Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon Morocco: Najeriya ta kai zagaye na biyu da maki tara
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku bayanai kan wasan Uganda da Najeriya da na Tanzaniya da Tunisia a gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 da ake yi a Moroko.
Taƙaitattu
- Afcon 2025: Wasan karshe rukuni na uku tsakanin Uganda da Najeriya
- Ko Tunisia za ta doke Tanzaniya ta kai zaaaagaye na biyu a Afcon a Morocco
- Morocco ta ja ragamar teburin farko da Mali zuwa zagaye na biyu
- Masar da Afirka ta Kudu sun kai zagayen tawaga 16 a Afcon a Morocco
- Angola za ta san matsayinta ko za ta samu gurbin shiga zagaye na biyu
- Latsa nan domin samun labarin wasanni a tasharmu ta WhatsApp
- Ranar Asabar za a ci gaba da karawar zagaye na biyu a Afcon a Morocco
- Za ku iya tafka muhawara kai tsaye a BBCHausa Facebook
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
Wasu karin kokarin Najeriya a Afcon, Afcon Morocco 2025
- Super Eagles ta zura ƙwallo a raga a wasa tara baya a Afcon - wasan da ba ta ci ƙwallo ba shi ne a zagayen ƴan 16 da Tunisia ta doke ta a 2021.
- Haka kuma ta kan zura ƙwallo a raga a wasa takwas baya a karawar cikin rukuni a Afcon, rabon da ta kasa cin ƙwallo a wasan karshe a cikin rukuni tun 2019 da ta yi rashin nasara 2-0 a hannun Madagascar.
- Tun daga 2010 Najeriya ta ci ƙwallo takwas da ka a Afcon, Kamaru ce kan gaba a wannan bajintar mai 11 da kuma Ivory Coast mai 10.
- Victor Osimhen ya ci ƙwallo na biyu a Afcon a wasan Tunisia - ta farko da Equatorial Guine a 2023 da suka tashi wasa 1-1 a karawar farko a cikin rukuni.
- Dukkan ƙwallayen da Osimhen ya ci Ademola Lookman ne ke bashi su da yake ci da kai.
- Osimhen ya ci ƙwallo shida a wasa biyar baya a dukkan karawa a Najeriya.
- Ƙwallon da Ademola Lookman ya ci da bayar da biyu aka zura a raga a karawa da Tunisia ya zama na biyu da yake da hannun a cin ƙwalo uku a wasa ɗaya tun bayan ƙwazon Odion Ighalo a wasa da Kamaru a 2019 (ya zura biyu a raga ya kuma bayar da ɗaya aka ci).
- Kenan Lookman ya zura ƙwallo biyar a raga a AFCON.
- A wasa tara da Lookman ya yi, yana da hannu a cin ƙwallo takwas, wanda ya zura biyar a raga ya bayar da uku aka ci.
- An ci Najeriya ƙwallo a kowanne wasa huɗu baya a Afcon - wasan karshe da ta yi ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba tun 1-0 da ta doke Angola a kwata fainals a 2023.
Ƴan Tunisiya 11 da za su kara da Tanzaniya, Afcon Morocco 2025
Ƴan wasan Tanzaniya 11 da za su fuskanci Tunisiya
Karin kokarin Tunisiya a gasar ta kofin Afirka, Afcon Morocco 2025
Idan har Tunisiya ta kai zagayen gaba zai zama karo na 15 kenan za ta buga wasanin yan 16.
An yi waje da Tunisia a karawar cikin rukuni a 2023, rabon da ayi waje da ita a gasa biyu a jere daga cikin wasannin rukuni tun 1982 da kuma 1994.
A gasar Afcon biyar baya da suka halarta, sau daya ne aka yi waje da ita a zagayen cikin rukuni, shi ne a 2023.
Kwallon farko da Super Eagles ta ci Tunisiya ita ce ta 100 da aka zura a ragarta a tarihin Afcon.
Kenan Tunisiya ta zama ta biyu da aka ci kwallo 100 ko fiye da haka a Afcon bayan Ivory Coast.
