Rufewa
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/08/2025.
Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov da mai bai wa Shugaba Putin shawara kan harkokin ƙasashen waje, Yuri Ushakov za su kasance tare da Putin a ɗakin ganawarsa da Trump, kamar yadda kakakin fadar Kremlin, Dmitri Peskov ya bayyana.
Lavrov da Ushakov ƙwararrun jami'an diplomasiyya ne da ke tsara wa Rasha manufofinta na ƙasashen waje.
Lavrov ya shafe fiye da shekara 20 yana jagorantar ma'aikatar harkokin wajen Rasha, yayin da Ushakov - wanda a baya shi ne kadancan Rasha a Amurka - ya shafe fiye da shekara 10 a matsayin mashawarcin shugaban ƙasa.
Shugaba Trump da takwaransa Vladymir Putin sun sha hannu bayan saukar a filin jirgin Alaska.
Shugabannin biyu sun yi tafiya a kan jan kafet da ak shimfiɗa daga bakin kowane jirgi sinda suka haɗu da juna a tsakiya.
Manyan shugabannin duniyar sun gaisa da juna yayin da suka ɗauki hoto a gaban ƴan jarida.
Shugaban Rasha, Vladimir ya sauka a Alaska cikin jirgin sama ƙirar Anchorage domin ganawa da takwaransa na Amurka a yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Ana sa ran shugabannin biyu za su gana a wani mataki na yunƙurin kaso ƙarshen yain Ukraine.
Ɗaskin a Trump da Putin za su gana zai samu ƙarin mahalarta daga tawagar shugaban Amurka.
Sakatariyar yaɗa labaran fadar White House Karoline Leavitt ta faɗa wa manema labarai cewa tawagar Trump da za ta shiga gawanar ta ƙunshi sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio da jakadan Trump na musamman Steve Witkoff.
Haka ma a tattaunawar huldar dangantaka tsakanin ƙasashen da za a gudanar bayan ganawar Arco Ruboi da sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent, da sakateren kasuwanci Howard Lutnick da sakateren tsaro Pete Hegseth da shugabar ma'aikatan fadar Susie Wiles za su halarta.
Jirgin sojin saman Amurka da ke ɗauke da Shugaba Trump ya sauka a Alaska domin ganawarsa da Putin.
Shugaban na Amurka na tare da wasu ƙusoshin gwamnatinsa, da suka haɗa da sakataren harkokin waje, Marco Rubi da jakadan fadar White House na musamman, Steve Witkoff da darakta leƙen asirin ƙasar, John Ratcliffe.
Mista Trump na ƙoƙarin ganawa da Putin don yunƙurin yin sulhu a yaƙin da Rasha ke yi da Ukraine.
Ana sa ran shugabannin biyu za su gana a sansanin Elmendorf-Richardson da misalin ƙarfe 8:30 agogon Najeriya.
Wannan ne karon farko da manyan shugabannin duniyar za su gana tun bayan da Trump ya koma fadar White House a karo a biyu.
Adadin mutanen da suka mutu a Pakistan sakamakon ambaliya cikin kwana guda, ya kai fiye da 200.
Ruwa kamar da bakin ƙwarya - wanda ya janyo ambaliya da zafarewar ƙasa ne - ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen a arewa maso yammacin ƙasar.
Wani jirgi mai saukar ungulu da ke aikin ceto a yankin ya yi hatsari, kuma mutane biyar da ke ciki duk sun mutu.
Masana kimiyya sun ce ɗumamar yanayi ne ke ƙara ta'azzara hatsarin samun ambaliya.
Hukumomi a Sudan sun yi gargaɗin cewa fararen hula na ta mutuwa sakamakon yunwa a kudancin Kordofan.
Sojoji da mayaƙan RSF na ci gaba da gwabza yaƙi a cikin makonnin baya bayan nan, wanda ya hana mutane yin noma.
Wani ɗan siyasa a ƙasar mai suna Siddiq Tower ya shaidawa BBC cewa an yi wa birnin ƙawanya tun watan Mayu.
