Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 2 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

  • Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
  • An kashe sojoji a musayar wuta da ƴanbindiga a Zamfara
  • Mutum 80 da aka sace a jihar Kaduna sun koma gida
  • An gurfanar da mutanen da ake zargin hannu a kisan gillar Yelwata
  • An shirya kama ni a harbe ni a yunƙurin juyin mulkin da aka yi - Janar Musa
  • Falasɗinawa sun fara tsallaka iyakar Rafah bayan shekar biyu a rufe
  • Yadda maciji ya kashe matashiyar mawaƙiya ƴar Najeriya a Abuja
  • Sheikh Usman Kusfa Zaria ya rasu
  • Su wane ne shugabannin Boko Haram da ISWAP a yanzu?

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Mutum 80 da aka sace a jihar Kaduna sun koma gida

    ...

    Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce mutum 80 daga cikin masu ibada da aka sace sun koma gidajensu lafiya, makonni bayan aukuwar lamarin.

    Mutanen na daga cikin mutum 177 da aka yi garkuwa da su daga coci uku a Kurmin Wali, wani yanki dake Kajuru a arewacin jihar Kaduna.

    Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Mansur Hassan, ya shaida wa BBC cewa mutanen sun tsere ne a ranar da aka sace su, a lokacin da ’yan bindigar ke ƙoƙarin kwashe su zuwa wani wuri.

    Ya ce bayan tserewar, sun ɓuya a wasu ƙauyuka na kusa tsawon makonni, inda suka jira har sai sun ga yanayin wurin ba matsala kafin su koma gida.

    DSP Mansur ya ce an tantance mutanen tare da kuma duba lafiyarsu sannan daga bisani aka haɗa su da iyalansu.

    Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutum 86 da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutanen.

    Harin na Kurmin Wali na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke addabar Najeriya, musamman a jihohin arewa, inda ake fama da hare-haren ’yan bindiga da sace-sacen mutane da kashe-kashe.

    Hukumomi sun sha bayyana cewa suna ƙara tsaurara matakan tsaro da haɗa kai da al’umma domin daƙile irin waɗannan hare-hare.

  2. Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe kwamandan Boko Haram na biyu a Sambisa

    Soji

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wani babban kwamanda a kungiyar Boko Haram da kuma wasu 'yan kungiyar 10 a samamen da ta kai a jihar Born da ke arewa maso gabashin kasar.

    Cikin wata sanarwa data fitar, rundunar ta ce Abu Khalid shi ne babban kwamandan Boko Haram na biyu a dajin Sambisa.

    Ta ce ya taka rawa wajen kitsa hare hare da dama da mayakan kungiyar suka kai a yankin.

    Najeriya dai ta jima tana fama da matsalar hare haren masu ikirarin jihadi inda har abin ya kai ga an samu wasu 'yan bindiga da ke satar mutane don karbar kudin fansa a ƙasar.

  3. Falasɗinawa za su fara tsallaka iyakar Rafah bayan shekara biyu a rufe

    Gaza

    Asalin hoton, Khames Alrefi/Anadolu via Getty Images

    A yau ne Falasɗinawa za su fara tsallaka iyakar Rafah da ke tsakanin zirin Gaza da kuma Masar, wadda ta kasance a rufe kusan shekara biyu bayan da sojojin Isra'ila suka ƙwace ɓangaren yankin Gaza.

    Sake buɗe mashigar Rafah da aka daɗe ana jinkiri wani muhimmin ɓangare ne a yarjejeniyar tsagaita wuta ta shugaba Trump a Gaza.

    Wakiliyar BBC ta ce rahotanni sun ce Isra'ila ta ce a kowacce rana marassa lafiya 50 tare da ƴanuwansu bibbiyu ne za su tsallaka iyakar, sannan kuma wasu mutum 50 daga cikin waɗanda suka bar Gaza a lokacin yaƙi ne za a barsu su shigo Gazan.

    Dubban Falasɗinawa marassa lafiya da masu rauni ne ke jiran su bar Gaza domin fita su nemi magani.

  4. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.