Karin nasarorin Uganda a fafatawar Afcon, Afcon Morocco 2025
- Idan har Uganda ba ta doke Najeriya ba, za ta yi ban kwana da gasar Afcon karo na shida ba tare da cin wasa ba da ya haɗa a gasar 1968 da 1974 da 1976 da kuma 2017.
- Idan kuma har ta kai zagaye na biyu zai zama karo na uku kenan bayan 1978 da kuma 2019.
- Dukkan ƙwallo biyu da Uganda ta ci daga ƴan wasan da suka shiga canji ne da ya haɗa da wadda Denis Omedi ya zura wa Tunisia da ta Uche Ikpeazu da ya ci Tanzania.
- Denis Omedi yana da hannu a ƙwallo biyun da Uganda ta ci, wanda ya zura ɗaya a ragar Tunisia, shi ne ya bayar da wadda aka ci Tanzania.
- Omedi ya shiga wasa biyu a canjin ƴan wasa yana da hannu a ƙwallo biyun da Uganda ta zura a raga.
- Allan Okello ya nemi ragar Tanzani sau biyar, shi ne kan gaba a wannan ƙwazon a wasa ɗaya a Afcon a kasarsa.
- Uganda ta kai hari shida zuwa ragar Tanzania da cin ɗaya daga ciki.
- An zura ƙwallo huɗu a ragar Uganda daga hari bakwai da aka kai mata a Afcon a Morocco.
Kokarin da Super Eagles take yi a Afcon, Afcon Morocco 2025
- Ta lashe wasa biyu a jere a cikin rukuni da doke Tanzania da Tunisia.
- Tuni ta kai zagayen ƴan 16 a gasar cin kofin Afirka da ake yi a Morocco.
- Wannan shi ne karo na 16 a jere da Najeriya ta kai zagaye na biyu a Afcon.
- Rabon da ta kasa kaiwa zagaye na biyu a Afcon tun 1982.
- Wannan shi ne karo na 19 da Najeriya take haura zagaye na biyu daga karawar rukuni a Afcon
- Babu kasar da ta kai Super Eagles yawan kaiwa zagaye na biyu a Afcon fiye da Najeriya.
- Wasan da ta ci Tunisia shi ne nasara ta 35 da Najeriya ta yi a cikin rukuni a Afcon daga karawa 59 da rashin nasara 10 daga ciki, Masar ce kan gaba da yawan nasara a karawar rukuni mai 41.
- Kan yi nasara a karawar cikin rukuni a wasa huɗu baya har da cin wasa biyu a 2023 da doke Ivory Coast 1-0 da kuma Guinea Bissau da kuma nasara biyu a gasar da ake yi a Morocco.
- Dukkan wasannin tana yin nasara ne da rarar ƙwallo ɗaya tsakani.
- Karawar cikin rukuni da ta yi nasarar cin ƙwallo fiye da ɗaya ita ce a kan Guinea-Bissau da ta ci 2-0 a 2019.
- Idan har Najeriya ta yi nasara a kan Uganda, zai zama ta lashe dukkan karawa uku a cikin rukuni a karon farko tun bayan 2021.
Bajintar da Tanzaniya ke yi a wasannin cin kofin Afirka, Afcon Morocco 2025
Ta fara wasan bana a Afcon da rashin nasara 2-1 a hannun Super Eagles da kuma tashi 1-1 da Uganda a karawar cikin rukuni na uku.
Har yanzu Tanzania ba ta ci wasa ba daga 11 da ta buga a Afcon, wadda tasha kashi karo bakwai da canjaras hudu daga ciki.
Idan har ba ta yi nasara ba ranar Talata za ta zama ta hudu da ta kasa cin wasa daga karawa 12 ko fiye da hakan a Afcon, bayan Mozambique karawa 16 da Benin wasa 15 da kuma Guinea-Bissau mai fafatawa 12.
A tarihin wasan karshe a cikin rukuni a Afcon ta buga fafatawa uku da rashin nasara daya da canjaras biyu.