Ya ce an kulle manyan hanyoyin da ke kudancin Kordofan, kasuwanni da shaguna yanzu duk babu abinci.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce zai bai wa Ukraine damar zaɓin ko za ta tattauna da Rasha kan batun musayar yankuna.
Mista Trump ya shaida wa manema labarai da ke cikin jirgin shugaban ƙasa na Air force one hakan a hanyarsa ta zuwa Alaska domin yin ganawa mai muhimmanci da shugaban Rasha Vladimir Putin.
Gabanin ganawar, shugabannin ƙasashen Turai da na Ukraine sun buƙaci shugaba Trump kada ya amince da wata yarjejeniya kan yankunan Ukraine ba tare da jin ta bakin Kyiv ba.
Mista Trump ya ce ganawar ta yau za ta iya share fagen yin ganawa ta biyu da shugabannin ƙasashen biyu, wanda ya ce shi ne ya fi muhimmanci.
Al'ummar unguwar Sharada da ke cikin ƙaramar hukumar Birni a jihar Kano, sun bijiro da wasu dokoki 29 domin tsaftace halayyar mutane da tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu.
Daga ciki dokokin akwai dokar hana zance ko hirar dare tsakanin sauraryi da budurwa da ma hana zance a cikin mota sannan ka da masoya su wuce ƙarfe 10 dare suna zance.
Wannan matakin, a cewar mahukuntan yankin, ya fito ne sakamakon damuwar da ake fuskanta kan taɓarɓarewar tarbiyya da ƙaruwar matsalolin tsaro, da kuma rashin bin ƙa'idojin al'ada a tsakanin matasa masu neman aure.
Jagoran ƙungiyar Hezbollah ya gargaɗi gwamnatin Lebanon kan cewa matsa wa ƙungiyar ta ajiye makamanta nan da ƙarshen shekara, zai iya jefa ƙasar cikin yaƙin basasa.
Naim Qassem ya ce shirin, wanda ya biyo bayan matsin lamba daga Amurka, kamar miƙa wa Isra'ila Lebanon ne.
Kafin yaƙin da aka yi tsakanin Hezbollah da Isra'ila a bara, ana hasashen ƙungiyar mai goyon bayan Iran na da makaman da suka fi na sojin Lebanon.
Duk da tsagaita wutar da aka yi a watan Nuwamba, Isra'ila ta ce za ta ci gaba da kai hari kan Hezbollah har sai ta ajiye makamanta baki ɗaya.
Kafin zaɓen cike gurbi da za a gudanar a gobe, rnanar Asabar a majalisun tarayya da na jiha a Jihar Kaduna, jam’iyyar adawa ta African ADC ta zargi jam’iyyar mai mulki ta APC da daukar ’yan daba da kuma karɓar biliyoyin naira daga cikin jihar da wajen ta domin yin magudi.
Zaɓen cike gurbin zai gudana ne a mazaɓar tarayya ta Chikun/Kajuru da mazaɓar tarayya ta Zaria/Kewaye, da kuma mazaɓar majalisar jiha ta Basawa.
Waɗannan zarge-zargen na ADC sun haifar da musayar maganganu tsakaninta da gwamnatin jihar da kuma jam’iyyar APC.
Kwamishinan ƴaɗa Labarai na jihar, Ahmed Maiyaki da ya mayar da martani yana cewa zarge-zargen na ADC “ba su da tushe kuma abin dariya ne.”
Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta buƙaci a daina amfani da taswirar duniya ta Mercator saboda tana rage girman Afirka fiye da yadda take a zahiri.
A cikin wani sakon da ta wallafa, AU ta ce a koma amfani da Equal Earth — taswira da aka ƙirƙira a 2018 wadda ke nuna girman Afirka na gaskiya, wanda yake kilomita murabba’i miliyan 30.37.
