Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/08/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Putin ba zai min wargi ba - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Amurka Donald Trump ya ce ba don shi ne shugaban Amurka ba, da yanzu shugaban Rasha Putin ya mamaye Ukraine baki ɗaya.

    Trump ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar wato White House, inda ya ƙara da cewa ba zai laumci wargi ba.

    "Ni ne shugaban Amurka, don haka Putin ba zai min wargi ba," in ji Trump a lokacin da suke shirye-shiryen ganawa da Putin a Alaska.

    Trump ya ce tun a farko ganawar ce zai fahimci inda Putin ya dosa, domin a cewarsa, "gawanar ba za ta ɗauki lokaci mai tsawo ba."

    Ya ce maƙasudin ganawar ita ce a buɗe ƙofar tattaunawa domin samar da yarjejeniyar da za ta kai ga tsagaita wuta a Ukraine.

    Daga wannan tattaunawar ce za a samu damar janyo shugaban Ukraine ciki domin a ci gaba da tattaunawa tare har a samar da maslaha.

    "Idan tattaunawar ta yi kyau, zan kira Zelensky shi ma sai mu haɗu, amma ina fargaba da kashi 25 cewa tattaunawar ba za ta yi nasara ba."

  2. Peter Obi ya buƙaci magoya bayansa su zaɓi ADC a zaɓukan cike gurbi

    Peter Obi

    Asalin hoton, Peter Obi

    Tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya a Jam'iyyar Labour, Peter Obi ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri'a a Najeriya, musamman masoyansa na ƙungiyar Obidient da su zaɓi jam'iyyar ADC ne a zaɓukan cike gurbi da za a yi a gobe Asabar.

    Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce, "a game da zaɓukan da za a yi a gobe Asabar, 16 ga watan 2025 domin cike gurbin wasu kujeru a jihohi 16 na Najeriya, tunda jam'iyyar LP ba ta da ƴantakara saboda kotu ta hana sanadiyyar rikice-rikicen da ke cikin jam'iyyar, ina kira ga masoyana da su su zaɓi jam'iyyar haɗaka ta ADC a jihohinsu."

    Wannan jawabin na Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara game da yunƙurin haɗakar siyasa, inda ake tunanin manyan jam'iyyun hamayya za su iya haɗuwa a guri ɗaya domin fuskantar Tinubu a zaɓe mai zuwa.

    Za a zaɓen ne a jihohi 16 a Najeriya, inda za a yi zaɓen cike gurbi na sanatoci biyu, da majalisar wakilai biyar da majalisar jiha guda 9 a jihohi daban-daban.

  3. Gwamnatin Mali ta kama wanda ake zargi da yi wa Faransa leƙen asiri

    Mali

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a ƙasar Mali mai mulkin soja sun ce sun kama wani Bafaranshe da ake zargi da yi wa sojojin Faransa leƙen asiri.

    Gidan talabijin ɗin ƙasar ya nuna hotonsa, tare da na wasu manyan jami'an ƙasar Mali da aka kama a kwanakin baya bisa zargin shirya juyin mulki.

    Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ya ce sojoji sun daƙile wannan makirci ne sakamakon ƙwarewar da suka nuna tare da sa ido kan tsaroo.

    Gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta kuma zargi ƙasashen waje da ƙoƙarin tada zaune a ƙasar.

    Rahotanni sun ce fiye da jami'ai hamsin cikin harda janar-janar biyu aka kama a cikin makoni biyu da suka gabata.

  4. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'atu babbar rana daga sashen Hausa na BBC, inda za mu cigaba da kawo muku labaran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su Facebook da X da Instagram da m zaurenmu na Whatsapp domin karanta wasu labaran da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.