Ba a doke ta ba a wasan karshe a cikin rukuni a Afcon karo biyu baya, wadda ta tashi 1-1 da Ivory Coast a 1980 da kuma 0-0 da Jamhuriyar Congo a 2023.
Wasan bayan nan da ta yi rashin nasara a karawar karshe a rukuni shi ne 3-0 da Algriya ta ci a 2019.
Sau nawa aka kara tsakanin Uganda da Super Eagles?
Jimilla sun kara sau takwas tsakaninsu a dukkan fafatawa. Uganda ta yi nasara huɗu, Najeriya ta ci wasa biyu da canjaras biyu
Haka kuma an haɗa rukuni tare da Uganda da Najeriya a wasan neman shiga gasar cin kofin Afirka na 1994 da kuma na 2008.
A wasa huɗu da za su kara kenan gida da waje Najeriya ta yi nasara biyu, Uganda ta ci ɗaya da canjaras ɗaya - Kuma Super Eagles ce kan kai bante zuwa gasar.
Wasan baya-bayan nan da suka haɗu shi ne na sada zumunta ranar 20 ga watan Nuwamba da aka tashi canjaras a Asaba a jihar Delta a Najeriya.
Kawo yanzu a wasa uku ba a doke Uganda ba a karawa da Najeriya, wadda ta yi nasara biyu da canjaras ɗaya.
Wasan karshe da Super Eagles ta ci Uganda a Afcon a wasan neman shiga gasar 2008 ta ci 1-0 ranar 24 ga watan Maris 2007 a filin MKO Abiola a Abeokuta, inda Nwankwo Kanu ne ya zura ƙwallon a raga a minti na 73.
Ƙwazon da Tunisiya ke yi a gasar Afcon
Ta fara gasar bana da yin nasara 3-1 a kan Uganda daga baya ta sha kashi 3-2 a hannun Super Eagles a wasa na biyu a rukuni na uku.
Karon farko da ta yi rashin nasara a Afcon duk da cin kwallo biyu da ta yi tun bayan doke ta da Kamaru ta yi 3-2 a kwata fainal a 2008.
Kafin shan kashi a hannun Najeriya, Tunisiya ta yi karawa tara a Afcon ba tare da an doke ta ba da zarar ta ci kwallo biyu ko fiye da hakan daga ciki ta lashe wasa takwas da canjaras daya.
Wasa takwas ta yi nasara a jere da zarar ta ci kwallo biyu ko fiye da haka daga baya ta yi rashin nasara a hannun Najeriya.
Ta kasa cin wasa na uku a cikin rukuni a karawa uku baya a Afcon daga ciki ta tashi 0-0 da Mauritania a 2019, sannan ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Gambia, da kuma tashi 0-0 da Afirka ta Kudu a 2023.
Wasan da ta ci na karshe a cikin rukuni shi ne a 2017, inda ta ci Zimbabwe 4-2.
Nasarorin da Uganda ke yi a wasannin Afcon, Afcon Morocco 2025
- Ta fara da rashin nasara a hannun Tunisia, sannan ta raba maki da Tanzania.
- Kenan ta buga wasa biyar a Afcon ba tare da nasara ba, aka dke ta uku da canjaras biyu.
- Wasan bayan nan da ta ci a Afcon shi ne nasara 2-0 a hannun Jamhuriyar Congo a 2019.
- Ana zura mata ƙwallo a raga a wasa biyar baya a Afcon, karawar da ƙwallo bai shiga ragarta ba tun wasan farko a cikin rukuni a 2019.
- Tarihin da take take da shi a wasa na biyu a cikin rukuni a Afcon shi ne ta yi fafatawa shida da nasara ɗaya da canjaras ɗaya aka doke ta huɗu daga cikinsu.
- Rabon da ta yi nasara a wasan karshe a cikin rukuni tun bayan da ta ci Morocco 3-0 a 1978.
- An kuma doke ta wasa na uku a karawar cikin rukuni a 1968 da 1974 da 1976 da kuma 2019.
- Wasan da ba a doke ta ba a wasan karshe a cikin rukuni shi ne a 2017 da ta yi 1-1 da Mali.