Taswirar Mercator an kirkire ta tun 1569 domin taimaka wa jiragen ruwa yin tafiya, amma tana nuna Afirka a matsayin ƙarama, yayin da take nuna ƙarawa wasu nahiyoyi kamar Amurka ta Arewa girma.
Da goyon bayan AU, ana jiran a ga ko wannan yunkuri zai samu nasara wajen dawowa da Afirka matsayinta ba kamar yadda duniya ke kallonta ba.
Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta kuma kai tsaye ga gidajen mai a Najeriya daga yau, matakin da ake sa ran zai kawo sauyi a harkar man fetur ta ƙasar.
Kamfanin ya ce wannan shirin zai rage yawan masu shiga tsakani ya kuma ƙara inganci, tare da bai wa masu amfani da kuma gidajen mai damar samun zaɓuɓɓuka masu rahusa.
Matatar man Dangote dai mai ƙarfin tace ganga 650,000 na mai a rana ta fara aiki ne a shekarar 2023, inda ta taimaka wajen rage farashi bayan tashin gwauron zabin da ya biyo bayan cire tallafin mai da shugaba Tinubu yayi.
A jiya ne gwamnatin mulkin sojin Mali ta bayyana cewa ta kama wasu mutane da dama, ciki harda wani ɗan ƙasar Faransa da wasu manyan jami'ai biyu bisa zargin shirin juyin mulki a ƙasar.
Ministan Tsaro, Janar Daoud Aly Mohammedine, ya bayyana a gidan talabijin na ORTM cewa an kama mutanan ne a ranar 1 ga Agusta.
A cewarsa, lokacin da al’ummar Mali ke ƙoƙarin ƙarfafa ‘yancin ƙasa da kawar da ta'addanci daga yankin ƙasashen haɗin Sahel, waɗannan sojoji da fararen hula tare da haɗin gwiwar ƙasashen waje suna ƙoƙarin ruguje nasarorin da ake samu.
Ana zargin wani ɗan Faransa mai suna Yann Vezilier da yin aiki tare da leƙen asirin Faransa.
Hukumomin Faransa har yanzu ba su yi tsokaci kan wannan batu ba.
Mohammedine ya ce gwamnatin Mali ta la’anci wannan yunƙuri, tana kuma ci gaba da bincike don gano sauran masu hannu a shirin.
A yau ne wa’adin kwana biyar da hukumomin Sudan suka bai wa dubban ’yan gudun hijira da ke mafaka a makarantun gwamnati a El-Obeid, babban birnin jihar Kordofan ta Arewa, ya cika.
Rahoton gidan jaridar Darfur24 mai zaman kanta ya ce an bai wa ’yan gudun hijirar umarni duk da babu tsare-tsare na musu matsuguni na madadin makarantun da suke kwana.
Birnin da sojojin Sudan ke riƙe da shi na ɗauke da sama da ’yan gudun hijira 700,000 da aka raba da muhallansu sakamakon tashin hankali da dakarun RSF a yankin Kordofan.
Hukumar ilimi ta jihar ta ce makarantu za su buɗe a ranar 17 ga watan Agusta, lamarin da ake fargabar zai kara tsananta halin da ’yan gudun hijirar ke ciki.
Ƙungiyoyin ma'aikatan manyan makarantun Najeriya na ci gaba da yin watsi da sabon shirin da gwamnatin tarayyar kasar ta ɓullo da shi domin inganta jin dadin ma'aikata, da haɓaka ƙwarewar aiki, ga ma'aikatan manyan makarantun ƙasar.
Ita dai gwamnatin Najeriyan ta ƙaddamar da wani sabon shiri wanda aka tsara zai bayar da bashin kudi har naira miliyan 10 ga ma'aikatan manyan makarantun ƙasar da suka haɗa da na jami'a da kwalejin kimiyya da fasaha da kuma kwalejin ilimi.
To sai dai ƙungiyoyin ma'aikatan na ganin cewa ba hanyoyin samar da bashi gare su ya kamata gwamnatin ta ɓullo da su ba a wannan lokaci da ake ciki.