon battar ƙarfe tsakanin Portugal da Spain

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Zagaye na biyu
Portugal versus Spain kick off 20:00
Portugal
20:00
plays
Spain

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Haruna Ibrahim Kakangi

Yadda za a yi karon battar ƙarfe tsakanin Protugal da Spain

Ana jiran fafatawa tsakanin ƴan wasa masu cin zamani daban-daban a ranar Litinin a lokacin da tauraron ƙwallon ƙafa Cristiano Ronaldo zai fafata da matashin ɗan wasan ƙwallon ƙafa Lamine Yamal a wasan zagaye na 16 na gasar cin kofin duniya inda za a kece raini tsakanin Portugal da Spain.

Wasan hamayya na yankin iberia ya zama tamkar maimaici ne na wasan ƙarshe na gasar UEFA Nations League ta bara, wanda Portugal ta lashe ta hanyar doke zakarun Turai Spain a bugun fenariti.

Duk da haka, ba Portugal ce ake sa ran za ta yi nasara a wannan wasan da za a yi a Dallas ba.

Bayan samun tsallakawa zuwa zagaye na ƴan sha shida Ronaldo da tawagarsa na fuskantar ƙalubale wajen iya tunkarar wannan tawagar matasan ta Spain.

Tun bayan da suka tashi babu ci a wasan farko, Spain ta ƙara ƙarfi a gasar bana kumayanayin wasansu tare da yadda suke iya tsare gida da kyau ya sa an fara kyautatawa tawagar zaton samun damar ƙetarawa zuwa zagayen kwata fainal a karon farko cikin shekaru 16.

Yadda ƙasashen biyu suka kai zagayen ƴan 16

Portugal ta zo ta biyu a rukunin J da maki biyar, inda ta lallasa Uzbekistan sannan ta yi canjaras sa Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da Colombia. A zagayen ƴan 32, ta yi nasara a kan Croatia a wani wasa da ke cike da taƙaddama, inda ta yi nasara da ci 2-1.

Spain ta ja ragamar rukunin H da maki bakwai, inda ta doke Saudi Arabia da Uruguay, sannan ta yi canjaras babu ci da Cape Verde. A zagaye ƴan 32, ta yi nasara a kan Austria da ci 3-0.

La Roja ba ta rashin nasara a wasanni 34 da ta buga a baya ba (W25 D9), wanda hakan ya sa ta kusa karya tarihinta na tsawon wasanni 35 ba tare da ta sha kashi ba, wanda ta kafa daga watan Fabrairun 2007 zuwa watan Yunin 2009.

Gasar Ronaldo ta ƙarshe

A lokacin da yake da shekaru 41, Ronaldo, shi ne ɗan wasan da ya fi tasiri tawagar ƴan wasan Portugal, ba don saboda ƙwarewarsa a filin wasa kaɗai ba, har ma da matsayin da ya ke da shi a ƙasar baki ɗaya . Duk da cewa har yanzu abokan hamayya na buƙatar ba shi kulawa ta musamman a filin wasa saboda ƙwarewa da kuma hazakarsa, za a iya cewa Ronaldon da aka sani a shekarun baya, ba shi ne na yanzu ba.

Kafin a fara gasar, ana ta raɗe-raɗi kan makomarsa, inda gasar cin kofin duniya ta 2026 za ta iya zama ta ƙarshe da zai buga. Yayin da Ronaldo - ɗan wasa na biyu mafi shekaru a gasar bana - ya yi watsi da tambayoyi game da abin da zai biyo baya, ƴar uwarsa ta ce zai yi ritaya daga bugawa ƙasa a ƙarshen gasar cin kofin duniya ta bana.

Wannan ya sa duka wasannin zagayen kifa-ɗaya-ƙwala na Portugal suka kasance masu matuƙar muhimmanci- domin idan suka sha kashi, hakan zai iya kawo ƙarshen wasan Ronaldo a matakin ƙasa da ƙasa.

Ronaldo ya lashe kofuna da dama a tsawon shekaru da ya yi yana taka leda, amma idan Portugal ta sha kashi a hannun Spain, jerin nasarorinsa ba za su cika ba saboda rashin lashe gasar cin kofin duniya.

Ko wannan ce gasar da Yamal zai haska?

Bayan raunin da ya samu a cinyarsa, wanda ya yi barazanar kawo cikas ga irin rawar da Lamine Yamal zai taka a gasar cin kofin duniyarsa ta farko, ɗan wasan gefen mai shekaru 18 ya farfaɗo kuma a hankali ya fara jan hankalin jama'ar a Arewacin Amurka.

Lambar yabon gwarzon ɗan wasa da ya samu a wasan da Spain ta yi nasara a kan Austria a karon farko a zagayen kifa-ɗaya-ƙwala a gasar ya nuna tasirin matashin mai hazaka, shekaru biyu bayan ya nuna ƙwazon da ya taimaka wa Spain lashe gasar Euro 2024.

Ya zuwa yanzu, Yamal ya ci ƙwallo ɗaya kacal, yayin da Mikel Oyarzabal ke kan gaba a jerin masu zura ƙwallaye a tawagar da ƙwallaye huɗu. Spain dai tana harin lashe gasar kofin duniya ta biyu a tarihinta, shekaru 16 bayan ta lashe ta farko a Afirka ta Kudu a shekarar 2010.

Yadda wasanni suka kaya tsakanin ƙasashen biyu

Babu wani muhimmin bambanci tsakanin Portugal da Spain a karawa biyar da suka yi a baya a manyan gasanni, inda kowacce ta samu nasara sau ɗaya, sauran wasannin uku kuma aka yi canjaras.

Wannan ya haɗa da karawarsu ta baya-bayan nan a gasar cin kofin duniya, inda suka tashi ci 3-3 a shekarar 2018, wasan da Ronaldo ya ci ƙwallo uku rigis.

A tarihin karawa tsakaninsu, ƙasashen sun fafata sau 41; inda Spain ta yi nasara sau 18, Portugal kuma sau bakwai, yayin da aka yi canjaras sau 16.

Portugal za ta samu ƙwarin gwiwa daga nasarar da ta samu kan Spain—duk da cewa ta hanyar bugun fenariti ne—a karawarsu ta baya-bayan nan a wasan ƙarshe na gasar UEFA Nations League a watan Yunin 2025.