- Ta sha kashi a wasan karshe a cikin rukuni a 2019 da Masar ta doke ta 2-0.
Ko Najeriya za ta doke Uganda a wasa na uku a cikin rukuni?, Afcon Morocco 2025
Uganda da Najeriya za su fuskanci juna a karo na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka, bayan da za su kara a fafatawa ta uku-uku a rukuni na uku ranar Talata a Complex Sportif de Fes.
Wasa tilo da suka fuskanci juna a Afcon shi ne a zagayen daf da karshe a 1978, inda Uganda ta yi nasarar cin Najeriya 2-1
A karawar da suka yi a 1978 a daf da karshe, Uganda ta fara cin ƙwallo ta hannun Abdulla Nasur a minti na 11 daga baya Najeriya ta farke ta hannun Martins Eyo a zagaye na biyu.
Sai dai daf a tashi ne Phillip Omondi ya ci wa Uganda na uku da ya kaita zagayen gaba.
Tanzaniya da Tunisiya wa zai kai zagaye na biyu a Afcon, Afcon Morocco 2025
Filin wasa na Stade Prince Moulay Abdellah Olympique Annexe a Rabat zai karbi bakuncin wasan karshe a rukuni na uku tsakanin Tanzania da Tunisia ranar Talata.
Dukkansu tawagogin na neman gurbin kai wa zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirka da ake yi a Morocco.
Wannan shi ne karon farko da za su fafata tsakanin Tanzania da Tunisiya a Afcon.
A wasan baya da suka kara a neman shiga Afcon na 2021, Tunisiya ce ta yi nasara a wasan farko 1-0 a Rades ranar 13 ga watan Nuwambar 2020, inda Youssef Msakni ya ci kwallon.\
A wasa na biyu a Dar Es Salam ranar 17 ga watan Nuwambar 2020 suka yi 1-1, kuma Saïf-Eddine Khaoui na Tunisiya ne ya fara cin kwallo a minti na 11 daga baya Feisal Salum na Tanzania ya farke a minti na 48.
Tunisia ce ta samu gurbin Afcon a 2021, yayin da Tanzania ta zama yar kallo.
Wasa tsakanin Tanzaniya da Tunisiya
Wannan shi ne karo na hudu da Tanzaniya za ta kece raini da tawaga daga Arewacin Afirka a Afcon, kuma duk rashin nasara ta yi a uku baya - Masar ta ci 2-1 a 1986 da Aljeriya a ta doke ta 3-0 a 2019 da rashin nasara a hannun Morocco a 2023.
Idan har Tanzaniya ta kai zagaye na biyu zai zama a karon farko, bayan da ta kasa kai bante zuwa zagayen yan 16 a Afcon a 1980 da 2019 da kuma 2023.
Afirka ta Kudu ta yi ta biyu ta kai zagayen ƴan 16 a Afcon, Afcon Morocco 2025
Oswin Appollis ne ya zura kwallo a bugun fenareti a cikin mintuna 10 na karshe, wanda ya bai wa Afirka ta Kudu nasarar doke Zimbabwe 3-2 a wasan da suka yi a Marrakech ranar Litinin.
Hakan ya sa ta kare a mataki na biyu a teburi a rukuni na biyu, ta kuma yi waje da takwararta daga Kudancin Afirka daga gasar Afcon da Morocco ke shiryawa.
Afirka ta Kudu ta kammala a mataki na biyu a rukuni da maki shida da tazarar daya kacal tsakani da Masar, wadda ita ce ta ja ragamar rukuni.
Ita kuwa Angola ta yi ta uku da maki biyu, za ta jira ko hakan zai sa ta kai zagaye na biyu daga tawaga hudu da za a dauka da suka yi na uku a cikin rukuni da maki mai kyau.
Mali ta kai zagayen ƴan 16 bayan canjaras da Comoros
Mali da Comoros sun tashi ba ci a gasar cin kofin Afirka a rukunin farko da suka kara ranar Litinin a Casablanca.
Da wannan sakamakon Mali ta kai zagayen yan 16 kai tsaye, an kuma yi waje da abokiyar hamayyarta daga Afcon na bana.
Mali ta kare a mataki na biyu a rukunin farko da maki uku, bayan canjaras a wasa uku, biye da mai masaukin baki, Morocco mai maki bakwai daga karawa uku.
Comoros, wadda ta kare a mataki na uku mai rarar kwallaye biyu da ake binta, kenan ba ta daga cikin tawaga hudun da za a zaba, domin shiga wasannin zagaye na biyu
Amma dai Mali za ta kara da duk wadda ta yi ta biyu a rukuni na biyu inda ranar Talata ake sa ran sanar da wadda za ta kara da ita - amma dai ana hasashen Tunisia ce.
Sai dai Mali za ta buga wasan zagayen gaba ba tare da Amadou Haidara ba, saboda jan katin da aka yi masa a karawa da Comoros ranar Litinin kan cewa ya yi keta mai muni.
Mai masaukin baƙi Morocco na fatan ci gaba da taka rawar gani a Afcon, Afcon Morocco 2025
Dan wasan gaban Morocco, Ayoub El Kaabi ne ya ci kwallo biyu, yayin da gwarzon nan mai taka leda daga tsakiya Brahim Diaz ya kara daya a raga , yayin da masu masaukin baki a gasar AFCON suka doke Zambia da ci 3-0 a ranar Litinin, sun kuma kare a saman teburi a rukunin farko.
Morocco ta kammala wasa uku a cikin rukuni da maki bakwai, gaba da Mali da ke matsayi na biyu da maki uku.
Bayan da ta fara gasar cikin shakku — ta fara da yin nasara da kyar da karamar kasar Comoros, sannan ta yi kunnen doki 1-1 da Mali a ranar Juma’a — a wasan karshe na uku a cikin rukuni, Morocco ta nuna da gaske take yi, tana daga cikin tawaga 24 da ake hasashen za ta iya lashe kofin.
Da wannan sakamkon an yi waje da Zambia a gasar bana, bayan da ta kare a matakin karshe da maki biyu kacal.
Masar ta kai zagayen gaba duk da hutar da manyan ƴan wasanta, Afcon Morocco 2025
Masar ta hutar da manyan yan wasanta, amma ta ci gaba da wasa ba tare da an doke ta ba a gasar cin kofin nahiyar Afirka, wadda ta tashi 0-0 da Angola - kenan ita ce ta farko a teburin rukuni na uku da maki bakwai.
Tun kan take wasan Masar ta kai zagaye na biyu, hakan ya sa ta canja yan wasa 11 daga wadanda suka ci Afirka ta Kudu 1-0 ranar Juma'a a karawa ta biyu a rukuni na biyu, inda Mohamed Salah da Omar Marmoush suka huta.
Angola ta kare a mataki na uku a rukunin, sannan za ta jira ta ji ko za ta samu damar kaiwa zagaye na biyu na yan tawaga 16 daga cikin hudun da za a zaba daga wadanda suka kare a mataki na uku da maki mai kyau.
Bayan da aka ci Zambia, sannan Comoros ta tashi 0-0 a wasan rukunin farko, kenan watakila ta bai bante idan aka ci Uganda da Tanzania ranar Talata.
Aubameyang ya gama buga Afcon ya koma Marseille, Afcon Morocco 2025
Pierre-Emerick Aubameyang ya kammala buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Morocco, bayan da ya koma Faransa a ranar Talata kenan ba zai buga wa Gabon wasan karshe ba a gasar.
Bayan shan kashi a wasa biyu a rukuni na shida a hannun Kamaru da Mozambique, Gabon ta fice daga gasar duk da akwai wasa daya da ya rage mata, wanda za ta fafata da mai rike da kofin, Ivory Coast, a Marrakech ranar Laraba.
Mai shekara 36, an sa ran cewa wasa da Ivory Coast zai kasance na karshe da zai yi wa kasarsa a shekaru 16 yana wakiltarta, sai dai yanzu haka ya koma ƙungiyarsa ta Olympique de Marseille.
Tsayuwar rukuni na huɗu, Afcon Morocco 2025